Saturday, 4 February 2017

TAUSAYI A SO...

TAUSAYI A SO...


Shi tausayi wani halitta ne da Allah Ya kaga a zukata, kauna kuma wani sashe ce daga zuciya. 
Sadiya Wallahi ina kaunarki, ki tausaya ki aminta da soyayyata. Sadiya idan baki aminta dani ba zan tsinci kaina cikin mawuyacin hali.
Ina so ki sani cewa nafi kowa sonki, nafi kowa kaunarki, na soki lokaci mai tsawo alhali nasan ke baki sani ba. Ki yarda dani Sadiya zan kula da soyayyarki, Sadiya ni nasani rashinki a guna tamkar rasa rayuwatace. Ya Allah na kai karar kukana, Ka taimakeni. Sadiya ki taimaka ceci zuciyata yanzu haka ba lafiya zuciya sai faman buguwa take, ki tausaya ki yarda dani. 

No comments:

Post a Comment