MAGANGANUN HIKIMA KAN SO
100+
1.
A lokacin da na karanta, na kamu da so kamar yanda nake
kamuwa da bacci: sannu sannu, sannan gaba daya a lokaci guda.
2.
A soyayyarki ba wai ta tsaya a kunnuwa na bane, soyayyar ki
ba ta tsaya a zuciya ka dai ba, ba kuma a labba na ba amma ta tsaya a cikin
raina.
3.
Abokai sukan taimaki junan su. abota ta gaskiya itace wadda
zaka samu sukuni ka kasance a kashin kanka.
4.
Abota tana karewa a cikin soyayya, amma abota bayan soyayya
bazai taba yuwa ba har abada.
5.
Abu daya ne wanda bazai taba karshe ba kuma shine so
6.
Abuki shine wanda yasan komai daga gareka duk da haka ya so
ka
7.
Ace ana sona, yafi ince ina so a guna
8.
Ba dabi’ar so bane, sai dai dabi’ar abota ne yin auren da ba
farin ciki a cikisa.
9.
Ba ka zama na farkon ta ba, ba ka zama na karshen ta ba, ko
nata kai kadai. Tayi soyayya kamin ta sake soyayya. Amma idan tana sonka yanzu,
to menene damuwa? Ita ba cikakka bace kaima haka, sannan dukan ku ku biyu
bazaku taba zama cikakku ba, amma idan tana faranta maka, tana sanya ka tunanin
biyu, don haka yi kokarin zama mutum wanda ya san yakan iya yin kuskure, ka
rika ta, sannan ka bata abin da kake iya bata. Zata iya kasancewa tana tunanin
ka a kowane dakika ta kowace rana, zata baka wani bangare wanda tasan bazaka
karya ba a zuciyar ta. Don haka kada ka tsane ta, kuma kada ka canja mata, kada
ka yi tunani ko tsammanin zata iya baka abin yafi karfin ta/bata iyawa. Kayi
murmushi idan ta faranta maka, ka bari ta sani idan ta bata maka, idan bata nan
kayi kewarta.
10.
Ba wanda ya san gaskiya a so
11.
Babu wani lokaci ko wani mazauni na soyayyar gaskiya. Tana
faruwa ne batare da sani ba, a cikin bugawar zuciya, cikin faskawa guda, zai
samu bagire na din din din”.
12.
Bari mu zamu daya, tunani ya zamu daya
13.
Ciwon so na da azaba ya bogeni ni naji a zabar shi
14.
Da mai arziki
da sarki da talaka duk wawaye ne a duk lokacin da suka fada tarkon so
15.
Daga karshe, duk soyayyar da ka karba tana dai dai da
soyayyar da ka bayar
16.
Duhu baya gusar da Duhu: haske kawai ke yin wannan. Tsana
bata gusar da tsana (ciyayya): So kawai ke yin wannan.
17.
Duk kan so yakan iya kafuwa ko ya canja. Ban sani ba ko
zuciyar ka na cikin so a koda yaushe
18.
Duk kanin mai
rai yana son mai son shi
19.
Duk kanin
rayuwa ta, da zuciya ta sun tabbata ga abu daya da ni ban san shi ba
20.
Duk kanin soyayyar da ta roshe tana da bukatar dama ta biyu.
Amma ga wani na daban
21.
Duk wanda kake kauna kayi gaugawar sanar dashi
22.
Duk wanda ya raina mace to bai san asalinsa ba, wanda ya
wutakanta mace, bai godewa Allah ba, don mace ni’imace da Allah ya yi zuwa ga
namiji
23.
Ga dukkan kyau
akwai idon da zai ganta. Ga dukkan gaskiya akwai kunnen da ke saurararta. Ga
dukkan so akwai zuciyar da ke karbar ta.
24.
Ga dukkan wani
abu mai rai akwai so a tare da ita
25.
Gaskiyar
soyayya babu ta marmari
26.
Hakika mu bama so don muzama masoya sai dai muna so don so
27.
Har yaushe zaka kasance a cikin so? Kana nufin har abada?
28.
Hawaye kawace ga masoya
29.
Idan akace sai ka tabi so, to, kowa ma zai zama kuturu.
30.
Idan har zaka iya son kan ka to zaka iya son wasu mutanen da
ba kai ba fiye da kanka. Idan kayi haka zaka samu jin dadin rayuwa.
31.
Idan kayar so ta soke ka a zuciya babu mai cire maka dafi
32.
Idan zaka iya sanya mace tayi dariya, to zaka iya jefa
soyayyarka a zuciyarta
33.
In da ke zuciya bata yin kunya
34.
Ina so a so ni amma kuma ina so ince ina so.
35.
Ina son ki shine mafarin komai
36.
Ina sonka ai ko
da munafurci ne an gama maka komai.
37.
Bani da cikkakken tsaro kuma na tafka kura kurai masu yawa,
na kuma fiya hayyaci na a wannan lukacin kuma na kasa kula da kaina. Amma idan
zaka iya kula dani komai tsanani, to ka da ka yanke mini hukunci da rauni na.
38.
Itacen fure suna tabbatuwa daga hasken rana da suke samu.
Haka ma so yake tabbatuwa da kulawar da zuciya take zuwa gare shi
39.
Jahiltar so shine tilasta wanda bai son ka ya so ka
40.
Ka So a So ka to ai shi ne So!
41.
Ka so mutum ya guje maka ya zama cin zarafi
42.
Ka tsofa dani shine abin da yafi har kullum
43.
Kabar wanda kake so kabi wanda ke son ka
44.
Kasan cewa cikin zurfin so yakan sanya maka karfafa, amma
tsanani a son wani ya kan baka dama
45.
Kasancewa cikin farin ciki baya nuni da cewa komai na tafiya
dai dai
46.
Kaso mai sonka
ai yafi
47.
Kauna da dadi
amma kima ta na idon mai kunya
48.
Kaunar ki yau na adana ban barinta a hanya gudun taki
49.
Kayi komai cikin so, shi ne matakin cin nasara
50.
Kayi Soyayya kamar baza’a taba shiga damuwa ba, haka Rayuwa
take da nauyi fiye da duniya.
51.
Komai akayi ai
dai dai ne a cikin so
52.
Komai dai dai yake in kana cikin soyayya
53.
Kowa da daidan
sa a soyayya
54.
Kowa makahone idan aka ce dashi sai ya nuna so
55.
Labarin zuciya fuska ake tambaya
56.
Lokacin da ka ke zuba kalanzir a wuta take ruruwa, amma ita
wutar so tana ruruwa ne a dalilin lafazi
57.
Mace ta san fuskar wanda take so
58.
Mafi dadin sauti shine muryar macen da kake so"
59.
Mafi karamci a matakin cin nasara shine haifar da soyayya a
cikin zuciya
60.
Masoya kan rabu amma shi so baya rabuwa
61.
Me yasa nake sonki alhali baki san inayi ba? So da kunya ko
So cikin So?
62.
Mu kasance kullum muna haduwa da junan mu da murmushi, domin
shi murmushi shine mafarin So.
63.
Mun karbi So muna tunanin mun tsira
64.
Mutane da dama kan iya yin komai kan so
65.
Mutane na tunanin so shirme ne. So shine cikar hankali
66.
Na baki sirri na, ki ban naki. Guri na na zama naki, Kaunar
ki ta zama shuka cikin taki.
67.
Na baki so zo ki bani kauna
68.
Na koyi hakuri a cikin so amma ba kowa zai mallaki zuciya ta
ba
69.
Namiji kan samu saukin samun soyayya ga dakkan macen da ke
iya sauraren shi
70.
Ni ba wani abu
mai muhimmanci bane, ga wannan ni mai tabbaci ne. Ni mutum ne da ba kowa ba
kuma ina yin rayuwa ta a matsayin haka. Ina sanar da ku wannan ku sani sunana
ba da dadewa ba za a manta da shi, amma ka rayu kana son wani da dukkanin
zuciyar ka da rayuwar ka, wannan shine wadataccen abu har kullum.
71.
Rashin kusanci shine abu mai sauki wajen kula da soyayya
72.
Rayuwa idan ba so to tamkar ice ne da ba shida ganyaye ko
yaya
73.
Sai da so ake samun ilimi
74.
Sau daya a rayuwa, Na yarda na amince, ka samu wanda ka ke
tsammanin zai taimaka maka a rayuwa. Ka sanar da shi wani abu wanda baka taba
sanar da wani shi ba a rayuwar ka amma sai ya tarwatsa ya fallasa dukkanin sirrin
ka. Sannan kuma ya nemi da ka kara sanar dani wani. Sai na sanar dashi manufar rayuwa,
manufar da ba zata taba zama gaskiya ba, manufar da ba zan taba cimma ba, da
kuma wadansu abubuwan da banshirya a cikin rayuwa ta ba. Lokacin da wasu abubuwa masu kyau suka faru,
zaka tsaya don sanar da su game da abubuwan, alhali ka sani zasu tarwatsa maka
al’amari. Basu damu da suyi kuka tare da
kai ba idan ka shiga tsananin damuwa ba, ko farin ciki lokacin da ka shiga
nishadi. Ba zasu taba aikata wannan ba, don sun tsani al’amur ranka, ko suna so
ka kasance a kullum a wulakance ba ka da amfani, sannan kuma suce sune zasu
doraka a bisa wata hanya mai kyau su nuna maka abubuwan da zasu gina maka
rayuwa, su tabbatar maka da kariyar mutuncinka. Ka sani wannan ba zai taba faruwa ba har abada, ko da a
cikin wasa. Abin da kawai za ka yi shine shuru da bakinka a duk lokacin da kuke
tare dasu. Sannan ka da ka damu da abin da za su ce ko za su yi tunani
game da kai, sabuda suna son ka ne don abin hannunka. Wannan tunanin
nawa, mutane su rike shi saboda gudun shiga yanayin rashin sanin makiyi, ku
adana a cikin zukatanku, ku dinga tuna wannan har abada. Ku tunatar da ‘ya‘yan
ku tun kuna tare, ku fahimtar da su za su girma wata rana. Rayuwarsu za ta yi haske sannan kuma za tayi
kyau. Mayanka/Mahauta tana ganin rayuka a kowace rana, wata rayuwar sai
an zu ta ke tafiya, wata kuma za ta zo bata gaba daya. A tsawon lokacin aikin
ka, ka kasance mai fara’a a fuskarka. Idan suka zo ba dole ba ne gareka da ka cigaba
da tattaunawar da ka ke ba, amma ka nemo yanda za kayi shuru, don ka kawar da
tunaninsu. Ka yi tunani fa ba sa ra’ayinka kamin wannan lokacin da ka samu cin
gashin kanka. Saboda kasan kana da amfani da wannan mutumin wanda ke da
kyakkyawar manufa a gareka. Ka yi tunani wannan mutum ba zai taba amfani ba a
duk kan sha’aninka da al’amurranka da ka ke gudanarwa, nemi aboki na gaskiya
wanda ka ke da tabbaci tsara ne a rayuwaka, wanda zai zauna har karshe ku na
tare. Rayuwa za ta samu cika da bambanci wajen tafiyar ta. Sirrin ka da tsaro
don kana da tabbacin suna daya daga cikin rayuwarka.
75.
So ba abu bane da kake iya nemowa ba. So abu ne da ke iya nemoka.
76.
So baya da iya ka kuma ba za’a taba lokacin da ba bu so ba
77.
So baya misaltuwa
78.
So baya tsofa
79.
So da mutuwa ce wacce take kasancewa batare da shawara ba,
sai dai ta na jan akalar ka ta yanda take so
80.
So gamun jini ne
81.
So hana ganin laifi
82.
So kamar iskokai ne, baka iya ganin shi amma kana jinshi.
83.
So kamar wani irin fure ne kyakkyawa wanda ni bana iya taba
shi, sai dai ina ta kukarin shayar da shi
84.
So kamar wuta ne, ya kan iya kona zuciya
85.
So kamar yaki ne ya na da sauki a wajen faruwa amma yana da
wuyar dainawa
86.
So na gaskiya baya yankewa
87.
So shine a kullum mafificiyar kyauta kuma ta kan samu kai
tsaye batare da zato ko tsammani ba.
88.
So sina dari
89.
So tubalin Aminci
90.
So wani yanayi ne wanda farin cikin wani mutum zai cudanya
da naka.
91.
Son masoyin wani ai ya zamu kirawa kai wahala
92.
Soyayyar gaskiya bata boyuwa
93.
Tsontsayema sunyi, kudajen zuma ma sunyi, don haka muma
muyi, mukasance cikin kauna a koda yaushe.
94.
Wanda duk yace baya sonka to ka kiyaye kanka da shi don kuwa
komai zai iya aikata wa kanka
95.
Yafi ka yi so ya bare, da ace baka ta ba so ba
96.
Yana daga kammaluwa ka so mutane fiye da yanda zaso soka
97.
Zaifi a tsaneka da yanda ka ke da a So ka da yanka baka kaiba
98.
Zaka iya sanin kana cikin So idan har ka kasa yin bacci
saboda a kullum abu a bayyane yafi yin mafarci.
99.
Zaka iya yiwa kowa murmushi amma su hawaye martabace ga
masoya
100.Zaman lafiya
kan maida komai mai yuwa. So kuma kan mai da komai mai sauki
101.
Zamu mai son
jama’a, jama’a zasu so ka
102. Zama da masoyi shine makurar ni’ima
103.
Zan iya rayuwa batare da kudi ba, amma bazan iya rayuwa babu
so ba
104.
Zancen ki kullum idan na saurara, shi ke sani in dauwama
cikin murna
105. Zo ka rayu a cikin zuciya ta, biya zaka yi ba aroba.
106.
Zuciyar da take dauke da kauna itace mafarin dukkan sani
107. Zuciyar da take dauke da soyayya itace mafi amintuwar zuciya
Allah ya biyaka
ReplyDeleteAllah biya
ReplyDelete