Showing posts with label Heart. Show all posts
Showing posts with label Heart. Show all posts

Thursday, 5 April 2018

HUBBUL YAQEEN SERIES 5

HUBBUL YAKIN cigaba
  
ASIYA SADIQ MACCIDO
(ASIKHAN)

Copyright © Asiya Sadiq September, 2017
Hakkin Mallaka (M) Asiya Sadiq September, 2017

Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State, Nigeria
Website: www.hausacc.ml
Tel: 08113777717

Book 1 of Hubbul Yaqeeen Series 


Shi kuwa Sulaiman tunda ya wuce bai tsaya ko inaba sai a bakin gate din office dinsu, kaf ya tsaya tsam kamar wanda yaga wani dodo, sani ya manta oganshi yayi tafiya, ya tafi wajen wani comfrence da za’ayi a sokoto kuma zasuyi kamar kwana shida zuwa biyar basu dawo ba, to meyasa ma wai bai tuna ba sai a yanzu, wani tsaki yayi mai hade da takaici, said a yayi kamar minti biyar a bakin gate din office din nasu sanna ya tada mashin dinshi ya nufi gidan Alhaji day a basu haya domin ayita takare idan yanada wani gida ya canza musu ko kuwa asan yanda za’ayi kafin nan da zuwan kwanaki shida da oganshi zai dawo ya nemi transfer ya bar gari tun a kan layin gidan Alhajin ya fara ganin dandazon mutane ba adadi har ya iso kofar gidansa, me zai gani ga dukan alamu wani abu akayi ras! Gabansa ya fadi a wurinda shimfida take ya dire takalma yayi sallama ya mike hannu tabbas gaisuwar rasuwa ake yayi gaisawa aka ansa masa ya nemi ya gana da babban dansa, kasan cewar yasan sulaiman domin tare dashi akayi process din gidansu Sulaiman. Bayan da Sulaiman ya kara yi masa gaisuwa ya tambayeshi yanda haka ta faru, ya shaida mai matukar rudarwa, a jiya da dare ne yana bacci sai kawai akaga ya mike tsaye ya sauka daga kan gado, ya farayin da baya-dabaya yana ta ko’ina har ya fadi kasa, likitoci sun auna sun fada cewa sakamakon ganin wani mummunan tashin hankali da idon dan adam da kuma kwakwakwar sa basa iya dauka da yayi shiya hifar masa da wani matsanancin bugun zuciya da har yayi sanadiyar rasa rayuwarsa a nan take dirshan ya fadi a kasa hawaye suka riqa zuba a idanuwansa, al’amarinda yayi matukar bawa mutanenda ke wurin mamaki kenan hade da tausayin musamman babban dan Alhaji, lallashin shi aka dingayi har ya dawo cikin hankalishi ya daina kukan da yake. Shi kadai yasan abinda yakewa kuka tabbas shakkah babu akwai wani mummunan abu dake shirin faruwa dasu, gashi sub a yan gari ba yaya zai yi. Ya zabura ya mike ya sake gaisuwa yayi sallama ya wuce, dole subar garinan gobe-gobe ba domin sko yanzu lokaci ya kure musu bad a sun bar garin a yau, kara gudu yayi kamar wanda zai tashi sama domin kar dai wani abu yazo ya sameta domin kuwa Bilkisu shi c eta fado mishi a rai, kar dai wani abu yazo ya sameta. Krar shit ta dawo masa da hankalin shi daga tunaninda yakeyi bai yi ni yar ya dauka ba kuma dai yaji bari ya dauka aljihu ya zara wayar shi sanan abakinshi Nuhu ya gani da sauri ya dayka ya karakan kunnensa, slamu alaikum ya fadawa alaikussalam, Sulaiman don Allah kayi hakuri kaga ban samu dammar kawo su uUmmi ba Wallahi jiya da sakiyar dare mamansu ta kuma da matsanancin ciwon ciki amai da gudawa tun sa’annan muna asibiti sai yanzu muka dawo, yanzu dai Alhamdulillahi ta samu sauki sosai, kayi hakuri fatun sannan ban masan ida wayana yake ba sai yanzu da muka dawo bare na kiraka na gagayama bazan samu dammar kawo su ummi ba kasan ya yanda al’amuran suke wallahi tun sannan bansamu nutsuwa ba sai fa yanzu da kaga na kiraka. Rasa ta cewa yayi can ya lalibo kalamai yace ai badamuwa Nuhu Allah dai ya bata lafiya ya tashi kafadarta sai munzo dubata nida Uwargidata tau amen, amee, Sulaiman, When sai kunzo, sai an jima ya katse wayar. Wani matsanancin gudu yakeyi kamar ranshi zai fiita ya nufaci gidanshi haiqan dearest!dearest! dearest! Yake fadi kamar wani mahaukaci, da karfi yasha kwanar gidansi, kicibis! Yayi da wani abin ban mamaki, Bilkisu ya hango tana fama dariya tana bye-bye da hannunta, kyar ya iso a gabanta, murmushi tayi ta nufaci inda yake sannu da zuwa ga baki daya ta jagula masa lissafi zauwa ke dawa kike bye-bye haka? Malam mu shiga daga ciki ai ko, biye kawai yake da ita, suka shiga cikin gida su waye suka zo wurinki ne haka, ni fah da farko duk kin tsoratani n zata ko ke kadaice a gidan duk hankalina ya tashi, wani kallo tayi mai alamar ina ma fushi da kai, eh ai dole kace haka ai, ta wani shagwabe murya sanna tace stunda kasan Nuhu ya kawo su Ummi! Shine ka tafi abinka ka shallake, to sune nakewa bye-bye da yazo daukan su, nayi-nayi ya jiraka amma yaki ta, su ummi!! Kuma Nuhun ne yazo daukan su!! Mikewa yayi inna lillahi wa inna  illaihi raji’un, a firgice itama ta mike hakika sulaiman dinta ba karamar razana yayi ba to muje na razana a cikin abinda ta fada. Lafiya dearest meya faru meye don Allah gayamin, Bilkisu tashi ki had kayanki gobe-gobe zamubar garinnan, me ya faru ka gayamin! Ta daka masa tsawa tana mai zubarda kwallah batareda tasan ma tayi ba, da kyar ya kwantarda hankalinshi ya zaunarda ita kana ya bayyana mata duk abinda ya faru tun daga farko har rasuwar Alhaji da rashi lafiyar mata Nuhu duka ya bayyana mata shiru tayi ta kasa koda motsa dan yatsan ta akan tsananin firgitarda tayi Bilkisu! Bilkisu! Ga baki daya batajin abinda yake fada, said a ya wujijigata da karfi sanna ta dawo ayyacinta, Bilkisu karki damu gobe-gobe zamu bar garinan a’a ba sai na ta fada tana mai fashewa da matsanancin kuka, a’a Bilkisu ki bari gobe tunda sassafe, a’a ta durkusa kasa ta rike masa guwayyunsa na rokka don Allah Mubargarin nan a yau din nan, nunfashi ya aje, to shikenan jeki hado kayanki mu wuce, karki damu sa sauran kayan, idan nazo karbar transfer letter din azan wuce dasaura, shiga tayi ta tattara kayanta shima tattara nashi kayan yakeyi, sai a yanzu ta gane lallai wayannan basu Ummmi bane, bayan da ta zuba maganin sai taga duk sun wani kamar rikice, ta tuna sanda ta aika amina kitechen ta dauko mata plate sam takasa shiga a kitchen din, sa yanzu ta fahimci tun lokacinda ta zuba maganin basu sake takawa daga cikin falon ba. Tsam ta mike tunawa tayi da yanda Ummi ta dauko jug a cikin feeg wanda ta cika da drinks din kwakwa ta wankada akan kofar fita falon wanda zata fitar da mutum zuwa ta gane da gangan ta fadi ta zubar da drinks din don dai kawai su samu su fita. Kamala hada kayan tayi a dai-dai lokacinda shima y agama kamala nashi muje ko yace ta janyo hijabinta data ajiye kalar kayanda ta saka tace eh, muje tare suka nufi hanyar fita, tsayawa sulaiman yayi ya kalli gidan da kyau ya gayda kai ya wuce suka kulle gida sun juya zasu wuce sukaji an kyalkayale da wata mahaukaciyar dariya, duban juna kawai sukayi ba tareda sun ce ko kalaba sukaja akwatunansu sai a kan titi suka tsaya, wani mai a daidaita suka tsayar, garge zaka kaimu, yasa kayansu ya nufaci garge din, misalign karfe uku da rabi ne narana garin ana tsananin zafi, wurin fifa ya tsayar day an layin su, jira suke ya dauko musu hannu su wuce, ji tayi kamar ana girgiza kasa, ruguzum komi na wurin ya fara rusgawa cikin kasa, kuwwa da hrgowar jama’a kawai kakeji, motuna da baburra sairuguzawa sukeyi kamar an cilla a dai daita sahu su, sulaiman ya runtuma cikin, caf tasa hannuwanta ta cafkoshi, wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta shiga kuka take tana hargowa karka tafi ka barni tana rike da hannunshi sauran jikinshi kuwa yana lib, hannunshi ya fara subuce mata tana mai tsala uwar kuwa tsundum ya fada yana kiiran sunanta Bilkisu! Bilkisu! Sulaiman ya ingi zata, caraf ta dawo daga wanna mummunan mafarki zatace ko tunani, ita dai tasan a zahiri taga wannan abu ya faru, lafiya me kike tunani haka? Sulaiman ya katseta, waige-waige take da idanuwata cikin mawuyacin hali, ke meye? Meya faru? Jin ta kama hannuwanshi ta jinike da nata, a jiyar zuciya yayi, karki damu masoyiyata insha Allahu zamu isa gida lafiya, gobe irin wannan lokacin kina gaban Umma, ya fada yana zolayata, duk day a kokarin da tayi wajen gani tayi murmushi ta kishingida dai-dai wajen ‘yanBauchi aka ajiye su, sune passengers na farko da suka fara loda a motar, bayan an saka masu kaya a mota, suka shiga ciki mota suka zauna suna jiran zuwan sauran passengers, zaunawar su keda wuya dum! Sukaji ko ina yayi rufe da wani matsanancin duhu smai tsananin muryoyi sukaji kala-kala ta yadda ba zasu iya tantance ko murya mace, namiji? Ko kuwa karamin yaro ba. Gargadinsu a kayi da murya mai kaushi akan suyi gaggawar fita daga cikin motar na su koma ya zuwa gidansu da suka baro, muddin kuwa sukace zasuyi taurin kai, kuwa zasu hadu da matsanancin hadarin motar da zatayi sanadin halkar duk wani passenger da ke a cikin motar, sanna kuma aka wayanda basuji basu gani ba, domin kuwa driver matarshi ta haihu kwana biyu yayi saura ayi biki, idan sukayi sanadiyar mutuwar wazai dauki nauyin iyalishi kuwa wanda yake kan gaba a kusa da driver dan makarantane shi kadai ne namiji a gidan su, mahaifinsa ya rasu mahaifiyarsa ke wahala wajen ganin ta biya masa kudin makaranta. Ita kuwa wannan matar ‘yaranta duka biyu marayu ne ‘yan uwan mahaifinsu sun kwace musu dukiyarsu, wajen ‘yan uwanta zataje neman agaji. A haka akaci gaba da lissafo musu ko wane passenger da abinda yake kunshe dashi duk domin dai so fita daga cikin motar bayanta aka gama gargadinsu, wayau! Sukaga ko’ina ya yaye, kuma motar da suke ciki hart a cika da passengers, kamar yadda aka shaida musu haka kuwa suka gani, duk wayanda aka lissafa musu a motar su da ne ke ciki. Kallon juna sukayi ba yareda sun samu dammar furta wata kalam ba, wayar direba ce yita wau kara, dauka yayi tareda sallama, slamu alaikum lafiya kalau wallahi, a’a alhamdulillahi mun gode Allah, amen, amen, sosa kunnenshi yayi yana ‘yar dariya, eh saura kwana biyu ma ayi bikin ai ina Allah ya yarda. Dam gabansu yafadi suka sake duban juna da karfi, tare suka hada baki dakata!! Duk motar kowa ya jiyo ya ba, ana saka kayane a but da hanzari suka bade murfin motar suka fito, mun fasa tafiya Sulaiman yace gaywa condester, don Allah kuyi hakuri wallahi mun fasa tafiyar me kace malam, kamar ya ya kunfasa lafiya wanna aima maganar banzace, duka mutanen wurin suka taso wasu na bayadda hakuri wasu na zugawa, anan dai aka samu wani dattijo mai hankali da sanin ya kamata, yace tunda ai ga wasu passengers nan ba sai kawai su shiga a madadin wayannan ba, ai wannan abun bai kai na wani dogon bayani ba, sukayi masa godiya suka nemi a dai-daita sahu suka sake saka kayansu suka nufi gidansu da suka saka baro, suka bar mutanen garage din kowa tana mamakin wayannan mutane haka, su kadai suka san dalilin da yasa suka bar motar, ba kuzari mai adai-daita ya sauke su a kofar gidansu, said a suka yi kamar minti bakwai a tsaye suna kallonn-kallo sanna Sulaiman ya bude gida suka dunguma a ciki, ga baki daya duniya tayi masu zafi komai ya kulle musu, sun ma rasa ta inda zasu fara bamai cewa kowa ko kala, suka isa bakin kofar falo ya saka key a ciki yana kokarin mirdawa ya bude kofar falon, kiririn,kirin wayar Sulaiman tayi kara su duka suka zabura da karfi, hannu yakai aljihu ya ciro wayar, sunan mahaifinshi ya gani ya bayyana a gaban screen din wayar shi, dauka yayi, yayi kokarin boye duk wata damuwar shi, da ke tattare dahshi, slamu alaikum Abba ina wuni lafiya kalau, lafiya kalau take, komai Alhamdulillahi, Na’am Abba na nameye ya tambaya yana mai nuna mutukar mamakinshi a filli kamar a gaban Abban nasa yake, kallonta yayi da hanzari eh yayi murmushin yake yace amen, har yanzu kallonta yake yi, to amen baba ehan, ya katse wayar har yanzu kallonta yakeyi, ga baki daya hankalin shi a tashe yake itama kallon nashi take yi, meye ta tambaya tana kallonshi wai Abbane yake tayani murya, wai a dazun nan Ummata ta kira ki a waya, kika gaya mata mun dawo ne daga Asibiti likita ya tabbatar mana da cewwa kinda juna biyu na tsawon wata biyu, dirshan ta fadi zaune barkewa tayi da wani matsanancin kuka, shima, sulaiman zama yayi a dai-dai kusa da ita sai dai wannan karon ba lallashinta yakeyi ba, hada tagumi yayi ta fada kogon tunani, shi ba abinya fada ta gida ba, a can hankalin su ya tashi, kuma ma zai iya yuwa idan wani yace zaizo a kasheshi a kan hanya sunfi minti goma anan zaune, sa’annan Sulaiman ya mike ya iyadda bude kofar falon su duka suka shiga ciki, jawo akwati takeyi itama suka nufi daki ji tayi kamar an ja mata kafa jicce ta fadi kass ram! Yunkurawa tayi ta tashi amma ta kasa, wasu taurarin wahala ta ringa gani sunayi mata yawo, yarda tashi akwatin yayi ya nufo inda take da gudu, yanka kokarin tada ta, lumshe idanuwanta ta farayi, tun tana iya budsu har takai ga duka suka rufe rungumeta yayi ya kwala uwar ihu, da hanzari ya tallabeta da gudu ya fito baima tsaya ta wani rufe gida ba. Mijin Khadija yayi kicibis dashi ya dawo, da karfi ya tsayadda mota, Sulaiman da gudu ya shiga, Asibiti, asibiti! Da isarsu asibiti aka daurata saman keke da gudu aka wuce da ita emergency, gaf aka rufe kofar emergency aka dakatar dashi daga yunkurin shiga cikin dakin da yayi, jiginawa yayi a jikin bango emergency zaune yayi a nan wurin ya fara kuka ne ya ringa lallashi da kyar da sidin goshin daina hargowarda yake ya zama hawaye kawai ke zuba daga idanunsa, nurse c eta fito da fara’arta da kafri suka mike su duka sister ya lafiyar jikinta, zan iya shiga yanzu, don Allah ku bari na shiga nag anta, Sulaiman k eke jero wayannan zancen duk shankalinshi a tashe relax malam cogratutaltion ma, wani kallo yake mata me kikace? Cewa nayi congratulation matarka na dauke da JUNA BIYYU na tsawon wata biyo, kuma zaka iya shiga ka ganta, za ma kaiya tafiya da ita, because she is out of danger known. Bai jira ta kommala jawabinta ba yaruga da gudu zuwa cikin inda dearest dinshi take, zaune ya taradda ita tana kallon yan yatsunta tsaye ya tsaya cak, kamar tasan dashi ta daga kai suka hada ido, ya karaso inda take ya rungumeta yana zubarda kwalla, Alhamdulillahi kin tsoratani, don sAllah kada ki sake yimin irin haka. A nan aka sallame su daga asibiti maigidansu Khadija ya maidasu gida, sukayi masa godiya sun ma rasa zaune kawai sukayi kamar masu ansar gaisuwa, kiran mariba akayi, suka tashi sukayi alwala, ya jagoranceta sukayi sallah, mikewa yayi ya fada kichen a dafa mata indomies, a wani bangare na rayuwarshi harga Allah dadi yakeji mara misaltuwa, matarshi nada ciki, kenan zai zama baba, zubo indomie yayi a flate ya kawo masu a nan bedroom dinsu tareda rowan da zasu sha, aka kira isha’I suka mike suka sauke farali, suka jawo kwanon abinci sukaci sukasha ruwa, ta tashi da dauki kwanuka da ni yar ta kai kitchen karaf ya amshe, no wannan ba aikin ki bane yanzu, zauna ki huta, kada ki wahaltamin da baby, duk da irin halin da suke ciki said a tayi yar dariya, duk kunya ta lullubeta, ya dauki kwanuka yaje ya ajiye ya dawo, suka yi addu’a suka kwanta. Wayyo!! Wata kara aka buga mai mai matukar firgitarwa zunbur suka sauka daga kan gaso jan abu sukaji anayi a falo, kasan tys idan ana jan abu akanshi zai ringa bada wani sauti daban, kuka sukeji anayi matsananci, a hankali suka tattaka ya zuwa bakin kofar daki yaddazasu iya hango abinda ke faruwa a falon, da baya sukaja da kafri saka makon ganin wanan tashin hankali da basu taba gani shi ba, wata mace ce ko ince budurwa wace bata wuce shekara goma sha takwas zuwa sha tara ba, ake ja, batareda suna ganin mai jan nata bag a baki daya jikinta jinine faca-faca, kama kuwa kadan ya rage ya rabuda gangar jikinta, rokonsu take tana kuka don Allah ku taimaka mini, karaja sukeyi da baya suka rungume juna suka kankame waje daya, wuf tayi ta nufo su da niyar ta cafke su, kamar an wulla ta ta fada can gefe daya, sake mikewa tayi kanta yana shillo ta kara nufo su amma kamar a karon farko ma sake wurgata akayi, kuwa take kala-kala iri-iri tana yunkurin kamasu amma ta kasa, su kuwa suka buga suka kara ja da baya suncakankame juna, duk wani yunkuri, na shiga cikin dakin tayi amma ta kasa Sulaiman ne yayi karfin hali ya ja kofar daki ya rufa da karfi ya dawo daga baya. Duk hargowarda takeyi a kunnuwansu yake, addu’a suka yi suka tottafa ko’ina suka haye kan gado ko runtsawa ba wanda yayi-sai yanzu Bilkisu ta gano dalilin da yasa ta kasa shigawa acikin dakin, maganinda baban nan ya btane, haka suka zauna ba wanda ya koda runtsa idanuwashi, sai a shiyoyin asuba su duka bacci ya sace sub a tareda sun sani ba Sulaiman ya fara falkawa, kasa rufe bakinsa yayi sakamakon kashin ganin matarshi da yayi akan gado, kofa ya gani bude, a hankali ya tashi ya fara tafiya yana duba kofar, can ya hango Bilkisushi a falo zauna murmushi, zo dearet, zo mu karanta Qur’ani kama meye yayi kadan ya cuta mana, shi nake karantawa kazoo mu sauke Qur’ani a yau dinna, ajiyar zuciya yayi ya sauke nunfashi da karfi okay bari na dauko nawa Qur’anin, a’a ai gashi na dauko duka zo kawai mu karanta, fitowa yayi ya nufa ci falon ya tsallaka ya fada cikin falon, sai dai kuwa abinda bai saniba Bilkisunshi tana kwance sa bias gado tana sharer bacci abinta. Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka itama kamar yadda Sulaiman yayi haka itama ta fara duban mijinta har a toilet ta dubashi bata ganshi ba cak ta tsaya da taga kofa a bude, a hankali ta fara tafiya ta nufaci kofar da zata kaita falo wani faduwar gaba taji da bugun zuciya tsallako kofar tayi ta nufo mijina kam ta kame tsaye akan matsanancin tashin hankalin da taji, mijinta dearest dinta ta gani a zaune da wasu kananan kayan da hula da wasu rufaffun takalma kai! Sak shigar USMAN! Yadda yake zama, yadda yake kada kafa daya juye hularda yake yi kai! Kome sak na MAN! Daga kai yayi ya fara dubanta tun daga sama har kasa, itama suban nashi takeyi, nikewa yayi kau!! Ya wanka mata wani hatsa bibin mari said a ta fadi ta fasa bakin ta, kamar wanda ya dawo daga hayyacinsa y ace cikin wata murya wadda ko ba’a gaya maka ba kasan mace c eke wannan murya, yanzu idan Usman yaji yanda nayi miki fa ya fara dube-dube kamar wanda yaga usman din a falon, da karfi kuma ya juyo ya kalleta kallo irin na mugunta da tsananin kiyayya yaci gaba da Magana wannan dai ta mata, idan na kasha ki ai bai zai taba sani ba yana fadi yana cize hakoranshi, ya nufaci inda take ya sa hannun ya cafko wuyanta ya dagata dashi sama har ya cirata har karfi aka banko kofar shigowa falon! Tsohon nan ne da suka saba dashi, da karfi ya wankada mashin wasu ruwa da suke rike da hannunshi, wai gowa Sulaiman din yayi da karfi suka hada ido da tsohon, wurgarda Bilkisu yayi da karfi ya sheka ya nufi bangon falo tuma yayi ya tsunduma cikin bandon baya bace. Baban yaje ya tayadda ita kuka takeyi kamar ranta zai fita, ba dai Usman ne keyin duk wannan abinda ke faruwa ba, take fadi tana kuka mai tsanani. Ba Usman bane ke muku wanna abun amma sanadiyar sa ne duk wannan abun ke faruwa, how? Tayaya? Ina mijina kuma wane sanadine na Usman aka da yake faruwa dan haka ta fada tareda zubewa a kasa tana kuka. Gyara zama yayi ya fara fadi mata kamar haka --------
        Ku biyoni a littafi na biyu dan jin cigaban kayatacce labari.
Taku mai debe muku kewa Asiya Sadiq Maccido
(Asikhan)
Tel: +2349037433171

https://myscvonline.blogspot.com/2019/03/hubbul-yaqeen-payment-method.html
              

Wednesday, 4 April 2018

HUBBUL YAQEEN SERIES 4


HUBBUL YAKIN cigaba 4
  
ASIYA SADIQ MACCIDO
(ASIKHAN)

Copyright © Asiya Sadiq September, 2017
Hakkin Mallaka (M) Asiya Sadiq September, 2017

Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State, Nigeria
Website: www.hausacc.ml
Tel: 08113777717

Book 1 of Hubbil Yaqeeen Series



A haqiqanin gaskiya taji dadin zuwan su matuqa domin tayi fira sosai dasu gaskiya gwanayene wajen  bayar da dariya sai faman dariya suke sta, kuma sun tattauna abubuwa masu muhimmanci wanda ya shafi aure, kasha gari da safe sbayan Sulaiman ya wuce office ta shirya tana zaman jiran habiba isowar habiba yar aiki su Khadija bata wani dade sosai ba tazo suka wuce sai gidan mai kitso: Habiba tayi Sallama dasu ta wuce tayi sa’a kuwa bata cimma kowa ba ita kadai ce suka gaisa da inna Kande tsohuwa dattijuwa da ita mai kirki, zauna yan nan ki jira na dan dama kokon nan kinji ta shimfida  mata tabarma Bilkisu ta zauna ita kuwa taje tadama koko ta sauke ta zuba a wani bokiti mai murufi ta kai daki ta ajiye ta fito. Sannu da zuwa fah, ince dai kona tsaidaki ko kiyi haquri fa, haba inna ba komai ai Bilkisu ta fada tana maid an murmushi. Kujera ta dauko ta zauna wane iri za’ayi? Kitson ulu nakeso tau sai ki juyo a fara aiko. Kitso take suna dan fira, basu dade da fara kitso ba sukaji Sallama, wa alaikissalam ah hajiya Larai sannu da zuwa, wata babbar mace c eta shigo suka gaisa sa juna. Kai bari kallah kitson nan yayi kyau sosai, murmushi kawai Bilkisu tayi ya sunan ki sunana Bilkisu, yarinya mai hankali da nutsuwa nan dai aka fara fira da matar, ita dai sba mai fara’a bace sosai irin mutanen nan ne da basa son Magana ba ruwanta, ita dai har a ranta Bilkisu ta shiga a zuciyanta. Bayan an kamala yi ma Bilkisu kitso ta bude Jakarta ta dauko wata leda wanda ta rikowa mai kitso,sabulai ne na wanka dana wanki ssai man shafi da turare ta ajiwa mai kitso tayi godiya. Kai! Alhamdulillah nagode sosai buki inna Kande ce da murnanrta sosai wane layi kike ne domin ban saba ganinki ba. Anan bayan naku nike gaidan mu yana kallon bayan ginar church dincan mune karshen layin da karfi. Inna Kande tace gidan gate kalar madara da baki a firgice, ita kuwa hajiya Larai da take zaune mikewa tayi zumbur da karfi firgice lafiya inna meya faru kika firgice haka na fadi wani abune ku gayamin a’a ba komai Bik ai---ai--- inna Kande bata samu dammar iyadda maganarda takeyi ba, ji kawai Bilkisu tayi an cakume tad a karfi an shaketa, ina dana? Hajiya laraice ta shaketa take mata wannan tambayar a gigice. Bilkisu ke kokarin kwatar kanta nace ina dada? Ki fito min da dana abinda taci gaba da fadi kenan da kyar inna kande ta kwace Bilkisu a hannunta t samu ta riketa shieka Bilkisu yi sauri inji inna Kande, daukawa tayi ta dauki jakar tat a wuce da karfi  said a takai bakin kofar fita tadan juya har yanzu hargon wa Hajiya Larai keyi tana fisge-fisge ku fitomin da yarona Bilkisu ki shega nace tsawa inna Kande ta bugamata, ai kuwa da gudu ta fita. Ga baki daya kan Bilkisu ya kulle tafiya kawai take amma hankalinta baya ga inda take tafiya. Shin ko dai hajiya Larai mahaukaciya ce? Amma kuma bata da alamun hauka, ko kuwa irin mahaukatan nan ne da haukar keyi tana taso musu? Can taji kamar a kunnenta maganar inna Kande “gidan gate kalar madara da baki?” hakika hajiya Larai ba mahaukaciya ce ba domin inna Kande ma a tsorace ta fadi wannan maganar, to wane yaronta kuma? Me yasa su suka suka firgita dajin gidan da take? A dai-dai lokacin da ta’iso kofar gidanta kenan, kicibis tayi da Sulaiman Bilkisu kin dawo har an gama kitson? Firgigi tayi kamar wadda ta tashi daga barci kallon shi kawai take batare da tace masa uffan ba lafiya tambaya yana meya faru Sulaiman ya tambayeta yana mai cike da fargaba hida da tsoron kallon shi kawai take gaba dayi kamar wata bebiya ta kasa furta kome. Hannunta ya janwo ya shiga da ita cikin gida bayan ta zauna ya sake tambayar ta Bilkisu lafiya meke damunki ne bata fasa kallon da take masa baga baki daya ta kasa Magana kamar wace aka rikewa harshe duk jikinta ya mutu tarasa meya sameta da kyar taji bakinta ya fadi bacci nakeji tare da wata hamma mai tsayi, to zo muje ki kwanta girgiza kanta kawai tayi alamar a’a sai kuma ta miqe kafa a nan saman kujerar da take bisa ta kwanta idanuwanta taji suna budewa suna kullewa sannu a hankali, nan take bacci ya kamata. Ita ce bata farka ba saida akayi isha’I, a hanakali ta bude idanuwanta tayi arba da Sulaiman take Bilkisu kin farka? Daga kai tayi ta bishi dany tace abinci lafiya naga kai bakaci ne murmushi yayi ai naci nawa wanna naki ne, maida masa tayi da murmushi to ai ni yayimin yawa dariya yayi nima dai nasan da haka kici kawai wanda zaki koshi harki damu da sauran to a ina ka siyo shi yayi dadi fat a fada tana dan kallonshi wani restaurant ne ko dalili sunan shi nan dai tace abinci ta koshi tasha ruwa masu sanyi hankalinta ya dawo jikinta. Nace ba Bilkisu dazu mun fara Magana sai kikayi bacci meya faru dake ne dazu? Ince dai lafiya ko? Ai kuwa nan take komai ya dawo mata kamar yadda ya faru dazu a gidan inna Kande mai kitso a tsorace ta fara bashi labara kasan meya faru dazu bayan naje wurin kitso har an faramin sai ga wata mata tazo ----- baran wani almajiri ya katseta almajiri yau a gidnmu Bilkisu ta fada tana mamaki, a kinga kuwa bamuyi asarar abincin mu ba saiki dauki saura ki zuba masa ki dawo kici gaba da gayamin abinda ya faru dazu to ta fada tare da daukan sauran abinci ta nufi almajiri zo ansa da hanzari ya shigo ya gaidata dan qarami dashi taro kwanon ka a taro kwanon shit a juye masa, nag ode Billy! Da karfi tadago me kace tasan duk/a fadin duniyarnan ba wanda ke kiranta Billy idan ba “Man” dinta nada ba kuma yama akayi yasan da sunanta me kace da karfi ta sake tambayarsa dagowa yayi yace cewa nayi nagode Hajiya ajiyar zuciya tayi cikin ranta tana mai godewa allah daba yadda taji ya fada ba, a cikin ran nata ne ta juya zata wuce domin taje ta idarma Sulaiman da labarinda ta fara bashi mai dauke da al’ajabi da kuma firgici ji kawai taji almajirin yace “ba wani tsoron da kikaji dazu Billyn da kikaji da farko na fada shi dai na fada tsayawa cak tayi ta daina tafiya a hankali ta fara juyawa maganarda tayi a rai wadda ko fatar bakintabatasan anyi baya akayi shi ya jiya Billy fah yace idonta a zare hankalinta a tashe a firgice ta nunashi da yatsa me kace sake maimautawa. Rike yake da kofar gate din gidan qafarsa daya ciki daya yana fuskantar ta ya bude baki yafara Magana “kowane mutum yanada lokacin shina tsoro inayi miki bushara da yanzu lokacin tsoron ne da firgici da tashin hankali a gareki da kuma mijinki Sulaiman daga yanzu kwanciyar hankali ta kaurace Mukuhar ----- bata jira ya I darda maganar da yakeyi bat a fara ja da baya baya ta wurga da kularda ke hannunta ta runtuma da gudu ya zuwa cikin gida. Da gudu ta fada falo Sulaiman ya mike ya dai wai Bilkisu meke daminki ne iye? Abinda almajiri ya fada mata duk ta kwashe fada mishi, tana Magana cikin firgita da ruduwa kuma a tsaye take bashi labaran ha ta kamala sai dai kuma daya a cikin labarinta ta boye almajiri ya kiramata wato Billyn da taji almajiri ya kirata dashi, dalilinta kuwa anan shine tana jin tsoron ta yadda Sulaiman zai kalli al’amarin ne kallonta yake yi idon sa a zare kai da gani kasan yana cikin tashin hankali, lokaci daya idanuwanshi suka ciko da kwallah da kyar ya samu ya iya zaunawa akan kujera, a da-dai lokacin kuwa Bilkisu durkushewa tayi kasa tana tsala uban kuka, ganin halinda ta shiga yasa Sulaiman ya tuna shifa namijine don haka yayi yake ya ta yadda ita ya zaunar da ita akan kujera kada ki damu Bilkisu koma me ne yake shirin faruwa, damu Allah nanan shine gatanmu, bata jira ya idar da abinda yake fadi bata tari nunfashin sa wallahi bana iya zama anan gidan, ko kwana daya bana karayi a cikinsa, tun ranar da nazo nake cikin fargaba da tashin hankali mara misaltuwa, ni bana iya zauna cikinsa ta kawo dai-dai nan ne ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi don Allah na rokeka ka maidani gidamu ka kaini garinmu bana son wanna garin duk tausayi ya kama Sulaiman hakika da gaskiya Bilkisu akwai wani mummunan abu dake biyarsu, tabbas akwai wani boyayyen al’amari a tattare da gidan nan da suke ciki. Bilkisu ki saurareni ki natsu da kyau koma menene nayi alkawarin zamu bar gidannan gobe zanje na nemi transafer dole ne mubar garin nan, yanzu ne taji sauki a ranta sossai, zo muje mu kwanta in Allah ya yarda komi yazo karshe Bilkisu. Ta shi tayi ta biyo shi tare sukaje suka kulle kofar gidan sannan suka wuce daki yayi addu’a akoina ya tofa itama Bilkisu haka suka kulle daki suka kwanta duk da kasancewar ba wanda bacci ya dauka cikin su. Kamar wadda aka gwanta ta tashi da sauri ta girgiza Sulaiman tashi-tashi sai dai abinda bata sani ba bacci yakeyi bad a sauri ya tashi lafiya wani abinne kuma? Menen? Gobe idan zakaje office neman transfer tare zamuje ko domin bazan iya koda second daya a gidannan ni kadai ba wallahi. Ajiyar zuciya yayi game da murmushi da yaji akan wannan bin ne kafin nawuce zanyi waya da abokin aikina Nuhu kinsan yanada ‘yaya mata masu dan girma kuma kinsan gobe ba skull kinga sai suzo su tayaki zamam har na dawo kinji to ta fada tare da da’a kai alamun ta gamsu da haka. Kasha gari asuba daya daya tashi baije masallaci ba domin samin halinda suke ciki, shi dai gurinshi su bar garinnan lafiya, bayaso wani abu ya cutarda su musamman ma Bilkisu. A hakikanin gaskiya sanan kanshi ne akwai abinda yake faruwa a gidannan, shima kanshi ba saudaya ba basau biyu ba yasha jin abubuwa a gidan sanna kuma yasha garin sai dais u kama yi masa kamar dabo, baifi sati biyi bad a ya fito daga wanka yazo a dressing mirrow kawai wani kato ya gani a bayanshi hankali a game da katon shine a gefen fuskarshi tun daga samamn girrshi harya zuwa kumatunsa wani irin mummunan rauni ne yank ace babba wadda har kama hango kashin fuskarsa, jinni ne yake zuba kamar fanfo daga mummunan raunin har ya rife masa gaba ki dayan fuska, da karfi ya juya amma ba’a mamakinsa ba wannan katon ba dalilinsa suke maida duban sa yayi ya zuwa madubi sai kuma ya sake ganin wanna katon da karfi ya juya zai fita yabar dakin sai ga Bilkkisu ta shigo kannewa kawai yayi domin kada ya fada Bilkisu ta firgita kai abubuwa ba iyaka da suke faruwa dashi a gidannan, lallai akwai boyayyen alamari, a dangane da gidannan numfashi ya sauke sa;annan ya tayar da Bilkisu domin ta tashi tayi alwala suyi sallah. Bayan sun idarda sallah ga musu break fast suka ci, ya tashi taje yayi wanka, Bilkisu bata yarda ba’a bakin bandaki tashi dai abin dariya ma ya koma yana bashhi, har ma dai lokacin da tace itama sai ya jirata a bakin bandakin tayi nata wankan domin ita sambata yarda ta fada bandaki ita kadai ba dolen shi ya zauna yayi gadinta hart a kare wanka yanata faan yimata dariya, ita kuwa ko a jikinta, ita dai kada yayi nisa da ita. Bayan ya kamala shiryawa yace mata shifa zaije ya nemo transfer dinda ya gayamata daga nan kuwa zai wuce gidan wanda ya basu haya domin ya sanarda shi sufa zasu bar masa gidanshi. Nnfa kawai, wata sabuwa inji iyan caca!! Alan baran taki yarda sam ita ba ba inda zaije ya barta. Ke tunfa a jiyannan nayiwa Nuhu text akan cewa ya kawo diyan shi a yau a gidanana suyi mana wuni, kinga shima yayimin reply kinga danna wayarshi shima ya nuna mata reply din Nuhu ta gani da kanna in allah ya yarda duk da haka said a kyar sannan ta yarda zata zauna da sharadin zata zaunaa kofar gate har Nuhu ya kawo yaranshi tukunna kafin nan su dunguma su koma cikin gida. Ya ya iya haka ya amince ta biyoshi suka fito tare, sunyi sa’a kuwa domin a bakin kofar gidan su. Ajiyar zuciya su duka sukayi. Sulaiman ya fara Magana Alhamdulillah baba kazoo akan dai dai lokacinda ake bukatar zuwanka cikin rashin gamsuwa da abida suka fada ya tambaya a dai-dai lokacinda ake bukatar zuwana? Me kuke nufi su duka suka fashe da dariya Baba wani tsoro takeji n tafi na barta ita kadai a cikin gida, tunda yanzu gaka ba sai ka tayata zamaba. Murmushi yayi mai hadeda ajiyar zuciya eh zan iya tayata zama daga nan wajen har kaje kadawo daga inda zakaje, ga baki daya suka sake dariya, ai ko aciki baba zaka iya shiga mu a wurinmu ai kai tamkar dan uwammu ne na jinni sulaiman ya fada a-dai-dai lokacinda yake shirin tada mashin dinshi, a’a nikam dana ai lokaci shigowana baiyi ba tukum, idan lokaci shigana cikin gidanku yayi bama sai kun kirani bada kaina zan shiga. Allah ko Baba Sulaiman ya fada a dai-dai lokacinda mashin dinshi ya tashi ya bashi amsa kai tsaya to Allah ya kaimu lokacin ya tuka mashin dinshi yayi gaba murmushi, suka sake su duka tareeda fadin amen, a nan Bilkisu a zauna suka dan fara hira da juna, Baba ne ya tambayeta ‘yata me yake baki tsoro cikin gidanku da har kike shakkar zama a ciki? Sai da ta danyi jim sanna ta iya bude baki ta fara gayamasa abinda ya dace ya sani bayan takai aya, yayi dogon numfashi daga ganina gujewa bla’I bashine tsira daga bala’I ba, fuskantar bala’In shine masalaha, irin wayannan abubuwa suna faruwa daku kuntaba samun dama kuka tambayi kanku shin meye dalilin faruwar duk wayanan abubuwa? Tabbas akwai dalili, dalili mai girma, da ganan kuwa har zuwa Birnin sin in kunje ba zaku tserewa faruwarsa ba. Diyata ina mai baki shawara duk da ba, za ki fuskanci koma meye yanzu gadan abinda zan iya taimaka miki dashi yasa shannunshi a cikin babbar rigarda ke sanye a jikinshi take cikin yanayi na rashin gamsuwa kana ta mika hannu ta karba. Bilkisu koda ni mai cutarwane bazan taba cutar daku ba ki duuki wanna maganin duk wata hanya da kikasan wurine da ake iya shiga cikin gidanki, ma’ana bakin kowace kofa harta bandaki ki zuba maganin, yadda kuwa zaki zuba kereriyar kofar zakibi, kina zuba maganin tun daga farko ta har karshe, karki damu kome muguntar abu bai isa ya ketare takan layin nan ba, kuma koda kin share maganin, aikin shi yanan bazai goge ba, abu daya kawai ke ruguza maganin shine idan ruwa ya zuba a inda aka zuba maganin, ruwa anan ana nufin duk wani abu da bane ina fatan kin fahinta, daga kai tayi eh Baba na fahinta nagode sosai Allah ya saka da alkhairi amen, tashi ki shiga cikin gidanki ba abinda zai sameki kinji yanzu ya zama mini dole na tashi na bar wurinnan ba domin naso ba. Ji tayi matukar karfafa mata guiwa ta tashi ta shiga cikin gida kai tsaye, da isarta kan kujera ta zauna kalaman Baban nan suka ringa fadomata a rai kwata tawata ta rasa ta inda zatasa kalaman nashi, shin gargadinta yakeyi ko kuwa shawara yake bata, koma meye yau zata saka maganinda ya bata kuma zata ga karshen koma meye kafin gobe su kaura ya zuwa garinsu, murmushi ta saka wani irin dadi taji ya ratsa zuciyarta. Aunty taji ankira da karfi, juyowa tayi su Ummi ta gani tana murmushi har a ranta taji dadin zuwansu, sai a yanzu kuka zo, waya kawo ku Babamu ko? Ina yake ne. amina ce tace ya wuce shine ko shigowa baiyiba, ku zo ku zauna, aunty sa mana nicklochen sukayi zamansu, suna masu nishadi, sai fara’a take yaran akwai su da shiga rai, sai dai abin mamaki zuwansu da salo Ummi kuwa shiru-shiru ba ruwanta, har iyayen suna fada ko Magana batason yi idan dai bata zama mata doleba amma a wannan karon itace mai baki karma bakin nata da salo ya zarce na Amina a wannan karon ita kuwa Amina itace ba ruwanta a wanna karon.
Zamu cigaba Insha Allahu 

Saturday, 31 March 2018

OYOYO MASOYIYA TA


OYOYO MASOYIYA TA

Oyoyo masoyiya ta
Oyoyo zan baki gata
Oyoyo kaunar ki jata

Kaunar ki ta zama tsarin zuciya ta
Ke ce wacce na baiwa raggamata
Zo gani ki bani gata

Oyoyo sai na yaba ta
Kaunarki ce abin fadata
Sadiya kin basu rata

Yau gani ina ta fata
Na so ace kudduri da fata
Sun cika yau na bata gata

Me yasa so yake da sata
Nan take zuciya ya sata
Yabi jini da jijiya ta

Gaki fara kuma kina da tsafta
Doguwa ce ga ido an bata
Tafiyar ta tafi ta, ai ta tsere mata

Ina sonki ya masoyiya ta
Kaunarki tana a zuciya ta
Zo gani ki bani gata

Sadiya ce masoyiya ta
Kaunarki ina fadarta
A zuci kuma baki ya furta

Na aminta da son tauraruwa ta
Mai tsari irin na mata

Kizo gani ki bani gata

Tuesday, 21 February 2017

MAGANGANUN HIKIMA KAN SO: Soyayyar Gaskiya


MAGANGANUN HIKIMA KAN SO: Soyayyar Gaskiya


Babu wani lokaci ko wani mazauni na soyayyar gaskiya. Tana faruwa ne batare da sani ba, a cikin bugawar zuciya, cikin faskawa guda, zai samu bagire na din din din”.

Written by:
Sharahbil Muhammad Sani