Daga Namaikyau ...
ZUWA GA GWAMNATIN JAHA DA SAURAN WA YAN DA ABIN YA SHAFA .
*SIRRIN ABINDA YA FARU*...
Rigimar Garin Barama dake karkashin karamar hukumar mulki ta Gwandu, Da Chairman din Gwandu Local Govt, Alh Shehu Bagudu Dalijan,
Hakki Na Farko Da Yafara Tauyewa Mutanen garin Barama Shine Lokacin Damina Anyi Iska Kwaninka Rufi Duk Sunkware, Anyi Anbaliyar Ruwa Tsakiya Garin Barama da gidajen Su Duk Suncika Da Ruwa Anyi Kusan Kwana Arba,in Ruwa Basu Janye A Tsakiyar Garin Barama ba,
Gidaje Suka Rurushe Nikaina Mai Wannan Rubutun Nayi Gina Ciki Da Falo Ko Shigarsu Banyi Ba Suka Rushe
Dakunan Da Suka Rushe Sunfi Dari A Lokacin Har Yanzu nan Wasu Basu Sami Daman Gyarawa Ba Saboda Rashin Abin Gyara,
Amma Chairman Baije ba kuma bai aika ba,
Gwamna Ya Turawa Gwandu local Govt Tallafi Akan A rabawa Wa Yan da Wannan Iftila,in nan da na lisafa Ya Shafa Amma Abin Mamaki Ko Magajin Barama Baisan Anyi Ba Ma,ana dai Babu Mutun Ko Daya Daga Cikin Barama Da Ya Samu Wannan Tallafin, Kuma Ina Sane Amma Ban fadawa Duniya ba,
Akazo A Kan Maganar Hanyar Da Tatashi Daga Gwandu Tabi Ta Barama Yawuce Argungu, Mu Mutanen Barama Bamumasan Da An Awon Hanyar ba muntashi Da Safe Kawai Mukaga Awo Yabiyo Ta Garin Barama Amma Sai Wani Kauye Da Ke Kusa Ga remu da Yake Suke da manyan yan Siyasar da akasani Suka Turo Yaran su Cikin Dare Suka Ciccire Itacen Awon Hanyar Suka Mayarda Shi Can Kauyensu, Abin Yazan Rigima Bamu Dauki Mataki ba mukaje Gurin Chairman muka Sanar da shi Halin Da ake ciki Yazo Dakansa yaga yadda Abin Yake Yace Wayan can yan kauyen basuda gaskiya Dan haka aiki nan barama zaayishi Saboda nan Awo Yabi Yayi Mana Rantsuwa Takai 3 Akan Bazaadauke Aikin nan daga Barama ba, Bayan Sati Biyu Zuwa 3 Sai Gashi Yadawo Tare Da Wa yan can yan Siyasar Kauyen Da aka Sani,
Zasu Dauki Motocin Aikin Hanyar Su Mayar da su Wacan Kauyen Batare Da Wani Bayanin Fahimta ba, Mukace Bamu Yarda Ba Abin Yazan Rigima Har Yayi Kirarin Sai Dai Duk Wanda A cikin Barama Yakare Amma Sai Ya Dauki Motocin Ya Mayarda Su Wajen Masu Galihu,
Mu kuma Mukace Sai Dai Yakashe Mu din Kamar Yadda Yayi Ikirarin Amma bazamu Yarda A Dauki Motoci Ba Daga Inda Gwamnati Ta Ajesu A Mayarda su Inda batasan da can ba, Daga Karshe Dai Komawa Yayi Yataho Da Motacin Yan Sanda Sunkai 16 Sukayi Tayi Mana Halbe Halbe Cikin Barama Babu Wanda Ya Kulasu, Saboda Tin Kafin Suzo Nayi Wani Bincike Akan Hanyar Nagano Sukadai ne Ke Haukar su Nacema Mutane Idan Yadawo Daukar Motar Sukyaleshi Kawai Saboda Bashi ne Dankwangilar Hanyar ba kuma ba Dan kwangilar yaturo shi ba Wannan Dalilin ne Ya hana akashe Mutanen Barama Ranar Da Yanzu Munzama Tarihi, Amma Wanna ma ban gayawa Duniya ba,
Yanzu Kuma Yadawo Maganar Dajin Da Ya Tabbatar da dashi Mutanen Barama Suka Dogara Saboda Ya Kwantata Mana Ya Damkawa Hillanin Da Basufi Su 20 Ba Dajin,
Bayan Kuma Duk Inda Yakamata Muje Saboda Ayi Mana Sulhu Tsakanin Mu Da Hillanin Nan Wlhy Munje Amma Anki Azo A Sulhuntamu Muzauna Lafiya Ko Dan Zaben Da Ke Tafe, da kuma magance rigima tsakanin Fulani da manoma.
Mutanen Kauyukkan Da Suka Shafi Argungu Local Govt Da Gwandu local Govt Anyi Meeting Akan Cewa A Raba Hulda Da Hillanin Nan Kar Asaya Garesu Kar A Sayarmasu Kar A Shiga Mota Daya Da su Idan Kuma Sun Mutu Kar Aje Janaiza Bale Gaisuwa,
Jin Wannan Hukunci Yasa Nayi Videon din tare da Hotuna Yada Domin Mahukunta Sushigo Cikin Lamarin Su Sulhuntasu A Zauna Lafiya, domin taimakawa gwamnatin jihar kebbi Wurin kokarin da takeyi Wurin kawo zaman Lahiya a cikin fadin jihar.
Amma Lokacin Da Wa yan da Abin Ya Shafa Sukagani Sukasa Aje Ayi Masu Bincike,
Shikenan Sai Chairman Ya Nuna Baisan Da Wannan ba Sai Ya Bincika Bayan Ya Bincika Yaga Labarin Da Video Sai Yasa Akira Daya Daga Cikin Mutanen garin Barama Ayi Sulhu Bayan Yaje Sai Yasa D p o Na Yansanda Ya kulleshi Yau Kwana 3 Kenan Anyi Ta zuwa Dpo Yaki Bayarda shi Yace Chairman Yace A rike mai shi Sai Ya Nemeshi, Yanzu Kuma Ya ba Dpo Umarnin Ya Kamoni Duk Inda Nake Tinda Ni Na Watsa Labarin Azo Ayi Sulhun Rigimar Da zata Iya Kawo Fadan Kabilanci, Shine Laifina, Yanzu Haka Bayan Wanda Suka Tsare Tin Shekaranjiya Yau Ma Dpo Yakirani Yace min Zasu Rike Magajin garin Barama Har Sai Nakawo Kai na,
Dan Haka Ina Sanarda Duniya Da Yan Uwana Yan Social Media Da Manyan Yan Siyasar mu Idan Kuka Daina Ganin Postin dina To Sunkamani Saboda Su Walakanta ni, ciki da gaskiya wuka bata hadashi,
Yanzu haka wasu cibiyoyin watsa Labarai da yawa sun kira ni kuma na fasa kwai saura D. P. O. Da kuma wanda yasa shi tsare mutane fiye da Kwana 3 Suma su fadawa Duniya nasu dalilin yin amfani da mukamin su na Duniya Domin takurawa talakawa.
By Namaikyau ...
No comments:
Post a Comment