Saturday, 31 March 2018

Wasikon Soyayya Series 1


Wasikon Soyayya
Masu cike da tabbacin cin nasara


Ina tunanin baki fahimci inda na dosa ba
Aminci a gareki,

Sarat! Kamar yanda na sanar da ke Ina tunanin baki fahimci inda na dosa ba, don haka sai na sake shawara da cewa abu mafi sauki shine in rubuta miki wannan takardar kamar yanda zai biyo baya.

Hakikanin gaskiya yaune ranar da zan bayyanar mikin da abin da yake zuciya ta, banyi zato ko tsammani ba zaki iya gujewa gareni, ko ki kyamace ni, sanin kowane Sarat yarinya ce kyakkyawa, wacce Allah ya baiwa farin jini, gakuma kyan fuska, gashi har gadun baya, a duk lokacin da Sarat take tafiya, nakan kure mata kallu, Sarat kin zance dukkanin yan mata, dayawa matan suke fata a ce sun taka sawun ki amma ina ba dama.
Kyan ki waye ba’indiya jiki mai kyau kuma inaga balaraba, tsayinki kuma dai dai kin tsayo matukar tsayowa Allah ya miki kyaun da bazan iya misaltawa ba.

Sarat idaniya sun hango farin cikinsu, sun hangu sanyi su, ranar da na aiko miki sako na na farko tunani na yayi rauni saboda tsoro da fargaba sai naga ba mafita idan har bana fito fili na sanar da ke sirrin zuciya ba.

Tsananin son ki ya tsanan ta a cikin zuciya ta har ma ya keta kirjina ya fito fili, duk wanda ya ganni na san ina cikin wani hali na daban, halayena, tunani na duk sun canja saboda ke.

Sarat ki amince da ni domin inyi alfahari da ke a wata rana da zamu tare a matsayin ma’aurata.

Ina sonki Sarat
Daga Muhammad Ishaq

No comments:

Post a Comment