Showing posts with label Wasikon Soyayya. Show all posts
Showing posts with label Wasikon Soyayya. Show all posts

Saturday, 31 March 2018

DUNIYA!

World



DUNIYA!  
1.     Duniya kamar misalin wasar kwaikwayo ce da ake shiryawa a ga abu kamar gaskiya alhali shiri ne wanda ba gaskiya ba
2.     Duniya karewa take yi kamar yadda idan an kunna Kandil yana ci da wuta komai tsawon lokaci za a taradda wutar ta mutu
3.     Duniya misalinta kamar wasan kasa ce da yara ke yi bayan karewar ruwan sama idan sun gina Gida mai kyau sai kaji suna fadar wanda bai rusa ba dan gidan ladi mai tandayen kasuwa hmmm!
4.     Duniya kamar aji ne da ake daukar darasi acikin sa da duk wanda ya yi abin kwarai zai samu sakamako mai kyau idan kuma ya yi ganganci ya ki amfani da damar da ya samu lokacin daukar darasi to fa zai ga ba kyau a sakamakonsa.
5.     Duniya na kama da kasuwa lokacin da zaka shiga tabbas lokacin wani zai barta ba dawowa
6.     Duniya rayuwar gidan kaso
7.     Duniya rayuwace mai cike da ban alajabi da mamaki wata rana zaka tabbatar da hakan, bayan ka mutu zaka rayuwa kamar yadda ka rayu a cikin cikin mahaifiya
8.     Duniya gidan bakin ciki da damuwa da bacin rai, ko wacce ana jindadin duniya to, lallai ya duba imaninsa mai imani kullum a fargaba yake kuma cike da jarabobi
9.     Duniya misalin ta misalin dan aike ne da ubangidansa ya aikeshi kuma ya samu wuri ya fake yana jiran dawowarsa daga inda ya aike shi
10.   Duniya makaranta ce
11.   Duniya budurwar wawa
12.   Duniya ki dauka ki aje duk yanda mutum ya ke jiji da kai yake wani fadi wallahi wata rana sai anyi bashi kamar yadda akayi babushi kamin shi
13.   Duniya da rayuwa abokai ne idan ka biyewa rayuwa ita kuma duniya zata biye maka amma kuma ka sani cewa zasu kai ka su baro wata rana
14.   Duniya kamar misalin bako ne da zai sauka a gidanka komai dadewa wata rana zai bar gidan zuwa gidanshi na ainihi
15.   Duniya! Abin ayi hattara da ita ce domin idan kayi sakaci wata rana zata saka kuka
16.   Duniya gidan danjin dadi dan kadan kayi fankama ka bushi hanci wata rana a kasa za a saka
17.   Duniya gidan sabani, duk wani sabani anayinsa ne a duniya amma a lahira babu wani sabani kowa ya san gaskiya
18.   Duniya kamar gona ce duk abin da ka shuka babu makawa shi ne abin girbarka
19.   Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba tamkar jakine da kaya
20.   Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba kamar kasuwanci ne da ba riba a cikinsa
21.   Duniya gidan neman abincin lahira
22.   Duniya gidan neman aljanna
23.   Duniya da kunci ga wanda bai riki gaskiya ba
24.   Duniya ga wanda ya shigo ta abin jajantawa ne
25.   Duniya gidan hatsaniya da tashin-tashina
26.   Duniya gidan hakuri da jajircewa
27.   Duniya da rayuwa a cikinta ba tare da bin gaskiya ba misalin haduwa da makiyane ba tare da shiri ba
28.   Duniya! Mai sonki shi kika ci don shi zaki nunawa soyayya irin na karuwar da ke dauke da cutar kanjamau da manufar jikawa wani
29.   Duniya! Wasu na kuka a cikinta wasu ko dariya suke
30.   Duniya! Yanda aka zo cikinta babu komai tabbas haka ake barinta babu komai
31.   Duniya! Gidan bakunta
32.   Duniya kamar hadarin mushaki ne (hadarin da baya ruwa) ana ganin hadari ya hadu kamar da gaske ruwa za a yi sai kaga ya watse wayam!

OYOYO MASOYIYA TA


OYOYO MASOYIYA TA

Oyoyo masoyiya ta
Oyoyo zan baki gata
Oyoyo kaunar ki jata

Kaunar ki ta zama tsarin zuciya ta
Ke ce wacce na baiwa raggamata
Zo gani ki bani gata

Oyoyo sai na yaba ta
Kaunarki ce abin fadata
Sadiya kin basu rata

Yau gani ina ta fata
Na so ace kudduri da fata
Sun cika yau na bata gata

Me yasa so yake da sata
Nan take zuciya ya sata
Yabi jini da jijiya ta

Gaki fara kuma kina da tsafta
Doguwa ce ga ido an bata
Tafiyar ta tafi ta, ai ta tsere mata

Ina sonki ya masoyiya ta
Kaunarki tana a zuciya ta
Zo gani ki bani gata

Sadiya ce masoyiya ta
Kaunarki ina fadarta
A zuci kuma baki ya furta

Na aminta da son tauraruwa ta
Mai tsari irin na mata

Kizo gani ki bani gata

Wasikon Soyayya Series 6


Dare da rana kai ne abin tunani na
Aminci ya tabbata ga farin cikin zuciya

Bayan gaisuwa da fatan alkhairi ina gabatar maka da wannan sako ba don komai ba sai don tuna tarwa a gareka da irin soyayar mu.

Masoyi na, kada ka manta a dare da rana kai ne abin tunani na, a duk lokacin da nakwanta idan har ba muryar ka na jiba to faufau ni da bacci munyi ban kwana, yau kimanin shekara biyu da yan kwanaki kenan da na kamu da sonka amma na kasa na sanar da kai nayi kokarin nuna alamu amma sai nake ganin kamar baka ma san inda na dosa ba, Ibrahim ka sani cewa bazan iya rayuwa ba idan ba tare da kai ba, Ibrahim kai ne kadai zaka iya zamuwa gata a wuri na, shin me yasa zuciya bata jin rarrashi ne?, ni da kai na na sani Ibrahim ya san irin zafi da kuncin da mai so kan shiga idan har bai samu gata ba a inda yake nuna soyayyar sa ba. Ibrahim me yasa idan ina nuna maka kauna da tausayi da kuma kulawa lokacin kake kauracewa a gareni? Ka da ka manta shi so hallittace kuma jaraba ce kuma baka sanin lokacin da yake riskuwar ka kamar yanda baka sanin kiskuwar mutuwar ka.

Tunani na ya yanke basira ta ta dallashe, shawarwari na sun kare, boyon da nake ya kai karshe yau ne ranar da ta zamu ranar tarihi a wurina. Ina sonka, ina kaunar ka Ibrahim, bazan taba mantawa da kaiba, ka aminci da ni.
Kaunar ka nake dare da rana
Aisha Abubakar

1.   Oyoyo Masoyiya ta
2.   Na aminta da ke
3.   Kin kasance farin ciki
4.   Ina kike mai So na


Wasikon Soyayya Series 5


Garabasa
Farin cikin zuciya ta

Assalamu alaikum,

Ya ke farin cikin zuciya ta kuma sanyi idanuwa, hakika ke cewa face ta farko wacce na yi gamu da ita, bantaba zato ko tsammani ba za’ayi wata ‘ya mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi kankantar lokaci ba, amma sai gashi ba tsammani nayi kicibis da kyakkyawar muskar da na kasa dauke wa kallo.

Hakika tun lokacin da idaniya ta kalle ki zuciya ta kamu da ciwon sonki, na aiko miki wannan sako ne ba don komai ba sai don na rasa irin hanyar da ya dace na biyo kwana da kwanaki ina tunani da irin hanyar da zan biyo ta sanar da ke wannan cutar da Allah ya yi min jarabawa da ita, amma ina, na kasa na yi tunanin samun ki a makaranta domin na sanar da ke irin kaunar ki da ke kunshe a cikin zuciya, sai naga ba mafi sauki irin rubutu miki wannan wasikar.

Ka da na cikaki da surutu ya ke hasken zuciya ta kin riga kin zamu ginshikin rayuwata, ina sonki, ina kuma kaunarki, a kullun ke ce abin tunane na, zan rasa dukkanin farin ciki idan har ban samu amincewar ki ba, hakika zuciya zata dan dani wata irin azaba idan kika ce bakya tare da ni.

Daga karshe ina miki fatan alkhairi, ina kuma sauraru daga gareki, nagode.
Masoyin ki na har abada
Ahmad Muhammad Kabir

Wasikon Soyayya Series 4


Salam,
So taskar zuciya

Saurare ni masoyiya, so ya canja tunani na, Zainab ki kula dani, ki min hakuri amince dani, ke ce ki ka zamu muradi na, fili da waje. Soyayya ce ta zamu   

Zainab ina sanar da ke cewa na dauki alkawali ba wani abin da zai sa in daina sonki a zuciya ta. Kaunar ki ce ka dai a zuciya ta.

Kasance dani kuma kiyar da dani ya ke haske mai haskaka zuciya ta.

Masoyin ki har kullum

Wasikon Soyayya Series 3


Amince dani ya ke silar jin dadi na
Aminci a gareki,

Ya ke sanyin idaniya

Bayan gaisuwa irin ta masoya, tare da fatar rayuwa mai inganci ina miki fatan wuni lafiya.

Rasarin zuciya ta, abar kauna, hasken zuciya hakika kece zuciya take ta bege, zuciya take tsantsar kauna. Na rubuto miki wannan sako ne badon komai ba sai don na sanar da ke gaskiyar hakikanin abin da ke cikin zuciya ta. Na kamu da kaunar ki, hakika ya gama zagaye ko ina a sassan jikina, bani da wani abu da zan iya aiwatar wa. Amince da ni, ya  ke silar jin dadi na.

Ya ke mai haskaka zuciya ta, hakika a sonki na matukar dimauta ki aminci da ni masoyi ta.

Na amince da ke sanyin idaniya
Sadiq Musa


Wasikon Soyayya Series 2


Na shiga tsaka mai wuya
Salam, barka da wara haka ina fatan aminin zuciya a mafi ribatuwar rayuwa, bayan haka; ya kai sanyi idanu na sani kai na a mafi munin safiya yau ne ranar da bazan taba mantawa da ita ba, kuma yau na dauki biro na rubuta a kundin tarihin rayuwata.

Aminin zuciya ina baka hakuri dangade da abin da ya faro nasan nayi kuskure kuma abinda nayi ban kyautaba, hakika shedan ne sanadiyar afkuwar wannan al’amari.

Masoyina!, idan baka hakura ba shin wa zan nemi afuwa gunsa? Kada ka manta kai kadai ne farin cikin rayuwata kuma kai ne wanda nake fata ka zame man sanyi idanu na. ina sahibin zuciya? Ahmad ina sanar da kai cewa na dauki alkawari ba wani abin da zai sa in dai na kaunar ka, Kaunar ka ce kadai a zuciya ta, kuma kai ne Insha Allahu wand azan zamo mata a gareshi.
Ina sonka Ahmad
Daga Sahibar ka
Zainab Isma’ila


Wasikon Soyayya Series 1


Wasikon Soyayya
Masu cike da tabbacin cin nasara


Ina tunanin baki fahimci inda na dosa ba
Aminci a gareki,

Sarat! Kamar yanda na sanar da ke Ina tunanin baki fahimci inda na dosa ba, don haka sai na sake shawara da cewa abu mafi sauki shine in rubuta miki wannan takardar kamar yanda zai biyo baya.

Hakikanin gaskiya yaune ranar da zan bayyanar mikin da abin da yake zuciya ta, banyi zato ko tsammani ba zaki iya gujewa gareni, ko ki kyamace ni, sanin kowane Sarat yarinya ce kyakkyawa, wacce Allah ya baiwa farin jini, gakuma kyan fuska, gashi har gadun baya, a duk lokacin da Sarat take tafiya, nakan kure mata kallu, Sarat kin zance dukkanin yan mata, dayawa matan suke fata a ce sun taka sawun ki amma ina ba dama.
Kyan ki waye ba’indiya jiki mai kyau kuma inaga balaraba, tsayinki kuma dai dai kin tsayo matukar tsayowa Allah ya miki kyaun da bazan iya misaltawa ba.

Sarat idaniya sun hango farin cikinsu, sun hangu sanyi su, ranar da na aiko miki sako na na farko tunani na yayi rauni saboda tsoro da fargaba sai naga ba mafita idan har bana fito fili na sanar da ke sirrin zuciya ba.

Tsananin son ki ya tsanan ta a cikin zuciya ta har ma ya keta kirjina ya fito fili, duk wanda ya ganni na san ina cikin wani hali na daban, halayena, tunani na duk sun canja saboda ke.

Sarat ki amince da ni domin inyi alfahari da ke a wata rana da zamu tare a matsayin ma’aurata.

Ina sonki Sarat
Daga Muhammad Ishaq