Saturday, 4 February 2017

SANADIN SO



SANADIN SO




Ni na aminta so zai sakani in miki komai
Na zamo gwani na fada kan sonki an kirani jarmai

Soyayya silar rikirewata na rike makamai
Sunanki ya zamo lakabi agareni na zama na sadiya fadamai


Naga sauyin al’amarina
Sai tunani safe da rana

Duk wanda za ya so ki nashaida ba za ya kai ya ni ba
Sunanki ya fimin komai daraja ban gano ya shi ba

Wazai tabaki in har gani da rai bai ciyo wuyaba
Sam bani fargaba sanadin soyayya na daura danba

Ban bukatar amini gyara
A tabaki in saka sara

Shi so saboda bashi da tabbas ne aka kirashi tsuntsu
Hanta da zuci in sunka firgice so ne yake tsumasu

Zanso batun da nayyo miki masoyiyatawa ki gamsu
Kudade na adana dominki ne nayyi asusu

So yasa na zama gwarzo
Ki ci nama ni inci kanzo

Indai ban ganta ba kunci kan hanani bacci
Ko yannayi na sanyi sai na rika mafeci

Kanne gareta in har na gansu sai na basu tukuici
Ko don su bani labarin abin kauna na bar maraici

Sannan rai yay ta nishadi
Su fadamin don naji dadi

Dukkan abokanai na sukan fadamin inbi a sannu
Nan take ince musu munafukai sun sakan idanu

Bana tsoron nayiwa mutum rauni ko na balla hannu
Nazam abin ayo rarrashi sai dai abini sannu

Ba a son raina na zamo ba
So ne ya sakani ukuba

Karko guda nai adduar iyaye taimini rana
Badan haka ba da tuni naje kas ba a kara jina

Kango da na shige makami nake boyo kuji batuna
Ko da wani zai kawo latsi gun rabin jikina


Makami sai da na dakko
Ban tsoron ai mini tarko

Ko yan sanda na zam musu tsawon gari sun gaji da nema
Ba mugun furuci na iyaye kaina na ga alama

Burin mahaifiyata na shiryo zuciya tayi salama
Na sari saurayi ga budurwa ta sanarwa hukuma

A gida namu na bar kwana
Banso ku gano laifina

Duk wadda nai hakan domin ta ashe bata san dani ba
Nasa yayanta yayi fada mata wai duk bata zataba

Ko zata makaranta a baya zan bita bada wai ba
Na hankure da tawa school din sai dai ingararamba

Indai na rikice ita dauce ke saita lammarina
Indai tana fadamini zan bi ko babu ra’ayina

Yau gani da damuwa ni da ita zanso ace mu gana
Amma a yanzu na kasa in fada mata sirrin cikina

Wayyo ni Allah Kaina
So ya canjan kudurina

Daure ki soni zan canja rayuwata tayo nagarta
In baki soni ba daga kai naki ban kara kula mata

Inkin aminta zaniyo sujuda domin ko nayi rata
Fatan da nai abin so gareni kada kimin mugunta

In kikai haka kin mini gata
Addata zai ajiye ta

Zakuji a kashi nabiyu sahiba ta me ta fadamin
Nan gun ne ni zan barku
Sharha M.S Nuhu Naku

No comments:

Post a Comment