Saturday, 31 March 2018

Wasikon Soyayya Series 5


Garabasa
Farin cikin zuciya ta

Assalamu alaikum,

Ya ke farin cikin zuciya ta kuma sanyi idanuwa, hakika ke cewa face ta farko wacce na yi gamu da ita, bantaba zato ko tsammani ba za’ayi wata ‘ya mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi kankantar lokaci ba, amma sai gashi ba tsammani nayi kicibis da kyakkyawar muskar da na kasa dauke wa kallo.

Hakika tun lokacin da idaniya ta kalle ki zuciya ta kamu da ciwon sonki, na aiko miki wannan sako ne ba don komai ba sai don na rasa irin hanyar da ya dace na biyo kwana da kwanaki ina tunani da irin hanyar da zan biyo ta sanar da ke wannan cutar da Allah ya yi min jarabawa da ita, amma ina, na kasa na yi tunanin samun ki a makaranta domin na sanar da ke irin kaunar ki da ke kunshe a cikin zuciya, sai naga ba mafi sauki irin rubutu miki wannan wasikar.

Ka da na cikaki da surutu ya ke hasken zuciya ta kin riga kin zamu ginshikin rayuwata, ina sonki, ina kuma kaunarki, a kullun ke ce abin tunane na, zan rasa dukkanin farin ciki idan har ban samu amincewar ki ba, hakika zuciya zata dan dani wata irin azaba idan kika ce bakya tare da ni.

Daga karshe ina miki fatan alkhairi, ina kuma sauraru daga gareki, nagode.
Masoyin ki na har abada
Ahmad Muhammad Kabir

No comments:

Post a Comment