![]() |
World |
DUNIYA!
1.
Duniya kamar
misalin wasar kwaikwayo ce da ake shiryawa a ga abu kamar gaskiya alhali shiri
ne wanda ba gaskiya ba
2.
Duniya karewa
take yi kamar yadda idan an kunna Kandil yana ci da wuta komai tsawon lokaci za
a taradda wutar ta mutu
3.
Duniya
misalinta kamar wasan kasa ce da yara ke yi bayan karewar ruwan sama idan sun
gina Gida mai kyau sai kaji suna fadar wanda bai rusa ba dan gidan ladi mai
tandayen kasuwa hmmm!
4.
Duniya kamar
aji ne da ake daukar darasi acikin sa da duk wanda ya yi abin kwarai zai samu
sakamako mai kyau idan kuma ya yi ganganci ya ki amfani da damar da ya samu
lokacin daukar darasi to fa zai ga ba kyau a sakamakonsa.
5.
Duniya na kama
da kasuwa lokacin da zaka shiga tabbas lokacin wani zai barta ba dawowa
6.
Duniya rayuwar
gidan kaso
7.
Duniya rayuwace
mai cike da ban alajabi da mamaki wata rana zaka tabbatar da hakan, bayan ka
mutu zaka rayuwa kamar yadda ka rayu a cikin cikin mahaifiya
8.
Duniya gidan
bakin ciki da damuwa da bacin rai, ko wacce ana jindadin duniya to, lallai ya
duba imaninsa mai imani kullum a fargaba yake kuma cike da jarabobi
9.
Duniya misalin
ta misalin dan aike ne da ubangidansa ya aikeshi kuma ya samu wuri ya fake yana
jiran dawowarsa daga inda ya aike shi
10.
Duniya
makaranta ce
11.
Duniya budurwar
wawa
12.
Duniya ki dauka
ki aje duk yanda mutum ya ke jiji da kai yake wani fadi wallahi wata rana sai
anyi bashi kamar yadda akayi babushi kamin shi
13.
Duniya da
rayuwa abokai ne idan ka biyewa rayuwa ita kuma duniya zata biye maka amma kuma
ka sani cewa zasu kai ka su baro wata rana
14.
Duniya kamar
misalin bako ne da zai sauka a gidanka komai dadewa wata rana zai bar gidan
zuwa gidanshi na ainihi
15.
Duniya! Abin
ayi hattara da ita ce domin idan kayi sakaci wata rana zata saka kuka
16.
Duniya gidan
danjin dadi dan kadan kayi fankama ka bushi hanci wata rana a kasa za a saka
17.
Duniya gidan
sabani, duk wani sabani anayinsa ne a duniya amma a lahira babu wani sabani
kowa ya san gaskiya
18.
Duniya kamar
gona ce duk abin da ka shuka babu makawa shi ne abin girbarka
19.
Duniya! Zamanta
ba a nemi lahira ba tamkar jakine da kaya
20.
Duniya! Zamanta
ba a nemi lahira ba kamar kasuwanci ne da ba riba a cikinsa
21.
Duniya gidan
neman abincin lahira
22.
Duniya gidan
neman aljanna
23.
Duniya da kunci
ga wanda bai riki gaskiya ba
24.
Duniya ga wanda
ya shigo ta abin jajantawa ne
25.
Duniya gidan
hatsaniya da tashin-tashina
26.
Duniya gidan
hakuri da jajircewa
27.
Duniya da
rayuwa a cikinta ba tare da bin gaskiya ba misalin haduwa da makiyane ba tare
da shiri ba
28.
Duniya! Mai
sonki shi kika ci don shi zaki nunawa soyayya irin na karuwar da ke dauke da
cutar kanjamau da manufar jikawa wani
29.
Duniya! Wasu na
kuka a cikinta wasu ko dariya suke
30.
Duniya! Yanda
aka zo cikinta babu komai tabbas haka ake barinta babu komai
31.
Duniya! Gidan
bakunta
32.
Duniya kamar hadarin
mushaki ne (hadarin da baya ruwa) ana ganin hadari ya hadu kamar da gaske ruwa
za a yi sai kaga ya watse wayam!
No comments:
Post a Comment