Na shiga tsaka
mai wuya
Salam, barka da
wara haka ina fatan aminin zuciya a mafi ribatuwar rayuwa, bayan haka; ya kai
sanyi idanu na sani kai na a mafi munin safiya yau ne ranar da bazan taba
mantawa da ita ba, kuma yau na dauki biro na rubuta a kundin tarihin rayuwata.
Aminin zuciya
ina baka hakuri dangade da abin da ya faro nasan nayi kuskure kuma abinda nayi
ban kyautaba, hakika shedan ne sanadiyar afkuwar wannan al’amari.
Masoyina!, idan
baka hakura ba shin wa zan nemi afuwa gunsa? Kada ka manta kai kadai ne farin
cikin rayuwata kuma kai ne wanda nake fata ka zame man sanyi idanu na. ina
sahibin zuciya? Ahmad ina sanar da kai cewa na dauki alkawari ba wani abin da
zai sa in dai na kaunar ka, Kaunar ka ce kadai a zuciya ta, kuma kai ne Insha
Allahu wand azan zamo mata a gareshi.
Ina sonka Ahmad
Daga Sahibar ka
Zainab Isma’ila
No comments:
Post a Comment