Sunday, 20 January 2019

KUNDIN QADDARATA

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
        📖📖📖📖📖


         *~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



                  6⃣3⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*MANZAN ALLAH S A W YANA CEWA,KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGIN DABINO NE*
_____________________________________






      "Ka yimin afuwa,a yanzu haka tafiya zanyi ta shekara daya,ka barni har na dawo don Allah,na sani cewa ka cika mutum,kuma ka nunan dukkan wata qauna da halacci,amma ina son ka barni har zuwa sanda zan dawo daga wannan tafiyar,wala'alla zuwa sannan zuciyata ta sake sanyaya daga rashin da nayi,ka sani abdur rahman yadda mutuwa ke da ciwo da wuyar barin zuciya,kayi haquri da ni don Allah" ta qarashe maganar muryarta na rawa idanuwanta na tara hawaye,tausayinta ya kamashi,ya sani cewa raba zuciyar sumayya da mukhtar ba qaramin abu bane,a kanshi ta fara sanin so da qauna,a kansa ta fara sabawa da wani namiji baare,ta soma iya magana da d'a namiji,tilas yaci gaba da haquri kafin ya cimma burinsa,zaici gaba da addu'ar samun zabi mafi alkhairi,kafin lokacin dawowarta ya tabbatar shima duk wasu burikansa sun gama cika,ya kammale hankalinsa guri guda,dubanta yayi cikin sigar lallashi
"Na sani cewa shekara daya ba kwana daya bace,amma gurin Allah ba komai bace,Allah ya nuna mana,amma kema sai kinyi yaqi da zuciyarki,sannan kada ki bawa wani dama bayan ni,kinyi alqawari?" Murmushi tayi saboda maganar ta bata dariya,to shi dinma tanqwara zuciyarta take qoqarin yi ina ga ace ta bawa wani dama,ko ya mance zuciyarta ba lafiyayya bace?
"Baka da wannan damuwar" ta fadi tana kada kai,maganar tayi masa dadi sai yayi murmushi ya soma janta da hira,bai tafi ba sai da ya rage mata damuwa sannan sukayi sallama.

       A daren kasa bacci tayi baki daya,juyi ta dinga yi daga farkon gado zuwa qarshensa,tunani fal zuciyarta,zuciyarta sam babu dadi,rayuwa kenan,yau zaqi gobe madaci,abinda ya dinga yi mata kai kawo kenan har bacci barawo ya dauketa.

       Kwanakinsu a kano sunyi mata dadi qwarai,ana ta gabatar da hawayan sallah irin na al'ada don ma saura suka tarar,garin cike yake da baqi cikin kowanne sassa na duniya masu zuwa kano daga qasashe daban daban,kama daga qasashen turawa har na larabawa don ganin hawan sallahr garin kano,wanda babu irinshi kaf arewa saidai a kwaikwayeshi,ta yadda tabbas kano nan ake morewa bikin sallah ba kamar sauran garuruwa ba da basusan ana yiba ma,tayi hira da mama malam da qannenta iya son ranta,abin dadin uncle farouq ya qara musu kwanakim yace su cikashe kwana goma,randa suka cika sati suka soma zaga 'yan uwa da qawayen anty dije suna musu sallama,kusan ko ina da sumayyan aka je don itama ta yiwa dangi sallama,kwana biyu suka kammala ya rage musu kwana biyu su koma abuja don fara shirin tafiya uk london.

     Washegarin ranar da zasu tafim bayan ta gama hada kayanta baki daya ta shirya tsaf ta shirya abdallah,ta riga data yiwa driver magana zata unguwa,gidan yaya yahaa take son zuwa don yi mata sallama,anty dije tace zaya zo ya kaita,qarfe sha biyu na rana ya iso,ta yiwa mama sallama ta dauki abdallah suka tafi.

       Daga falo suke amsa sallamar tata,yaya yahanasun ce kawai ta dauki murya,jamila fatima da fiddausi nr zaune duka a falon,gefe kwanon koko ke da kofuna da alama shi suka gama sha,baki daya fiddausin ta fige ta fita kamanninta tayi baqi kamar ba ita ba,yaranta uku a yanzu (banda yaran data haifa wanda sumayya taje sunansa)har yau tana gida babu wani ci gaba,uwar miji tace ba zasu iya ba ta cika haihuwa,danta ba qarfi gareshi ba,sai su fatima da rashin aure kan lokaci yasa suka soma tsotsewa,jamilan ta qwallafa rai kan wanda takeso shi kuma yayarsa ta hana tace auren gida zaiyi,fatima ma kuwa babu maganar kowa,baki dayansu anty dijen ke riqe da su,abun akwai tausayi,mataimakin madogarar dama qwaya daya ne MUKHTAR,a yanzu da babu shi kuwa babu wani mai dubansu,dukkaninsu washe bakin ganinta suke itama tana amsa musu fuska sake har tayi matsugunni kan daya daga cikin kujerun,tuni abdallah yayi wajen yaya yahanasu,ta rungumeshi tana shafa kansa tare da duban fuskarsa,qwalla ta cika mata idanuwanta har ta soma gangarowa,duk sanda taga yaron mukhtar yake tuna mata,kamanninsu daya,tana jin kanta a mai laifi,a wadda tayi silar maida shi maraya,kullum kwanan duniya sai ta yiwa zainab Allah ya isa.

      Baki dayansu jikinsu yayi sanyi ganin yadda yayan ke share hawaye,tuni itama sumayya ta fara goge tata qwallar,tsawon mintuna kafin su bawa zukatansu haquri sannan suka shiga gaisawa,baki dayansu kunyar sumayyan sukeji,ga wani girma da suke bata na daban,ranar anan ta wuni,har la'asar,sai ina kasa ina ka ajjiye suke da ita,sai da tayi sallar la'asar sannan tayi sallama da su bayan ta ajjiye ma yaya yahanasun sabulai klien da su maggi cikin leda mai layi layi,sannan ta baiwa fatima da jamila dari biyar biyar,fiddausi dubu daya duk cikin irin kudadenta.

       Hakanan ta tsinci kanta bayan fitowarta da yiwa mai a daidaita sahun data tsaida kwatancan gidanta,ma'ana gidan qarshe da suka zauna da mukhtar,wanda tun wajen raba gado ya shigo cikin kasan su,daidai madaidaicin get din gidan ya ajjiyeta,ta sallameshi ta dauki abdallab,jakarta ta laluba cikin sa'a muqullan na ciki ta sanya ta bude fa shiga.

      A hankali ta dinga takawa tana duban gidan,duk taku guda na dawo mata ne da duk wata rayuwa tata da ta shude can baya,sannu a hankali zuciya da gangar jikinta suka raunana,ta dinga takawa a sannu har ta kai ainihin falonsu,duk kayanta na jere ma ciki babu abinda ta fitar,saidai gidan yayi qura sosai saboda rashin kasancewar kowa a ciki,shimfide abdallah tayi saman kujera wanda ya soma bacci tun cikin adaidaita,idanuwanta suka wurga zuwa qofar da zata sadaka da bangaren mukhtar,sai ta miqe tana duban qofar harta sada kanta da ainihin dakin gadonshi,babu komai ciki kamar yadda mamallakin gun bai duniya,sai ta gaza riqe hawayenta suka fara sintiri kan kumatunta,gefe guda ta duqe tana bin bango saboda rawar da jikinta keyi ta rushe da kuka mai tsuma rai da zuciya,ta jima tana kokawa sannu a hankali har nauyin dake cikin zuciyarta ya soma raguwa,ta share qwallar tata ba don ta qare ba ta juyo da niyyar miqewa,abdallah ta gani tsaye bayanta yana kallonta
"Wa ya saki kuka ammi?"hannu ta miqa masa alamar ya taho,ya taho din kuwa ya fada jikinta ta rungumeshi tana ci gaba da goge hawaye.

       Sai data samu nutsuwa cikin ranta sannan ta qarasa zagaye gudan,duk inda ta taka da abinda zau tuna mata,a haka ta kai har biyar da rabi sannan ta lalubo abdallah dake can wani gu yana wasansa ta sauya masa kaya ta rufe gidan suka fito idanu jajur na kukan da ta sha.

       Washegari suka kama hanyar abuja,hankalinta yasi dagawa na barin abdallah da zata sakeyi,bata so yayi maraici irin na mahaifinshi,babu uwa babu uba,saidai ganin yadda sam bai damu ba shi ya kwantar da hankalinta,da fari ya soma maqale maqale amma daga bisani sai ya ware har da shi a masu daga mata hannu,ajiyar zuciya ta saki bayan sun hau hanya sosai ta maida idanuwanta ta rufe,sam bata son komawa abujan nan,tafi qaunar garinta kano,koba komai kowa nata yana can,da zata iya data roqi su anty dijen su barta a can din,saidai yin hakan tamkar butulci ne ga qaunar da anty dijen ke nuna mata fiye da dukkan wata 'ya dage cikin danginsu,duk da 'yan maganganu da ke fara tsowa na hassadar riqon nata da antyn keyi.

       Kasancewar basu taso da wuri ba shi yasa basu suka isa gida ba sai takwas na dare,a gajiye kowa yake,saboda haka kowa gun kwanciya ya nema idanuwa cike da bacci,dama tuni sunci abincin darensu kan hanya.

       Washe gari da gyaran gidan suka tashi,suka kintsa ko ina,kafin wani lokaci gidan ya dawo hayyacinsa,basuyi dai break da wuri ba saboda aiki.

        Zuwa la'asar har abincin dare sun gama,su khalipha na dakinsu suna gayaran kayayyakinsu tare da fara ware wanda zasuyu tafiya da shi,sumayya na zaune falon tana hutawa,hannunta riqe da waya tana neman lambar mama don su gaisa ta kuma ji ya abdallah yake,sallamar amira ita ta katse mata abinda take shirin yi din,ta shigo sanye da yadin sartin baqi sidik wanda aka yiwa doguwar riga,sai dan madaidaicin jan mayafin data yane kanta da shi,cikin fara'a sumayyan ke dubanta har ta qaraso ta samu wajen zama
"Mutanen kano ta dabo,sauka ba sanarwa?"
"Kada ki qorafi,saukar dare ce,har yanzun kuma bamu gama watstsakewa ba,sai dazun muka gama saita gidan"
"Gaskiya kam,ko mu muna nan muna hutu,baqi sun tafi sun barmu da kewa,gidan ba kowa duka ba dadi,kowa ya koma inda ya fito,dadin abun daya nima next week zamu koma school" murmushi kawai tayi,suna hutawa tamkar sunyi hidima da baqin,bayan komai akwai masu aiki dake gudanarwa
"Gaskiya kam ansha baqi,saidai Allah ya bada lada"
"Amin" amira ta fada tana lalubo wata number cikin wayarta qirar iphone 7
"Ki duba dakina can wajen bedside drower akwai black bag ki kawomin gidan umman khalipha" abinda tace kenan cikin salo na bada umarni ta kashe wayar,sumayya ta ajjiye lemo da ruwa gaban amiran tana tambayar maman husna,murmushi tayi tana daukar gorar ruwa
"Husna mutuniyarki,sun koma inda suka fito" idanuwa sumayyan ta dan fiddo
"Suma ba nan suke ba?"
"Eh,mijin anty farida custume ne,basu zama gu daya,yau suna can gobe suna nan,amma lokaci lokaci suna zuwa hutu da kuma lokacin bikin sallah kamar haka" kai ta jinjina 
"Allah ya taimaka"
"Amin"hira suke tabawa kadan kadan har ta shigo bakinta dauke da sallama.

     Sumayyan ta ganeta tare hadimar amiran ce,tare suke shigowa,isa da qasaitar gidan baabaa prof kusan kowa dame masa aikinshi shi daya,gaida sumayya tayi saidai ta kasa amsawa ta maida mata gaisuwar suka gaida juna,kusan zata dan girme musu saidai ita din yare ce,sannan ta rusuna cikin girmamawa ta miqawa amira jakar mai kyau,amsa tayi sannan tace
"zaki iya tafiya,idan ummee ta tambaya kice ina gidan umman khalipha"
"To madam" ta amsa ta fice,miqawa sumayya jakar tayi tana fadin
"Ga tsarabarki ta saudiyya,babu yawa a karba da haquri" murmishi ta saki tasa hannu ta karba tana godiya tare da fadin
"Mai yawan kenan" tana fidda kayan ciki,turaruka ne designers masu kyau guda uku,agogo cikin dan akwakunsa,sai hijabai saqar qasar oman suma guda uku masu azabar kyau,sun burge sumayya qwarai har sai data fidda murmushi saman lebanta
"Naga kina sonshi ne sosai"
"Naji kuwa dadin kyautarsa fiye da komai cikin kayan nan" 
"Ina fata kin yaba"
"Qwarai da gaske" suka sa dariya baki daya,a nan anty dije ta fito,gaisawa sukayi sumayya ta nuna mata kayan ta gani ta tayata godiya.


      Wayar amiran ce ta dauki qara,dagawa tayi tana dubawa,idanu ta zaro,a fili ba tare da tasan ta fadi ba
"Na shiga uku ya man yau kuma?" Da hanzari ta daga kiran ta kara kunnenta
"Ok,to yaya" ta fada tana miqewa
"Amiran umman khalipha na wuce,ya man ya aikeni na kaiwa umme waya kada ya qara kira ban je ba,ya kira wayarta taqi shiga haka land line din part dinta"
"Ok,muje na taka miki" sumayya ta fada tana miqewa
"Na gode" ta fada tana murmushi,don haka nan Allah yasa mata qaunar sumayya,burgeta take sosai.


          Jerawa sukayi suka fito,suna gab da kaiwa qofa amira tace
"Uhmmm,ko ki tambayi ma mutuminki ko?"
"Ayyah,ya mahmoud,ki gaidashi don Allah nayi laifi kam"
"Um um,ni ba ma shi nake nufi ba,ya mustapha mana" shiru ta danyi gabanta na duka tunda ta ambaci sunam nashi,da ido amiran ke karantarta ganin bata ce komai ba har tana shirin fita ya sanya ta bar zancan ta soko wani
"Yaushe zaki shigo gaida baabaa,yana ta maganan baiga mamanshi ba" dan qaramin murmushi ta saki,sai taji tayi kewar tsohon duk da ba sabawa sukayi ba,amma saidai ko kadan bata sha'awa ko marmarin sake shiga gidan,tun daga randa abun ya faru.
"Ki gaida min baabaa da kyau don Allah,zan shigo idan Allah ya yarda" ta fada da siga biyu don bata da niyyar zuwa din
"Allah yasa da gaske ne,saikin shigo din na gode"
"Nike da godiya,ki gaidamin su ummee ma" 
"Zasuji" ta fada tana ficewa tare da jin dadin yadda sumayyan ta nuna kulawa ga ahalinta.







 




*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

3 comments: