Saturday, 31 March 2018

Wasikon Soyayya Series 6


Dare da rana kai ne abin tunani na
Aminci ya tabbata ga farin cikin zuciya

Bayan gaisuwa da fatan alkhairi ina gabatar maka da wannan sako ba don komai ba sai don tuna tarwa a gareka da irin soyayar mu.

Masoyi na, kada ka manta a dare da rana kai ne abin tunani na, a duk lokacin da nakwanta idan har ba muryar ka na jiba to faufau ni da bacci munyi ban kwana, yau kimanin shekara biyu da yan kwanaki kenan da na kamu da sonka amma na kasa na sanar da kai nayi kokarin nuna alamu amma sai nake ganin kamar baka ma san inda na dosa ba, Ibrahim ka sani cewa bazan iya rayuwa ba idan ba tare da kai ba, Ibrahim kai ne kadai zaka iya zamuwa gata a wuri na, shin me yasa zuciya bata jin rarrashi ne?, ni da kai na na sani Ibrahim ya san irin zafi da kuncin da mai so kan shiga idan har bai samu gata ba a inda yake nuna soyayyar sa ba. Ibrahim me yasa idan ina nuna maka kauna da tausayi da kuma kulawa lokacin kake kauracewa a gareni? Ka da ka manta shi so hallittace kuma jaraba ce kuma baka sanin lokacin da yake riskuwar ka kamar yanda baka sanin kiskuwar mutuwar ka.

Tunani na ya yanke basira ta ta dallashe, shawarwari na sun kare, boyon da nake ya kai karshe yau ne ranar da ta zamu ranar tarihi a wurina. Ina sonka, ina kaunar ka Ibrahim, bazan taba mantawa da kaiba, ka aminci da ni.
Kaunar ka nake dare da rana
Aisha Abubakar

1.   Oyoyo Masoyiya ta
2.   Na aminta da ke
3.   Kin kasance farin ciki
4.   Ina kike mai So na


No comments:

Post a Comment