Sanadin so da kauna
Na rasa zabi na kaina
Kaunarki ce yau a raina
Kece na ke so na nuna
Uwa ga yaya wurina
Kaunarki ta zamto a raina
Jinin jiki na yau ta zauna
Na rasa yanda zanyi da kaina
Yaki ki zo kada ki yi sauna
Ni fa a sonki zan fansa raina
Nayi kuka zuciya har da kuna
Kan sonki sahiba yar amana
Kaunarki ta sani tunani da kaina
Nasan bazan iya rayuwaba in babu sunan
Sadiya a kaunarki zuci tayi kuna
Na rasa gane kanta bale na nuna
Wata rana kuka nake na zuci har da raina
Hawaye ke kwarara kanki yar
amana
Ki amince dani Sadiya mai tagwaye na suna
Kada kice baki sona
Kullun sunanta ne a raina
Idan nayi tunanin ko ba ki sona
Sai naji tamkar zan mutune ba lokaci na
Asibiti naje gun likkitana
Yace tunani ya yi jimar dan uwana
Aiki bana iyawa sai na kalli suna
Sahiba ta abin alfaharina
Mai kyan siffa tafiyar ta sai an nuna
Magana idan tayo maka sai ta auna
Hankali da tunanin ta waye batuna
Yar fara da farin hali ga amana
Yar mutan kwarai ce bani sauna
Ga tarbiyya da ilimi abin a nuna
Malama ce mai suna na yar amana
Kin ciri tuta mata sun biki sun tsugunna
Sawunki basu takawa don kin ci suna
Na kiraki da sarauniyar mata don na auna
Ki yarda na mallaki zuciyarki ko zan samu sauki a raina
In kika yimin haka ai sai dai a nuna
Ni wanda yafi kowa sa’ar mata yar amana
No comments:
Post a Comment