Showing posts with label Books. Show all posts
Showing posts with label Books. Show all posts

Saturday, 31 March 2018

SANA’A RAYUWAR MATASA


SANA’A RAYUWAR MATASA


YOUTH@KEBBI STATE
SAHIHIYA YOUTH ENTREPRENEURS PROJECT


SHIRIN KUNGIYAR
SAHIHIYAR RAYUWA YOUTH COMMUNITY DEVELOPMENT ASSOCIATION




NA
SARATU MUH’D SANI

Copyright © 2017 Sahihiyar Rayuwa
Hakkim Mallaka (m) 2017 Sahihiyar Rayuwa

Published by
SAHIHIYAR RAYUWA YOUTH COMMUNITY DEVELOPMENT ASSOCIATION BIRNIN KEBBI, KEBBI STATE  
E-mail:sahihiyarrayuwa@gmail.com
Tel: 08113777717, 08103139272




Cover Design/Book Setting/Layout By:

SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAKERA
Website: www.hausacc.cf
Tel: 08113777717
 










FADAKARWA
Ba a yarda wani ko wata suyi amfani da wannan littafi ba ko ta wace siga sai tare da izinin Kunigyar Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association


GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah, kuma aminci ya tabbata a bisa zababben Jakada Shugaban Annabawa Muhammad dan Abdullahi, wanda aka saukar da Alkur’ani domin ya zama shiriya da kuma waraka ga Muminai. Yarda da aminci su kara tabbata a bisa iyalan gidansa da sahabbansa da kuma muminai har ya zuwa ranar karshe.
Ina kara godiya ga Allah da Ya bani damar rubuta wannan littafi a bisa dalilin Shirin da kungiyar Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association ta shirya ga matasan Jihar Kebbi, hakan ya sa aka nemi da in rubuta wannan littafi domin amfanin matasan da ake koyarwa a karkashin shirin domin koda sun koma gidajensu wannan littafi zai zame musu jagora.
Bayan wannan takaitaccen bayani ina so inyi godiya ga Sharahbil Muhammad Sani Makera Shugaban Kamfanin Sharhamak Computer Ventures kuma Shugaban Kungiyar Sahihiyar Rayuwa bisa ga kokarin da suke yi don ganin matasa hasalima mata sun samu kyakkyawar Rayuwa inda suke bin hanyoyi daban daban don ganin sun wayar da kan matasa game da muhimmancin ilmi, sana’a da kuma kokarin hanasu shaye-shaye. Ina kara godiya ga mataimakansa, musamman Abdulmalik Abubakar Ubandoma Secretary da Ahmad Rufa’i P.R.O da Aisha Abubakar Sayyadi, da Ridwan (Tope Boy) da Jamilu Yahaya Ambursa da kuma Abubakar Imamu suma ina godiya sosai ga irin kokarin da suke na ganin sun bada lokacinsu da karfinsu don ganin tafiyar nan ta alhairi ta cigaba.
Godiya ta ba zata kare ba har sai na mika godiya ta musamman ga Uban Kungiyar Sahihiyar Rayuwa Alhaji Babangida Mai Ahu bisa ga jajircewa da yake yi domin ganin wannan tafiya ta alhairi ta cigaba, ina rokon Allah Ya sanya musu alhairi, Ya kuma kyautata rayuwarsu damu baki daya.           



SADAUNARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga Kungiyar Sahihiyar Rayuwa tare da Jama’arta da Masoyanta da kuma Matasa Maza da Mata a duk inda suka, tare da fatar Allah Ya sanya ma wannan littafin albarka, ya zama mai amfani a doron kasa, Ya kuma sanya wannan kyakkyawan aiki a mizanin mu na lada, amin.

TA’ALIKI  
Bashakka ita sana’ar hannu ba karamar muhimmaniyar sana’a bace musamman ga al’umma, domin kuwa tana iya zamowa:
·       Sanadiyyar wadata
·       Samun yanci ga kai da kuma kasa baki daya
·       Walwala
·       Hana ta’addanci kamar irinsu sata da yaudara
·       Hana zaman banza
·       Tare da bunkasa tattalin arzikin kasa da sauransu.
Ganin irin wannan yasa kungiyar Sahihiyar Rayuwa ta zare damtse kuma ta dage wajen ganin ta bada nata gudummawa ga rayuwar matasa saboda irin muhimmanci da rawar da matasa ke takawa ga rayuwar al’umma. Hakika wannan taimako na wannan marubuciya ya yi dai dai da manufofin da kasar Nigeria ke bukata a yau, na a himmanci sana’o’in hannu musamman abin day a shafi fasaha irin wannan… Bashakka, wannan littafi zai taimaka kwarai irin ganin yadda Matasa ke neman hanyoyin Karin ilmi akan wadannan sana’o’i. don haka ya wajaba ga ko wace Cibiyar koyarwa da kuma wadanda ke koyon sana’o’i a gida su mallaki wannan Littafi domin samun Karin haske akan sana’o’i iri daban daban.

SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
President/Founder
Sahihiyar Rayuwa
29th April, 2017


 COSMETICS
1.   ROOM FRESHENER
KAYAN HADI:
·       Ruwa
·       Menthol
·       Methanol
·       Thickner
·       Texaphor
·       Colour
·       Perfume
YADDA ZA’A HADA: 
A sami roba ko bokitin roba mai kyau, ya danganci yawan turaren da za’a yi, sai a zuba ruwa cikin bokitin sannan a kawo menthol a zuba cikin ruwan daga nan sai a ajiye ruwan cikin rana yadda menthol din zai narke. Idan an tabbatar ya narke sai a kawo methanol a zuba sannan a motsa sosai. Daga nan sai a zuba thickner a motsa sannan a zuba Texaphor sai a zuba kala da turare a motsa sosai. Shikenan turare ya hadu sai a samu mazubi a zube. 
2.   CAR WASH
ZA A NEMI: 
·       Ruwa
·       Anti-soap (natrol)
·       Sls
·       Sulphonic Acid
·       Soda ash
·       Kala
·       Madarar turare

YADDA AKE HADAWA:
Za a jika anti – soap ya kwana saboda ya narke da kyau gudun gudaji. Bayan ya kwana ya narke sai a motsa a zuba sls tare da sulphonic acid a motsa sosai har sai sun narke sai a jika soda ash da ruwa kadan, a zuba a motsa. Daga nan sai a zuba kalar da ake so da turare.
3.   VASELINE
KAYAN HADIN DA AKE BUKATA:
·       Candle wax
·       Petroleum Jelly
·       Paraffin oil
·       Perfume (madarar turare)
·       Mazubi
YADDA ZA A HADA:
Za a fara narka candle wax idan ya narke sai a zuba jelly, idan shima ya narke sai a zuba paraffin oil a motsa, sannan a zuba madarar turare a motsa. Shikenan sai a saukar da tukunya. Idan ya fara shan iska kadan ya rage zafi sai a zuba a mazubi.
4.   LIQUID SOAP
KAYAN HADIN DA AKE DA BUKATA:
·       Ruwa
·       Anti-soap
·       Sulphonic acid
·       Costic soda
·       Soda ash
·       Sls
·       Madarar turare da kala

YADDA ZA A HADA:
A jika anti soap da ruwa isasshe sannan a barshi ya kwana, sai a motsa shi sosai, sannan a kawo sls a zuba, sannan kuma a zuba sulphonic acid a motsa. Soda ash da costic soda daban-daban za a jika su, sannan a zuba soda ash da farko sai a sanya Costic soda a motsa hadin sosai daga karshe sai a zuba kala da turare a motsa, daga nan sai a zuba a mazubi.
5.   ROBB
ZA A SAMI WAYAN NAN KAYAN HADIN KAMAR HAKA:
·       Petroleum Jelly
·       Menthol
·       Camphor
·       Colour
A narka Jelly sai a zuba menthol, shima ya narke sai a motsa sosai sai a sauke kan wuta a barshi yadan sha iska kadan sai a zuba camphor tare kala a motsa sai a sami mazubi a zuba.
6.   SHAMPOO
KAYAN HADIN DA AKE BUKATA:
·        Anti soap
·       Coustic soda
·       Soda ash
·       Sulphonic acid
·       Sls
·       Kala da madarar turare
YADDA ZA A HADA:
A jika anti soap kamar dai yadda nayi bayani a baya, idan ya narke sai a kawo soda ash da costic soda da aka jika a zuba cikin ruwan anti soap a motsa sosai, sai a zuba sulphonic acid shima a motsa a zuba sls a motsa sannan a zuba kala da turare, a barshi kamar awa uku (3hrs) sannan a zuba a mazubi.
BODY CREAM
Kayan hadi da ake bukata:
Ø Stearic Acid
Ø Cytel alcohol
Ø Borass
Ø Koroda wax
Ø Parafine oil
Ø Colour and Perfume
Yadda za a hada:
A zuba stearic acid, cytel alcohol, koroda wax, cikin tukungya mai tsafta a dora a wuta har su narke, sai a zuba parafine oil a jika Borass da ruwan zafi idan ya jika sai a zuba ciki a motsa sosai, za a ga ya yi kauri kamar koko, sai a zuba kala da tura a motsa, a sami mazubi a zuba.
FARAR POWDER
Za a tanadi:
Ø Calcium carbonate   



DUNIYA!

World



DUNIYA!  
1.     Duniya kamar misalin wasar kwaikwayo ce da ake shiryawa a ga abu kamar gaskiya alhali shiri ne wanda ba gaskiya ba
2.     Duniya karewa take yi kamar yadda idan an kunna Kandil yana ci da wuta komai tsawon lokaci za a taradda wutar ta mutu
3.     Duniya misalinta kamar wasan kasa ce da yara ke yi bayan karewar ruwan sama idan sun gina Gida mai kyau sai kaji suna fadar wanda bai rusa ba dan gidan ladi mai tandayen kasuwa hmmm!
4.     Duniya kamar aji ne da ake daukar darasi acikin sa da duk wanda ya yi abin kwarai zai samu sakamako mai kyau idan kuma ya yi ganganci ya ki amfani da damar da ya samu lokacin daukar darasi to fa zai ga ba kyau a sakamakonsa.
5.     Duniya na kama da kasuwa lokacin da zaka shiga tabbas lokacin wani zai barta ba dawowa
6.     Duniya rayuwar gidan kaso
7.     Duniya rayuwace mai cike da ban alajabi da mamaki wata rana zaka tabbatar da hakan, bayan ka mutu zaka rayuwa kamar yadda ka rayu a cikin cikin mahaifiya
8.     Duniya gidan bakin ciki da damuwa da bacin rai, ko wacce ana jindadin duniya to, lallai ya duba imaninsa mai imani kullum a fargaba yake kuma cike da jarabobi
9.     Duniya misalin ta misalin dan aike ne da ubangidansa ya aikeshi kuma ya samu wuri ya fake yana jiran dawowarsa daga inda ya aike shi
10.   Duniya makaranta ce
11.   Duniya budurwar wawa
12.   Duniya ki dauka ki aje duk yanda mutum ya ke jiji da kai yake wani fadi wallahi wata rana sai anyi bashi kamar yadda akayi babushi kamin shi
13.   Duniya da rayuwa abokai ne idan ka biyewa rayuwa ita kuma duniya zata biye maka amma kuma ka sani cewa zasu kai ka su baro wata rana
14.   Duniya kamar misalin bako ne da zai sauka a gidanka komai dadewa wata rana zai bar gidan zuwa gidanshi na ainihi
15.   Duniya! Abin ayi hattara da ita ce domin idan kayi sakaci wata rana zata saka kuka
16.   Duniya gidan danjin dadi dan kadan kayi fankama ka bushi hanci wata rana a kasa za a saka
17.   Duniya gidan sabani, duk wani sabani anayinsa ne a duniya amma a lahira babu wani sabani kowa ya san gaskiya
18.   Duniya kamar gona ce duk abin da ka shuka babu makawa shi ne abin girbarka
19.   Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba tamkar jakine da kaya
20.   Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba kamar kasuwanci ne da ba riba a cikinsa
21.   Duniya gidan neman abincin lahira
22.   Duniya gidan neman aljanna
23.   Duniya da kunci ga wanda bai riki gaskiya ba
24.   Duniya ga wanda ya shigo ta abin jajantawa ne
25.   Duniya gidan hatsaniya da tashin-tashina
26.   Duniya gidan hakuri da jajircewa
27.   Duniya da rayuwa a cikinta ba tare da bin gaskiya ba misalin haduwa da makiyane ba tare da shiri ba
28.   Duniya! Mai sonki shi kika ci don shi zaki nunawa soyayya irin na karuwar da ke dauke da cutar kanjamau da manufar jikawa wani
29.   Duniya! Wasu na kuka a cikinta wasu ko dariya suke
30.   Duniya! Yanda aka zo cikinta babu komai tabbas haka ake barinta babu komai
31.   Duniya! Gidan bakunta
32.   Duniya kamar hadarin mushaki ne (hadarin da baya ruwa) ana ganin hadari ya hadu kamar da gaske ruwa za a yi sai kaga ya watse wayam!