Thursday, 9 February 2017

…BURINA



…BURINA



Bani sake soyayya
Bani sakara lobayya
Yau na juya baya

Na rasa farin ciki na
Mai haskaka ruhina
Mai tausayi ga kalbi na

Na zasa mai so na
Mun dade da son juna
Gashi yau iyaye sun raba mu da juna

Ni fa kece burina
Ke naso ace zan nuna
Surruka ga ummana

Meyasa kuke jifa na
Kuka nake kan kauna
Na rasa zabin kalbina

Masoyiya kizo zo guna
Zo kice kina burina
Aure muyo shi da juna

Zan rike amanar kauna
Zan tsare hakken mai sona
Ke ce muradin raina

Kaunarki ce burina
Kaunarki ta ratsan raina
In babu ke an barna

Farin ciki babu araina
Ya ke abin alfahari na 
Zo nan kizo muyi kauna

No comments:

Post a Comment