OYOYO
MASOYIYA TA
Oyoyo
masoyiya ta
Oyoyo zan
baki gata
Oyoyo
kaunar ki jata
Kaunar ki
ta zama tsarin zuciya ta
Ke ce
wacce na baiwa raggamata
Zo gani ki
bani gata
Oyoyo sai
na yaba ta
Kaunarki
ce abin fadata
Sadiya kin
basu rata
Yau gani
ina ta fata
Na so ace
kudduri da fata
Sun cika
yau na bata gata
Me yasa so
yake da sata
Nan take
zuciya ya sata
Yabi jini
da jijiya ta
Gaki fara
kuma kina da tsafta
Doguwa ce
ga ido an bata
Tafiyar ta
tafi ta, ai ta tsere mata
Ina sonki
ya masoyiya ta
Kaunarki
tana a zuciya ta
Zo gani ki
bani gata
Sadiya ce
masoyiya ta
Kaunarki
ina fadarta
A zuci
kuma baki ya furta
Na aminta
da son tauraruwa ta
Mai tsari
irin na mata
Kizo gani
ki bani gata
No comments:
Post a Comment