Sunday, 5 February 2017

So Yanayi: Umar M. Sharif



So Yanayi: Umar M. Sharif  



So Yanayi mai sauyawa
So Yanayi

So Yanayi na shigo sai naji sanyi nai sa’a a so bazanyi sake ba
So Yanayi kowa da zabinsa a zuci kai na rike a so bazan ma kishiya ba

So yanayi na shigo sai naji zafi kiyi agaji ki taimaka don naji sanyi
So yanayi kowa da zabinsa a zuci kai hakuri kaga wanda nake so

Nai damara a sonki sam baja da baya
Don na dace da wagga diya mai al’kunya
Kyan hali da dai kuma bata yimin karya
Soyayya ki shari hawaye na

Kwanciyar rai shin koko masoyi na
Kai ka zamo sanyi na idanu na
Kallonka ke kauda bakin ciki na
Kai na rike zanyiwa kalamai na

Sonki ya kama zuciya ya hanani sakewa 
Yawan tunani ya sakani nake yanewa
Ruwan hawaye a idona ki tausayawa
Ki bani kauna mai sanya farin ciki na

Ka Makara ba damar in waiwaye ka
Tamkar mutuwa ka zame mini babu shakka
Domin itace mai raba kauna ta zama kuka
Ina da masoyi wanda yazzam farin cikina

Maganar so ta wuce kimin yau nisa
Yau ni da masoya sunzo mun gaggaisa
Sunyi jinjina sunce kaunarmu babu irinsa
Sun bamu kambu sunce mu kara rirrike juna

Karki kulle idonki kince bazakiyi so dani ba
Maza bar guna sam haramta bazan iyaba
Tai nemi tamka ga yan mata baka rasaba
Bazan iyaba domin kin girma a raina

No comments:

Post a Comment