FARIN CIKI BAYA KIRGUWA GA MAI HAKURI
Farin ciki baya kirguwa
A kauna yau nayo kwaruwa
Ta so ni na so ta ta zam uwa
Ke ce na mallakawa dukan zuciya ta
Na yi kuka na zuciya
Kuma nayi na idaniya
Dare da rana zubar hawanya
Ke ce kika zam silar haka yan mata
Shekara biyar ina kaunarta
Zuciya ta tana mararinta
Idaniya ta babu bacci a kwayarta
Ina ta tunanin wai ya zaniyi da masoyiya ta
Sai gashi yau da kanta ta furta
Kauna ta take yi cikin lafazinta
Na aminta da kai sabina zo kaima ka furta
Dole na nasoki farin cikin rayuwa ta
Ina kwance ina ta tunani
A zuciya kullum dar-dar babu sukuni
A office idan naje ma'aikata hakuri suka bani
A yau naci ribar hakuri na ta aminta
Ina cikin gida sai nace fita zaniyi
Lokacin na dauko waya ta a falo silifas sun canja sauyi
Na saka hulla ta a ka amma babu layi
Na fita waje sai na kama da kaganni babu gata
Wani shago na harra sai najji an kirani
Ashe malamin ta ne shi ne ya neme ni
Na daga waya ta Sallama yayi gareni
Na karba masa yace nazo da albishir gare ka alhairi kayi fata
Munyi magana da Yar gidan kirki
Maganar kuma ta biya girki
Ta yadda ta aminta da kai mai halin kirki
Daga yau ka zamo nata
Daga nan zuciya ta ta buga don farin ciki
Na rasa abinda zaniya don farin ciki
Sai na ce da mai shago a yau ranar ce ta farin ciki
Daga yau shagonka zan dinga tunashi na mallaki yar gata
Ku bari zaku ji me ya faro da ni bayan mun hade
Ni da ita ya muka zauna da juna fatarmu kar mu kade
Soyayya a tarihi ban taba ganin irin wannan harhade
Nasha wahala amma yau gani na samu gata
No comments:
Post a Comment