Sunday, 5 February 2017

INA SON KI



INA SON KI


Ina sonki gimbiyar mata
Amince dani sahiba ta
Ki yar da dani ke ce jagoran zuciya ta
Ina sonki jarumar mata

Kaunar ki ce silar jarumta ta
Kin ratsa zuciya jini da anta
Bazani barki ba sahiba ta
Kina raina kinji yan mata

Zanyi kuka idan har ba gata
Zuciya ta yi kunci ina ta fata
Kasan cewa da ke a matsayin miji da mata
Kasance da ni kiyar da ni aminyar zuciya ta

Tunani na kisan uwar ya ya a rayuwata
Ki kasance dani zaman da ba’a manta
Zama na har a bada suruka ga umma ta
Kasance dani zo kiyar da dani yan mata

No comments:

Post a Comment