Kaunarki nayo tun fari
Kaunar ki nayo tun fari
Kece ni nasa a tsari
Zo yaki ki sani a tsari
Masoyanki zo gimbiya
Farko sai na sa sunan Allah
Wanda shi muke yiwa sallah
Shine sarki mai kowa Allah
Na zo da koko wajen Ka bani gimbiya
Kaunarki a zuci da baki
Na furta kuma nai d'oki
Kaunarki abinyi ko kwance a d'aki
Karki ce dani bakiyi Sarauniya
Kullum idaniya sai hawaye
Kwaranya suke da hawaye
Har zuci tana yin hawaye
Na rasa inda zanisa zuciya
No comments:
Post a Comment