Saturday, 31 March 2018

SANA’A RAYUWAR MATASA


SANA’A RAYUWAR MATASA


YOUTH@KEBBI STATE
SAHIHIYA YOUTH ENTREPRENEURS PROJECT


SHIRIN KUNGIYAR
SAHIHIYAR RAYUWA YOUTH COMMUNITY DEVELOPMENT ASSOCIATION




NA
SARATU MUH’D SANI

Copyright © 2017 Sahihiyar Rayuwa
Hakkim Mallaka (m) 2017 Sahihiyar Rayuwa

Published by
SAHIHIYAR RAYUWA YOUTH COMMUNITY DEVELOPMENT ASSOCIATION BIRNIN KEBBI, KEBBI STATE  
E-mail:sahihiyarrayuwa@gmail.com
Tel: 08113777717, 08103139272




Cover Design/Book Setting/Layout By:

SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAKERA
Website: www.hausacc.cf
Tel: 08113777717
 










FADAKARWA
Ba a yarda wani ko wata suyi amfani da wannan littafi ba ko ta wace siga sai tare da izinin Kunigyar Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association


GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah, kuma aminci ya tabbata a bisa zababben Jakada Shugaban Annabawa Muhammad dan Abdullahi, wanda aka saukar da Alkur’ani domin ya zama shiriya da kuma waraka ga Muminai. Yarda da aminci su kara tabbata a bisa iyalan gidansa da sahabbansa da kuma muminai har ya zuwa ranar karshe.
Ina kara godiya ga Allah da Ya bani damar rubuta wannan littafi a bisa dalilin Shirin da kungiyar Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association ta shirya ga matasan Jihar Kebbi, hakan ya sa aka nemi da in rubuta wannan littafi domin amfanin matasan da ake koyarwa a karkashin shirin domin koda sun koma gidajensu wannan littafi zai zame musu jagora.
Bayan wannan takaitaccen bayani ina so inyi godiya ga Sharahbil Muhammad Sani Makera Shugaban Kamfanin Sharhamak Computer Ventures kuma Shugaban Kungiyar Sahihiyar Rayuwa bisa ga kokarin da suke yi don ganin matasa hasalima mata sun samu kyakkyawar Rayuwa inda suke bin hanyoyi daban daban don ganin sun wayar da kan matasa game da muhimmancin ilmi, sana’a da kuma kokarin hanasu shaye-shaye. Ina kara godiya ga mataimakansa, musamman Abdulmalik Abubakar Ubandoma Secretary da Ahmad Rufa’i P.R.O da Aisha Abubakar Sayyadi, da Ridwan (Tope Boy) da Jamilu Yahaya Ambursa da kuma Abubakar Imamu suma ina godiya sosai ga irin kokarin da suke na ganin sun bada lokacinsu da karfinsu don ganin tafiyar nan ta alhairi ta cigaba.
Godiya ta ba zata kare ba har sai na mika godiya ta musamman ga Uban Kungiyar Sahihiyar Rayuwa Alhaji Babangida Mai Ahu bisa ga jajircewa da yake yi domin ganin wannan tafiya ta alhairi ta cigaba, ina rokon Allah Ya sanya musu alhairi, Ya kuma kyautata rayuwarsu damu baki daya.           



SADAUNARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga Kungiyar Sahihiyar Rayuwa tare da Jama’arta da Masoyanta da kuma Matasa Maza da Mata a duk inda suka, tare da fatar Allah Ya sanya ma wannan littafin albarka, ya zama mai amfani a doron kasa, Ya kuma sanya wannan kyakkyawan aiki a mizanin mu na lada, amin.

TA’ALIKI  
Bashakka ita sana’ar hannu ba karamar muhimmaniyar sana’a bace musamman ga al’umma, domin kuwa tana iya zamowa:
·       Sanadiyyar wadata
·       Samun yanci ga kai da kuma kasa baki daya
·       Walwala
·       Hana ta’addanci kamar irinsu sata da yaudara
·       Hana zaman banza
·       Tare da bunkasa tattalin arzikin kasa da sauransu.
Ganin irin wannan yasa kungiyar Sahihiyar Rayuwa ta zare damtse kuma ta dage wajen ganin ta bada nata gudummawa ga rayuwar matasa saboda irin muhimmanci da rawar da matasa ke takawa ga rayuwar al’umma. Hakika wannan taimako na wannan marubuciya ya yi dai dai da manufofin da kasar Nigeria ke bukata a yau, na a himmanci sana’o’in hannu musamman abin day a shafi fasaha irin wannan… Bashakka, wannan littafi zai taimaka kwarai irin ganin yadda Matasa ke neman hanyoyin Karin ilmi akan wadannan sana’o’i. don haka ya wajaba ga ko wace Cibiyar koyarwa da kuma wadanda ke koyon sana’o’i a gida su mallaki wannan Littafi domin samun Karin haske akan sana’o’i iri daban daban.

SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
President/Founder
Sahihiyar Rayuwa
29th April, 2017


 COSMETICS
1.   ROOM FRESHENER
KAYAN HADI:
·       Ruwa
·       Menthol
·       Methanol
·       Thickner
·       Texaphor
·       Colour
·       Perfume
YADDA ZA’A HADA: 
A sami roba ko bokitin roba mai kyau, ya danganci yawan turaren da za’a yi, sai a zuba ruwa cikin bokitin sannan a kawo menthol a zuba cikin ruwan daga nan sai a ajiye ruwan cikin rana yadda menthol din zai narke. Idan an tabbatar ya narke sai a kawo methanol a zuba sannan a motsa sosai. Daga nan sai a zuba thickner a motsa sannan a zuba Texaphor sai a zuba kala da turare a motsa sosai. Shikenan turare ya hadu sai a samu mazubi a zube. 
2.   CAR WASH
ZA A NEMI: 
·       Ruwa
·       Anti-soap (natrol)
·       Sls
·       Sulphonic Acid
·       Soda ash
·       Kala
·       Madarar turare

YADDA AKE HADAWA:
Za a jika anti – soap ya kwana saboda ya narke da kyau gudun gudaji. Bayan ya kwana ya narke sai a motsa a zuba sls tare da sulphonic acid a motsa sosai har sai sun narke sai a jika soda ash da ruwa kadan, a zuba a motsa. Daga nan sai a zuba kalar da ake so da turare.
3.   VASELINE
KAYAN HADIN DA AKE BUKATA:
·       Candle wax
·       Petroleum Jelly
·       Paraffin oil
·       Perfume (madarar turare)
·       Mazubi
YADDA ZA A HADA:
Za a fara narka candle wax idan ya narke sai a zuba jelly, idan shima ya narke sai a zuba paraffin oil a motsa, sannan a zuba madarar turare a motsa. Shikenan sai a saukar da tukunya. Idan ya fara shan iska kadan ya rage zafi sai a zuba a mazubi.
4.   LIQUID SOAP
KAYAN HADIN DA AKE DA BUKATA:
·       Ruwa
·       Anti-soap
·       Sulphonic acid
·       Costic soda
·       Soda ash
·       Sls
·       Madarar turare da kala

YADDA ZA A HADA:
A jika anti soap da ruwa isasshe sannan a barshi ya kwana, sai a motsa shi sosai, sannan a kawo sls a zuba, sannan kuma a zuba sulphonic acid a motsa. Soda ash da costic soda daban-daban za a jika su, sannan a zuba soda ash da farko sai a sanya Costic soda a motsa hadin sosai daga karshe sai a zuba kala da turare a motsa, daga nan sai a zuba a mazubi.
5.   ROBB
ZA A SAMI WAYAN NAN KAYAN HADIN KAMAR HAKA:
·       Petroleum Jelly
·       Menthol
·       Camphor
·       Colour
A narka Jelly sai a zuba menthol, shima ya narke sai a motsa sosai sai a sauke kan wuta a barshi yadan sha iska kadan sai a zuba camphor tare kala a motsa sai a sami mazubi a zuba.
6.   SHAMPOO
KAYAN HADIN DA AKE BUKATA:
·        Anti soap
·       Coustic soda
·       Soda ash
·       Sulphonic acid
·       Sls
·       Kala da madarar turare
YADDA ZA A HADA:
A jika anti soap kamar dai yadda nayi bayani a baya, idan ya narke sai a kawo soda ash da costic soda da aka jika a zuba cikin ruwan anti soap a motsa sosai, sai a zuba sulphonic acid shima a motsa a zuba sls a motsa sannan a zuba kala da turare, a barshi kamar awa uku (3hrs) sannan a zuba a mazubi.
BODY CREAM
Kayan hadi da ake bukata:
Ø Stearic Acid
Ø Cytel alcohol
Ø Borass
Ø Koroda wax
Ø Parafine oil
Ø Colour and Perfume
Yadda za a hada:
A zuba stearic acid, cytel alcohol, koroda wax, cikin tukungya mai tsafta a dora a wuta har su narke, sai a zuba parafine oil a jika Borass da ruwan zafi idan ya jika sai a zuba ciki a motsa sosai, za a ga ya yi kauri kamar koko, sai a zuba kala da tura a motsa, a sami mazubi a zuba.
FARAR POWDER
Za a tanadi:
Ø Calcium carbonate   



No comments:

Post a Comment