MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 01
Sanin mutuncin
bawa wannan sai Allah don shi ya san iya gatan da ya tanadar mishi a ranar
tsayuwa. Mu girmama mutane ko muma za a girmama mu.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 02
Hakuri guzuri
ne, Allah Ya na tare da masu hakuri.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 03
Kyautatawa
mutanenka shi kuma Allah Ya kyautata maka. Idanuwanka su daina rufewa kan abin
duniya da ka samu, wata rana kana ji zaka bar abin da ka tara ko kuma abin da
ka tara ya barka. Don haka mu lazimci taimako don kaucewa yin da nasani
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 04
Duniya Labari,
Duniya
Makaranta,
Duniya Kasuwa,
Duniya wasan
gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 05
Duniya bata
gurbacewa a sanadiyyar masu aikata barna da ke cikinta, sai dai tana gurbacewa
ne a sanadiyyar wadanda ke ganin ana aikata ba daidai ba su sa ido suna kallo
basu ce komai ba.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 06
Ko kana cikin
masu matattar zuciya wanda baya ganin d’an wani nashi? Yi maza ka gyara halinka
d’an makocinka ya zama d’anka, haka ake yi sai rayuwa ta dawo sabuwa.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 07
Taimako
ma’adanace da bata gunda, gara ko tsatsa. A duk lokacin da ka yawaita taimako
shi kuma Allah zai yawaita maka a cikin duniyarka.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 08
Mutuwar zuciya
abune mai muni, yawan barace-barace fitinace ga musulmi.
Muyi kokarin
rufawa kanmu asiri ko ma samu martaba a cikin idon makiya.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 09
Sana’a sa’a inji
bahaushe.
Mu rike sana’a
don itace ke da kaso 99% na arzikin da aka saukar a cikin duniya.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 10
Wasu sunce dare
mahutar bawa.
Ni na ce dare
mahangar bawa
Mu bi dare, mu
raya dare domin cimma nasara akan al’amarinmu.
Dare shine
lokacin cin nasara ga kowane irin abu da ake nema.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 11
Bi rayuwar nan a hankali don kuwa baka immata. Haka Rayuwa
take da nauyi fiye da duniya.
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk
www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 12
Duhu baya gusar da Duhu: haske kawai ke yin wannan. Tsana
bata gusar da tsana (kiyayya): So kawai ke yin wannan.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 13
Kyautatawa wanda
ya kyautata maka, haka ake yi. Butulci guba ne wata rana za’a yi da-na-sani na
har abada.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 14
A duk lokacin da
ka taimaki wani to, Allah zai taimake ka. Sirrin kenan taimakawa jama’a sai ka
daukaka akansu..
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 15
Shin ko kana
kishin Kasarka? Wannan shine mafi girman al’amari da burin da ake nema ga reka.
Ka so kasarka ko ka samu martaba a wajen Ubangijinka, Son kasa wajibi ne ga
kowa..
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 16
Kada kayi mummunar
adu’a ga Shuwagabanni, domin lalacewarsu kai zata shafa. Kyakkyawar addua ita
ce maganin dukkanin bakin ciki.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 17
Shin kai mai
amana ne? ko mai gaskiya ne kai? amana da gaskiya suna tafiya ne a tare, ka
rike amana kuma ka fadi gaskiya zaka buwaya.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 18
Gaskiya na da
daci, haka ne. amma kuma gaskiya itace hanyar tsira da cin nasara.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 19
Ka fadi gaskiya
koda kuwa za’a kashe ka, bayan ka bar duniya, gaskiyar za tayi halinta. Rashin
ka zai rama barazana a cikin zukatan su.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 20
Ko kana so ka
buwayi makiyanka, rufe sirrinka kuma kayi dariya lokacin kuka za suyi tsammanin
ba suyi nasara ba.
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 21
Addua itace
makamin mai imani, ka rike addua don cin galaba ga makiya
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 22
Ka kyautata
manufarka kuma ka tsarkake zuciyarka ba zaka kunyata ba
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 23
Kada
ka damu da cewa karya ta mike kafa. Tabbas karya zata gushe. Kada ka damu da
tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana? Lallai za ta bayyana komai dadewa.
Abin da ya kamata ya da meka shi ne, menene matsayinka; a kan gaskiya ka ke ko
a’a?
Sharahbil
Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA
TA 24
A lokacin da na karanta, na dade ina
tunani me yasa Karya take da kyalle da
sha’awa gamai yin ta? Kuma gaskiya take da tsananin daci tare da sanya
bakin jini ga mai kiyayeta: Gaskiya itace misalin bullowar rana: sannu sannu,
sannan gaba daya a lokaci guda.
Sharahbil Muhammad Sani:
www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA
TA 25
Ba Dabi’ar So ba ne, sai dai Dabi’ar
abota ne yin auren da babu farin ciki a cikisa.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 26
Ka zama mai
Rahama ga Mutane: Mai yiyuwa ne kaima ka samu Rahamar Allah.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 27
Ka yi magana mai
kyau ga kowa don itama Sadaka ce
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 28
Kayiwa bakinka
linzami wata rana sai ya jefaka a rami
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 29
Zina itace mafi
munin laifi a cikin al’uma, ka guji aikata ta, don kaucwa mummunan sakamako.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 30
Nagarta itace
hali mai kyau, ka zama mai nagarta sai ka rabauta.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 31
Kayi jinkai da
wadanda basada, ka tausaya musu, wata rana za kayi galaba…
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 32
Kada kiyayyar da
ke tsakaninka da makiya ta hanaka fadar gaskiya akansu. Wannan shi zai kusantar
da kai ga jin tsoron Allah.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 33
Yi kokarin zama mutum wanda ya san ya kan iya yin kuskure:
kuma idan ya nemi gafara. Ganin kankantar laifi bala’ine mai girma.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 34
Duk wanda ya raina mace to bai san
asalinsa ba, wanda ya wutakanta mace, bai godewa Allah ba, don mace ni’imace da
Allah ya yi zuwa ga namiji
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 35
Kauna da dadi amma kima ta na idon mai kunya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 36
Kayi komai cikin so, shi ne matakin
cin nasara
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 37
Ni ba wani abu mai muhimmanci bane, ga wannan ni mai tabbaci ne. Ni mutum
ne da ba kowa ba kuma ina yin rayuwa ta a matsayin haka. Ina sanar da ku wannan
ku sani sunana ba da dadewa ba za a manta dashi, amma ka rayu kana son wani da
dukkanin zuciyar ka da rayuwar ka, wannan shine wadataccen abu har kullum.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 38
Sau daya a rayuwa, Na yarda na
amince, ka samu wanda ka ke tsammanin zai taimaka maka a rayuwa. Ka sanar da
shi wani abu wanda baka taba sanar da wani shi ba a rayuwar ka amma sai ya
tarwatsa ya fallasa dukkanin sirrin ka. Sannan kuma ya nemi da ka kara sanar dani wani. Sai na
sanar dashi manufar rayuwa, manufar da ba zata taba zama gaskiya ba, manufar da
ba zan taba cimma ba, da kuma wadansu abubuwan da banshirya a cikin rayuwa ta
ba. Lokacin da wasu abubuwa masu kyau
suka faru, zaka tsaya don sanar da su game da abubuwan, alhali ka sani zasu
tarwatsa maka al’amari. Basu damu da
suyi kuka tare da kai ba idan ka shiga tsananin damuwa ba, ko farin ciki
lokacin da ka shiga nishadi. Ba zasu taba aikata wannan ba, don sun tsani
al’amur ranka, ko suna so ka kasance a kullum a wulakance ba ka da amfani,
sannan kuma suce sune zasu doraka a bisa wata hanya mai kyau su nuna maka
abubuwan da zasu gina maka rayuwa, su tabbatar maka da kariyar mutuncinka. Ka sani wannan ba zai taba faruwa ba har abada, ko da a
cikin wasa. Abin da kawai za ka yi shine shuru da bakinka a duk lokacin da kuke
tare dasu. Sannan ka da ka damu da abin da za su ce ko za su yi tunani
game da kai, sabuda suna son ka ne don abin hannunka. Wannan tunanin nawa, mutane su rike shi
saboda gudun shiga yanayin rashin sanin makiyi, ku adana a cikin zukatanku, ku
dinga tuna wannan har abada. Ku tunatar da ‘ya‘yan ku tun kuna tare, ku
fahimtar da su za su girma wata rana. Rayuwarsu za
ta yi haske sannan kuma za tayi kyau. Mayanka/Mahauta tana ganin rayuka a
kowace rana, wata rayuwar sai an zu ta ke tafiya, wata kuma za ta zo bata gaba
daya. A tsawon lokacin aikin ka, ka kasance mai fara’a a fuskarka. Idan suka zo
ba dole ba ne gareka da ka cigaba da tattaunawar da ka ke ba, amma ka nemo
yanda za kayi shuru, don ka kawar da tunaninsu. Ka yi tunani fa ba sa ra’ayinka
kamin wannan lokacin da ka samu cin gashin kanka. Saboda kasan kana da amfani
da wannan mutumin wanda ke da kyakkyawar manufa a gareka. Ka yi tunani wannan
mutum ba zai taba amfani ba a duk kan sha’aninka da al’amurranka da ka ke
gudanarwa, nemi aboki na gaskiya wanda ka ke da tabbaci tsara ne a rayuwaka,
wanda zai zauna har karshe ku na tare. Rayuwa za ta samu cika da bambanci wajen
tafiyar ta. Sirrin ka da tsaro don kana da tabbacin suna daya daga cikin
rayuwarka.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 39
So shine a kullum mafificiyar kyauta
kuma ta kan samu kai tsaye batare da zato ko tsammani ba.
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 40
Zaifi a tsaneka (ki ka) da yanda ka
ke. Da a So ka da yanka ba ka kai ba
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 41
Zaman lafiya kan maida komai mai yiyuwa. So kuma kan mai da komai mai sauki
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 42
Zuciyar da take dauke da soyayya
itace mafi amintuwar zuciya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 43
Duniya
na kama da kasuwa lokacin da zaka shiga tabbas lokacin wani zai barta ba dawowa
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 44
Duniya
misalin ta misalin dan aike ne da ubangidansa ya aikeshi kuma ya samu wuri ya
fake yana jiran dawowarsa daga inda ya aike shi
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 45
Duniya
ki dauka ki aje duk yanda mutum ya ke jiji da kai yake wani fadi wallahi wata
rana sai anyi bashi kamar yadda akayi babushi kamin shi
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 46
Duniya
da rayuwa abokai ne idan ka biyewa rayuwa ita kuma duniya zata biye maka amma
kuma ka sani cewa zasu kai ka su baro wata rana
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 47
Duniya
kamar misalin bako ne da zai sauka a gidanka komai dadewa wata rana zai bar
gidan zuwa gidanshi na ainihi
MAGANGANUN HIKIMA:
SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 48
Duniya!
Abin ayi hattara da ita ce domin idan kayi sakaci wata rana zata saka kuka
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 49
Duniya
kamar gona ce duk abin da ka shuka babu makawa shi ne abin girbarka
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 50
Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba tamkar jakine da kaya
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 51
Duniya!
Zamanta ba a nemi lahira ba kamar kasuwanci ne da ba riba a cikinsa
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 52
Duniya!
Wasu na kuka a cikinta wasu ko dariya suke
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 53
Duniya!
Yanda aka zo cikinta babu komai tabbas haka ake barinta babu komai
MAGANGANUN
HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 54
Duniya
kamar hadarin mushaki ne (hadarin da baya ruwa) ana ganin hadari ya hadu kamar
da gaske ruwa za a yi sai kaga ya watse wayam!
Masha Allah jazakallahu khairan zadakallahu ilman wa imanan wa taufiqan
ReplyDeleteMasha Allah
DeleteAllah Yasaka da Alkhairi 🙏
ReplyDeleteAllah ya tai maka
DeleteMasha Allah muna gdy
DeleteAllah yatsare
ReplyDeleteMasha Allah muna jin dadin hakan Allah kara basira da daukaka
ReplyDeleteGreat and I have a nifty supply: Who Repairs House Siding residential renovation contractors near me
ReplyDelete