SIRADIN KAUNA
Siradin kaunarki zan tsallaka
Masoyiya ta zo ki taimaka
Ke kadai ce zan kusanta
Ina tunani a zuciya ta
Kaunarki lallai ta samu gata
Ke kadaice kauna na furta
Zo ki yarda dani aminiya
Kauna muyu da ke zo sarauniya
Tunani na bani da tamka ni na furta
Sanadin kaunarki na zama jarumi kauye da birni
A sonki na yi suna duniya anka sanni
Na samu masoya masu fata da alkhairi ni na furta
Amma gani yau siradin na kasa tsallakawa
Sai na fada don gazawa
Shin laifi na ne ko kuwa al’adar so tambaya ta
Nayi bincike kanki kuma na gane
Cewa ke ce wacce ta dace kuma na gane
Koda najje nai magana iyaye miji sunka mata
Nayi kuka idaniya sun gajarta
Zuciya ta sai faman bugawa kamar ta busta
Na kasa hakuri amma can sai sunka furta
Sun bani kauwar ta don ita an rigani
Nace zanyi shawara zaku jini
Da naje gida na bacci yaki zowa gareni, aminiya so zoki furta
Idan ka duba hannu na sunanta shine
Kullun itace abin tunawa, tunaninta shine
Abinyi gareni don na yi nisa a so ne zo na baki gata
Ina neman shawarar yan dandalina
Me zance gun mahaifanta don na nuna
Karfin soyayya ta gareta ko zasu gane zan bata gata
Wannan shawara ce ni na nema naji ta babba
Gunku masoya ni bani zamba
Ina sonta amma basu banba, aminiya zo na baki zuciya ta
Siradin kaunarki zan tsallaka
Masoyiya ta zo ki taimaka
Ke kadai ce zan kusanta
Ina tunani a zuciya ta
Kaunarki lallai ta samu gata
Ke
kadaice kauna na furta
No comments:
Post a Comment