Showing posts with label Love SMS. Show all posts
Showing posts with label Love SMS. Show all posts

Saturday, 31 March 2018

OYOYO MASOYIYA TA


OYOYO MASOYIYA TA

Oyoyo masoyiya ta
Oyoyo zan baki gata
Oyoyo kaunar ki jata

Kaunar ki ta zama tsarin zuciya ta
Ke ce wacce na baiwa raggamata
Zo gani ki bani gata

Oyoyo sai na yaba ta
Kaunarki ce abin fadata
Sadiya kin basu rata

Yau gani ina ta fata
Na so ace kudduri da fata
Sun cika yau na bata gata

Me yasa so yake da sata
Nan take zuciya ya sata
Yabi jini da jijiya ta

Gaki fara kuma kina da tsafta
Doguwa ce ga ido an bata
Tafiyar ta tafi ta, ai ta tsere mata

Ina sonki ya masoyiya ta
Kaunarki tana a zuciya ta
Zo gani ki bani gata

Sadiya ce masoyiya ta
Kaunarki ina fadarta
A zuci kuma baki ya furta

Na aminta da son tauraruwa ta
Mai tsari irin na mata

Kizo gani ki bani gata

Tuesday, 21 February 2017

MAGANGANUN HIKIMA KAN SO: Soyayyar Gaskiya


MAGANGANUN HIKIMA KAN SO: Soyayyar Gaskiya


Babu wani lokaci ko wani mazauni na soyayyar gaskiya. Tana faruwa ne batare da sani ba, a cikin bugawar zuciya, cikin faskawa guda, zai samu bagire na din din din”.

Written by:
Sharahbil Muhammad Sani 



Monday, 20 February 2017

Maganganun Hikima Kan So: Idan tana sonka yanzu, to Menene damuwa

 Idan tana sonka yanzu, to Menene damuwa

Ba ka zama na farkon ta ba, ba ka zama na karshen ta ba, ko nata kai kadai. Tayi soyayya kamin ta sake soyayya. Amma idan tana sonka yanzu, to menene damuwa? Ita ba cikakka bace kaima haka, sannan dukan ku ku biyu bazaku taba zama cikakku ba, amma idan tana faranta maka, tana sanya ka tunanin biyu, don haka yi kokarin zama mutum wanda ya san yakan iya yin kuskure, ka rika ta, sannan ka bata abin da kake iya bata. Zata iya kasancewa tana tunanin ka a kowane dakika ta kowace rana, zata baka wani bangare wanda tasan bazaka karya ba a zuciyar ta. Don haka kada ka tsane ta, kuma kada ka canja mata, kada ka yi tunani ko tsammanin zata iya baka abin yafi karfin ta/bata iyawa. Kayi murmushi idan ta faranta maka, ka bari ta sani idan ta bata maka, idan bata nan kayi kewarta. 

Written by: 
Sharahbil Muhammad Sani

MAGANGANUN HIKIMA KAN SO: Na kamu da So....


MAGANGANUN HIKIMA KAN SO: Na kamu da So.... 

 A lokacin da na karanta, na kamu da so kamar yanda nake kamuwa da bacci: sannu sannu, sannan gaba daya a lokaci guda.
                                                                                         

Writing by: 
Sharahbil Muhammad Sani