Showing posts with label Slider. Show all posts
Showing posts with label Slider. Show all posts

Thursday, 9 February 2017

…BANI SADIYA



…BANI SADIYA



Allahu Allah bani Sadiya
Allahu Jallah kayo Soyayya

Kaunarta ce azuciya
Tunaninta ne ke sa hajijiya

Babu Sukuni cikin zuciya
Inna tuna soyayyarki sai in shiga Hajijiya

Ina sonki sona gaskiya
Ki amince dani ya masoyiya

Nine amini na gaskiya
Babu mai sonki kamar ni da gaskiya

Rayuwa zan baki gaba daya
Zamu zauna baki da kishiya

Kaunarki zuci tayi mamaya
Wayyo ni kaunarki araina da zuciya

2017 KEBBI STATE SAHIHIYA RAYUWA SKILLS ACQUISATION TRAINING PROGRAMME






This is our great project event on 2017 Sahihiyar Rayuwa Skills Acquistion Training for 300 Youth in Birnin Kebbi, Local Government area.
* Computer Training

* Cosmetics
* Catering


https://web.facebook.com/events/1115224038604394/?notif_t=plan_user_joined&notif_id=1486650016214306

SOYAYYAH: KARSHEN ZANCE


SIRADIN KAUNA



SIRADIN KAUNA


Siradin kaunarki zan tsallaka
Masoyiya ta zo ki taimaka
Ke kadai ce zan kusanta

Ina tunani a zuciya ta
Kaunarki lallai ta samu gata
Ke kadaice kauna na furta

Zo ki yarda dani aminiya
Kauna muyu da ke zo sarauniya
Tunani na bani da tamka ni na furta

Sanadin kaunarki na zama jarumi kauye da birni
A sonki na yi suna duniya anka sanni
Na samu masoya masu fata da alkhairi ni na furta

Amma gani yau siradin na kasa tsallakawa
Sai na fada don gazawa
Shin laifi na ne ko kuwa al’adar so tambaya ta

Nayi bincike kanki kuma na gane
Cewa ke ce wacce ta dace kuma na gane
Koda najje nai magana iyaye miji sunka mata

Nayi kuka idaniya sun gajarta
Zuciya ta sai faman bugawa kamar ta busta
Na kasa hakuri amma can sai sunka furta


Sun bani kauwar ta don ita an rigani
Nace zanyi shawara zaku jini
Da naje gida na bacci yaki zowa gareni, aminiya so zoki furta

Idan ka duba hannu na sunanta shine
Kullun itace abin tunawa, tunaninta shine
Abinyi gareni don na yi nisa a so ne zo na baki gata

Ina neman shawarar yan dandalina
Me zance gun mahaifanta don na nuna
Karfin soyayya ta gareta ko zasu gane zan bata gata

Wannan shawara ce ni na nema naji ta babba
Gunku masoya ni bani zamba
Ina sonta amma basu banba, aminiya zo na baki zuciya ta

Siradin kaunarki zan tsallaka
Masoyiya ta zo ki taimaka
Ke kadai ce zan kusanta

Ina tunani a zuciya ta
Kaunarki lallai ta samu gata 
Ke kadaice kauna na furta

SIRRIN ZUCIYA



SIRRIN ZUCIYA






Yau zan bayyana sirrin zuciya
Kaunarki ta sani hajijiya
Yaki kiban so kinjiya
Ke zaki barni na tsallake tsiradin zuciya

Gani gaban ki ina juyayi
Kaunarki ta sa ni nake juyayi
Lallai yau zan bayyana sirrin nadai na boyoyi
Yau gani na zo da sirrin zuciya

Me sayasa a so na kasa yin tayi
Kullum idan na ganki sai nai ta juyayi
Kaunarki ta sa ni cikin juyayi
Yaki amince da ni masoyiya

Kullum idan na zo gidan ku sai na kasa tayi
Kallun idon ki dai nai tsayi
Kyakkyawar fuskarki ta sa ni tsayi
Ina son ki yan mata amince da soyayya

Kullum idaniya ta ke suke gani
Sun makanta a mata basu gani
Nayi nisa a soyayarki kizo ki gani
Amince da ni kar kice baki so na masoyiya

Kunnuwa na sun kurumta
Basajin kira bale a furta
Idanuwa ko sun azabata
Da soyayyarki wata basu gani sai ke aminiya

Kauna na bani kizo ki karba
Yafi a ce dake kizo sharba
Soyayyarki ce tasa ni nai ta kirba
Bani son ace dani zan rasaki a soyayya

Sirrin zuciya a yau na shaida
A zuciya ta babu tsida
Gun wasu matan tayi tsada
Ke kadaice zaki taya aminiya