Book 1 of Hubbil Yaqeeen Series |
HUBBUL YAKIN
ASIYA SADIQ
MACCIDO
(ASIKHAN)
Copyright
© Asiya Sadiq September, 2017
Hakkin
Mallaka (M) Asiya Sadiq September, 2017
Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin
Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State,
Nigeria
Tel: 08113777717
Godiya ta tabbata ga
Allah kuma aminci ya tabbata a bisa za babben jakada shugaban Annabawa Muhammad
dan Abdullahi wanda aka saukarwa fiyayyen littafi ma’ana al-kur’ani domin ya
zama shiriya da kuma waraka ga muminai, Yar da da aminci su kara tabbata abisa
iyalan gidansa da sahabbansa da kuma mabiya tafarkinsa har ya zuwa ranar
sakamako.
Ina kara mika godiyata
ga Allahu subhanahu wata’ala, wanda shine Ya bani ikon rubuta wannan littafi.
Ina mika godiya ta
musamman ga Maihaifana Abubakar Sadiq Maccido da Zainab Sadiq Maccido da Aisha
Sadiq Maccido da kuma Rukayya Sadiq Maccido ga irin dawainiyarsu da kuma nuna
kulawarsu akaina, fatana Allah Ya biyasu, Ya kuma sanya alhairi a cikin
rayuwarsu baki daya amin.
Godiya ta ba zata kare
ba har sai na mikata ga yan uwa da aminai na kamarsu: Farida M. Bello,
Shamsudeen Sadiq Maccido, Sharahbil Muhammad Sani, Yakub Al’amin Yakub, Walid
Kabir Gada, Malam Usman Umar Aliyu, Badadiya, Habiba, Balki, Maryam Mufida,
Ummu, Baby, Billy, Sumayya, Fatima, Jamila da kuma Lubabatu da fatar Allah Ya
sanya alhairi a cikin rayuwarmu baki daya amin.
HUBBUL YAKIN
Misalin
karfe biyar da rabi ne na yamma, a daidai lokacin da ake tashi daga islamiya,
dalibbai daga ko ina sa bullowa sukeyi kowa yana kokarin ya koma a gida .Wata
natsatstsuwar yarinya mai hankali da kamala ce sanye da uniform dinta na
islamiya hijab dogo har kasa tafe take tana tako a hankali kamar wadda kwai ya
fashewa a cikin uniform din sky blue ne sunyi matukar yi mata kyau duk da ba
wani kwalliya tayi ba, domin ga dukkan alamu ita irin wayannan ne da ake kira
da “Natural beuties” Ma’ana (wayanda
basa bukatar kwalliya) domin wai ta kara musu kyau. Bakowa bace wanna
face Bilkisu mai gadon zinari ‘ya daya tilo a wurin Malam Iro. Yau gabaki daya
a cikin wani yanayi take jin kanta kuma itama kanta ta kasa gano meke damunta, kawarta
Asiya ba karamar gwagwarmaya ta sha akan dai ta ga ta sake ta dawo dai- dai kamar
yadda aka saba amma abin yaci tura, ga baki daya komai ba yayi mata dadi a
duniya, kuma ta rasa gano dalilin faruwar hakan, bata tsaya fira da Asiya ba da
aka tashi sakamakon tsayar da ita da Malam Babba ya yi, kawai sa kai tayi gaba
abinta. A daidai wurin wani mazauni ta tsaya ta gaida dattawan da ke wurin
cikin girmamawa, ansawa sukayi ga baki dayansu, yauwa Balkisu dama ke nake jira
ungo wannan ledar kaiwa Umman ki, wani dattijo wanda ko ba’a gaya maka ba kasan mahaifintane akan tsananin kamar da suka yi, ya
fada tare da mika mata ladar, hannu biyu tasa ta karba batare da tace komai ba,
tasa kai tayi gaba.Wani daga cikin dattijawan wanda tun sa’adda Balkisu take
wurin yake kallonta yana murmushi, shine ya bita da kallo har sai da ta kure
masa.Ajiyar zuciya yayi sannan ya fara Magana gaskiya Mallam Iro kayi dacen
diya maihankali da natsuwa ga ganin girman manya, murmushi mahaifin nata yayi
mai nuna alamar har a cikin ranshi yaji dadin abinda ya fada ba tareda ya fadi
komai ba. Gabaki dayan dattawan wurin kowa ya amsa da cewa ai kuwa gaskiyar ka
Bilkisu yarinya ce mai hankali, Malam iro ya katse zancen tare da fadin ai
kaima Alhaji Haliru ba karamin dace kayi ba da samun yaro mai natsuwa ga
hankali da kokari, a gaskiya duk afadin anguwarnan ba sa’an Sulaima dana sani
da yayi hankalin shi da sanin ya kamata.Ai kuwa ka tunamin ina zuci-zucin na
gaya maku amma sai na manta, inji Alhaji Haliru ga baki daya hankali ya koma
kanshi, me ya faru? Wasu mutum biyu suka hada baki.Sulaiman ya samu aiki Kaduna,
kunsan ya tura takardar neman aiki, jiya sunanshi ya fito ya samu aiki a
Kaduna, an bashi nan da wata hudu masu zuwa da yakoma ba kin aiki Insha
Allah.Masha Allah! ai kuwa wallahi munyi murna Allah ya sanya Alkhairi ga baki
dayan mutane suka ce Ameen, Alhaji
Haliru ya fada tare da dan ya mutsa fuska kamar wanda ya tuna da wani abin
haushi.Kunsan meye damuwata? A hakikanin gaskiya bana so Sulaiman yayi wannan
tafiya shi kadai, har Kaduna garin da bayada kowa sai Allah ni na ma rasa me
yasa aka kaishi aiki can, hakane to amma kuma ai namiji ne wanna ai ba abin
damuwa bane ni a gurina. Wani daga cikin
mutanen ya fada. Ba wannan nake nufi ba, ina nufin zaifi dacewa da ace yanada
mata kaga sai kawai su tafi tare abinsu ai kaga zata ringa dabe masa kewa ko? A
gaskiya kayi tunani Alhaji, ta mai zai hana
ayi masa aure ne yanzu sai kawai ya
wuce da Amaryar tasa? Aikai Malam Sani ba auren bane bana so nayi masa
a’a Inaso ne na samar masa mace mai hankali da natsuwa. Abu mai sauki ai ina ga
ga Bilkisu nan kamar halayansu yazo daya, me zai hana sai a hada su ko kuwa?
Malam iro ne ya fadi haka kai tsaye tare da jefawa Alhaji Haliru wani kallo mai
nuna alamar ko kuwa ya ka gani? Kamar ya san abinda yake zuciyar Alhaji Haliru
kenan, shi tun da can yana son ace Bilkisu ta kasance suruka a gareshi, a ganin
shi ba wanda ya dace ta aura face danshi Sulaiman. Da hanzari ya amsa da
wallahi kuwa da gaskiyarka malam Iro wannan abin da ka fada shine daidai,
Alhamdulillahi kai! da kuwa abu yayi daidai wallahi. Kai masha Allah a
hakikanin gaskiya kunyi tunani yanzu sai arufe zance guda, Malam Iro ne ya fara
da cewa ya mallakawa Sulaiman “da” a wurin Alhaji Haliru “yar” sa Bilkisu, shi
kuwa Alhaji ya karba hannu bibbiyu tare da bashi sulaiman din damar yazo a
gidansa domin su dai-dai ta a tsakaninsu kafin ranar daurin auren ta zo.Murna a
wurin Ahaji Haliru ba’a cewa komai, kamar ma shine angon. Bai jira lokacin tashi
yayi ba ya hauri takalmansa ya nufi gida cikin farinciki kamar wani wanda aka
yiwa albishirin shiga aljanna. Shima Malam Iro da saurin sa ya nufi gidansa
bayan an tashi daga mazauna, Allah-Allah ya ke yi ya isa gida, ya gayawa matarshi
labari mai dadi har a ranshi yasan Sulaiman yaro ne mai hankaali da sanin ya
kamata yana kuma sane da cewa zaya rike masa diyarsa da amana. Tun a kofar gida
ya fara rangada sallama har ya isa a cikin gidan, da hanzari uwargidan shi ta fito,
sannu da zuwa maigida an dawo lafiya, lafiya kalau ina Bilkisu? Yanzunnan taje raka kaawarta
Asiya, lafiya dai Baban balarabe naga sai wani faman far’a kakeyi ko tsintuwa
jakar kudi kayine ta fada cikin zolaya, murmushi yayi hade da yin gajeren
tsaki,wannan abin yafi tsintuwar jakar
kudi, to madallah bari na dauko tabarma naji wannan abin wani irin abin alkhairi ne haka,har ta dan
yunkura ya dakatar da ita, ki bar tabarma kawai lokacin sallah ya gaba to yanzu
masallaci zan wuce, gyara tsayuwarta taayi
ta fuskance shi da kyau ina jinka
baban Balarabe. Wato wani abin alkhairi ya same mu, kinsan Sulaiman dan gidan
Alhaji Haliru na can hayin kusa da masallacin jumua’a? eh! Da hanzari ta fada
tana kallon shi, mahaifinshi ya nemar masa auren Bilkisu kafin zuwa nan da wata
hudu za’ayi biki a kai amarya dakinta. Daga nan ya kwance mata biri har wutsiya
yanda sukayi a mazauna. Itama fara’ar takeyi ta kuma yi na’am da maraba da zancen,
sai dai a wata zuciyar tana jin tausayin Bilkisu ne, ta yaya za’ayi mata haka
kuma wai duka abin cikin wata hudu, bama wannan yafi damunta ba wai ba anan cikin
garin zasu zauna ba a’a har Kaduna, inda su dukan su ba mai dangin iya balle na
baba. Arwala yayi ya wuce masallaci tareda gaya mata bazai samu dawowa da wuri
ba zasuje wani wuri kuma zasu dan dade yasa kai ya fita, da hanzari ya dawo da
baya yauwa Hauwa’u ki fa gayawa Bilkisu komai idan ta dawo kinji! Tau ta fada
tare da daga kai alamar naji. Yasa kai ya fita, daukar butar daya gama alwala
tayi ta fara yin alwalar itama, har a cikin ranta tana farin cikin da abinda
maigidanta ya gayamata kuma tasan bazai cutar da diyar shi ba. Sai dai kawai
bata san ya Bilkisu zata dauki al’amarinba duk da tasan baza taki yin abin da
mahaifinta yace tayi ba. Kamar ta tuna da wani abu kuma sai kawai ta shararda
wannan zancen ta fara murna a ranta tana hango yar tata a matsayin amarya.
Kabbarta sallar ta keda wuya sai ga Bilkisun ta shigo, ta nemi guri ta zauna a
falo, remot ta dauka ta fara canja tasha daga NTA Hausa zuwa zee
cinema, wani film akeyi duka hankalinta yana a wurin. Bayan mahaifiyar tata, ta
idar da salla ta juya ta fuskance ta, tadan jima tana kallon nata batare da ita
Bilkisu ta gani ba, kasantuwar duka hankalinta yana kan abinda take kallo, sai
da ta kira sunan ta sannan ta waigo, Umma kin kare sallar ashe, ina wuni, lafiya
kalau mi ya tsai dake daga rakiya? Wallahi Umma Asiya ce ke bani labari bamu
san lokaci yana tafiya ba kuma sai akayi daidai da mu dukan din ba mai yi shi
yasa bamu damu ba mukaci gaba, daga kai kawai tayi sai da tayi dan shiru na
mintoci sannan ta fara da cewa: Maigado (sunan da take kiranta dashi kenan) duk
da yake ba it ace yar fariba kasantuwar duk yaranda ta Haifa rasuwa sukeyi
Bilkisu kadai Allah ya raya musu. Itama Bilkisu ta fuskanci mahaifiyar tata
tace na’am Umma, dazu mahaifinki yazo yayi min wani albishir wanda naji dadin
shi sosai. Ya kuma umurceni dana gaya miki wannan abin alkhairin. Gabanta taji
ya fadi batareda tasan dalilin ba murmushin yake tayi meye umma, wani abin
alkhairi ya same mu? Eh maigado babanki ne ya zabar miki da mijin aure, yaro
mai hankali da natsuwa kyakawa dashi, har ma angama Magana za’ayi bikin ku
cikin wata hudu masu zuwa. Kamar saukar aradu taji abin, shin wai ko mafarki ne
takejin wannan, ko kuwa zolayace Umma keyi mata? Kuma tasan Umma bata haka da
ita, hakikanin gaskiya dai take gaya mata,da kyar ta hadeye yawu, tace aure fa
kikace Umma, eeh aure mana maigado.ya naga kamar bakiji dadin abinda na
fada ba, maigado ki sani cewa mu
iyayenkine ba kuwa zamu zabar miki abin da zai cutar da ke ba,
anan ta dukufa tana maiyi mata nasiha
tareda lurarda ita, har aka kira sallar isha’I, ta miko da nufin kabbarta sallah
dan juyowa tayi a dai-dai lokacinda Bilkisun itama ta mike ta nufi dakin ta.Maigado
ta kirata tana murmushi, waigowa tayi na’am Umma,ba za ki tambayi ko waye
surukinnawa ba? Dukar da kanta kawai tayi, murmushi mahaifiyarta ta sakeyi, sulaiman
na can hayin gidan da yake kusa da masallacin Jumuah, dan maman sule ta idar da
maganarta da yar gajeruwar dariya, ita kuwa Bilkisu da hanzari ta fice daga falon
ta fada dakin ta, a hankali ta zauna kan gadonta a dai-dai lokacin da ta kwanta
tabi gadon, fankar take kallo amma ga baki daya halinta baya wurin, ji take
kamar wata almara, wai ita za’ayiwa aure cikin wata hudu. hoton sulaiman h ta
gani a’a idunuwanta a gaskiya tasan Sulaiman baya da matsala kuma yana da
halaye masu kyau amma kuma batajin son shi kona kwayar zarra a ranta, dolene
tayi biyayya ga mahaifanta domin ita kanta tasan samun miji irin Suleiman ba
karamar sa’a bace amma ya zatayi ita dai ba sonshi bane batayi kawai dai tayi
alkawalin ba zata sake son wani da namiji ba har karshen rayuwarta. Rufe
idanunta tayi to idan ma bata amince da Sulaiman dinba wa take dashi da take
so.kwatsam masoyinta rabin jikinta ya
fado mata a rai wato Usman wanda take kira da (MAN) wani hadadden saurayi ne
wankan tarwatsa sosai yana da jiki amma daidai dashi, yana da manyan idanu farare tas kamar madara, hancin sa irin wannan ne da
yake faro tsawon shi tun a saman goshi wato dai irin na shuhrakan, yana dauke
da wushirya da take haskaka fararen hakuransa kyau idan yayi dariya, kai a hakikanin
gaskiya duk inda haduwata ta kai Usman ya wuce can domin idan ka ganshi ba tare
dayayi Magana ba zaka zaci irin yan indiyan nan
ne dake zuwa kasashe-kasashe yawon bude ido, sun hadu ne da Bilkisu
lokacin tana (Secondary School SS1), hakika Usman gwanine wurin iya soyayya,
sun kasance suna son junansa so na hakika Usman shine saurayin Bilkisu na farko
a duniya tun tana SS1,suke tare har
takai SS2, Suna matukar son junansu kamar su hadiye kansu amma ba wanda ya sani
a gidansu kai karewa ma ko Aminiyarta bata sani ba duk kuwa irin shakuwar da suka yi a duniya. Wata ranar
litinin bayan an tashi daga makaranta fitowarta bakin (Gate) din ta hangoshi
tsaye cikin wani mawuyacin hali da hanzarinshi yazo ya taryeta suka hadu, a inda
suka saba haduwa ya nufa.Lafiya (MAN) naga kamar kana cikin damuwa meke faruwa?
Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya fara BILLY (shine sunanta yake kiranta
dashi) nazone muyi------- kasa idarwa yayi idanuwansa suka cika da kwallah,
muyi me (MAN) don Allah ka gayamin hankalinta duk atashe. BILLY nazo ne muyi
bankwana zanyi tafiya kuma zan dan dade ban dawo ba, yanzu ma ni kadai ake jira
a wuce.Nan take idanuwanta suka cika da kwalla, idan ka tafi yaushe zaka dawo
ne? Ta fada dai-dai lokacin da hawayanda ke makale idanuwanta suka kwaranyo.
Wani dogon nunfashi yayi tare da kanne nashi hawye bazan dade ba BILLY zandawo
komai daren dadewa, zan dawo gareki domin ke kadai ce matata a duk fadin duniya
nan kamar yanda nine kadai mijinki, karar wayarshi yaji wadda ke cikin
aljihunshi, bai kula ba, ya cigaba da jawabinsa, “Nayi miki alkawarin duk
fadin duniyar nan ba wadda zanso idan bake ba, zan dawo muyi aure dake mu zauna
har karshen rayuwar mu”. Duk iya
daurewar da ya yi a wannan karon sai da hawaye suka zuba a idanuwansa. Ita kuwa
Bilkisu dama ta ke yi, juyawa ya yi da karfi “BILLY sai wata rana!” bai
sake waigo inda ta ke a tsaye ba. Tafiya kawai yake, hawaye na zubar masa kamar
wanda ya rasa iyayensa ko aka gayawa bazai sake ganin taba har abada. Bilkisu
durkushewa ta yi a kasa tana kuka tana kiran sunansa. Tun daga wannan rana bata
karajin ko labarinsa ba, abin da yafi ma ta zafi da radadi a zuciya shine bata
da hotonsa ko guda daya wanda zata rika dubawa tana tunawa dashi sabanin shi da
ya ke da hotunta bila adadin, domin kuwa ko haduwa suka yi suna hira zai rika
daukanta hotuna ba adadi, kuma duk lokancin da tayi hotuna sai ta bashi. Wani tsaki
ta saka mai dauke da takaici, “Mwts” a dai-dai lokacin da ta dawo daga
kogon tunanin da ta ke yi, duk fuskarta ta jike da hawaye. “A hakikanin
gaskiya Usman bai kyauta ba, haka ma zuciyata bata kasance mai adalci ba da ta
kasa mantawa da Usman". Balkisu ke fadar haka a cikin zuciyarta. Wannan
shine dalilin Bilkisu da yasa tun daga Usman bata sake gwada soyayya da kowa ba
duk da tururuwar masoyan da suka mata zarya, domin irin kyanta da kirarta ta
wuce gaban namiji ya kalleta sau daya ba tare da ya maimaita kallon nata ba. Bilkisu
farace amma ba tasba, ta na da manyan Idauwa masu (Shape) din nan da ko
ba’a sanya musu kwalli ba sai ka zata ai su na da. Ta na da Girar Ido irin
dara-daran nan masutsawo da basa bukatar (mascara) wurin bayyana tsabar kyansu,
girar idanuwawanta kuma irin bakar nan ce kirin mai matukar sha’awa, hancinta
kuwa dogo ne shigen irin na Rani Muhurji shi baiyi tsawo sosai ba amma kuma
dogo ne, gashin kanta kuwa dogo ne wanda ya zuba har a gadon bayanta baki wulik dashi kamar kullum tana
saka mishi man da zai kara mishi baki, tanada fararen hakora sai kace sai da aka
sanya ruler wajen daidaita su, shape dinta kuwa ko Nicki Minaj sai dai ta bawa kanta
lafiya domin kuwa koda ita Bilkisun aka bawa dammar ta kera kanta da kanta iya
shape dinda zata yiwa kanta kenan, kai! A gaskiya tsayawa bayanin halittar da
Allah yayiwa Bilkisu bannan lokaci ne domin kuwa sai mu cika rabin littafi muna
bayani ba tareda mun kammala ba.
Zamu cigaba Insha Allahu
No comments:
Post a Comment