Amince dani ya
ke silar jin dadi na
Aminci a
gareki,
Ya ke sanyin
idaniya
Bayan gaisuwa
irin ta masoya, tare da fatar rayuwa mai inganci ina miki fatan wuni lafiya.
Rasarin zuciya
ta, abar kauna, hasken zuciya hakika kece zuciya take ta bege, zuciya take
tsantsar kauna. Na rubuto miki wannan sako ne badon komai ba sai don na sanar
da ke gaskiyar hakikanin abin da ke cikin zuciya ta. Na kamu da kaunar ki,
hakika ya gama zagaye ko ina a sassan jikina, bani da wani abu da zan iya
aiwatar wa. Amince da ni, ya ke silar
jin dadi na.
Ya ke mai
haskaka zuciya ta, hakika a sonki na matukar dimauta ki aminci da ni masoyi ta.
Na amince da ke sanyin idaniya
Sadiq Musa
No comments:
Post a Comment