Saturday, 31 March 2018

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 01

Sanin mutuncin bawa wannan sai Allah don shi ya san iya gatan da ya tanadar mishi a ranar tsayuwa. Mu girmama mutane ko muma za a girmama mu.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 02

Hakuri guzuri ne, Allah Ya na tare da masu hakuri.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 03

Kyautatawa mutanenka shi kuma Allah Ya kyautata maka. Idanuwanka su daina rufewa kan abin duniya da ka samu, wata rana kana ji zaka bar abin da ka tara ko kuma abin da ka tara ya barka. Don haka mu lazimci taimako don kaucewa yin da nasani

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 04

Duniya Labari,
Duniya Makaranta,
Duniya Kasuwa,
Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 05

Duniya bata gurbacewa a sanadiyyar masu aikata barna da ke cikinta, sai dai tana gurbacewa ne a sanadiyyar wadanda ke ganin ana aikata ba daidai ba su sa ido suna kallo basu ce komai ba.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 06

Ko kana cikin masu matattar zuciya wanda baya ganin d’an wani nashi? Yi maza ka gyara halinka d’an makocinka ya zama d’anka, haka ake yi sai rayuwa ta dawo sabuwa.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 07

Taimako ma’adanace da bata gunda, gara ko tsatsa. A duk lokacin da ka yawaita taimako shi kuma Allah zai yawaita maka a cikin duniyarka.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 08

Mutuwar zuciya abune mai muni, yawan barace-barace fitinace ga musulmi.
Muyi kokarin rufawa kanmu asiri ko ma samu martaba a cikin idon makiya.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 09

Sana’a sa’a inji bahaushe.
Mu rike sana’a don itace ke da kaso 99% na arzikin da aka saukar a cikin duniya.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 10

Wasu sunce dare mahutar bawa.
Ni na ce dare mahangar bawa
Mu bi dare, mu raya dare domin cimma nasara akan al’amarinmu.
Dare shine lokacin cin nasara ga kowane irin abu da ake nema.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 11

Bi rayuwar nan a hankali don kuwa baka immata. Haka Rayuwa take da nauyi fiye da duniya.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 12

Duhu baya gusar da Duhu: haske kawai ke yin wannan. Tsana bata gusar da tsana (kiyayya): So kawai ke yin wannan.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 13

Kyautatawa wanda ya kyautata maka, haka ake yi. Butulci guba ne wata rana za’a yi da-na-sani na har abada.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 14

A duk lokacin da ka taimaki wani to, Allah zai taimake ka. Sirrin kenan taimakawa jama’a sai ka daukaka akansu..

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 15

Shin ko kana kishin Kasarka? Wannan shine mafi girman al’amari da burin da ake nema ga reka. Ka so kasarka ko ka samu martaba a wajen Ubangijinka, Son kasa wajibi ne ga kowa..

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 16

Kada kayi mummunar adu’a ga Shuwagabanni, domin lalacewarsu kai zata shafa. Kyakkyawar addua ita ce maganin dukkanin bakin ciki.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 17

Shin kai mai amana ne? ko mai gaskiya ne kai? amana da gaskiya suna tafiya ne a tare, ka rike amana kuma ka fadi gaskiya zaka buwaya.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 18

Gaskiya na da daci, haka ne. amma kuma gaskiya itace hanyar tsira da cin nasara.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 19

Ka fadi gaskiya koda kuwa za’a kashe ka, bayan ka bar duniya, gaskiyar za tayi halinta. Rashin ka zai rama barazana a cikin zukatan su.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 20

Ko kana so ka buwayi makiyanka, rufe sirrinka kuma kayi dariya lokacin kuka za suyi tsammanin ba suyi nasara ba.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 21

Addua itace makamin mai imani, ka rike addua don cin galaba ga makiya

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 22

Ka kyautata manufarka kuma ka tsarkake zuciyarka ba zaka kunyata ba

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 23
Kada ka damu da cewa karya ta mike kafa. Tabbas karya zata gushe. Kada ka damu da tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana? Lallai za ta bayyana komai dadewa. Abin da ya kamata ya da meka shi ne, menene matsayinka; a kan gaskiya ka ke ko a’a?
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
.
MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA
FITA TA 24

A lokacin da na karanta, na dade ina tunani me yasa Karya take da kyalle da  sha’awa gamai yin ta? Kuma gaskiya take da tsananin daci tare da sanya bakin jini ga mai kiyayeta: Gaskiya itace misalin bullowar rana: sannu sannu, sannan gaba daya a lokaci guda.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 25

Ba Dabi’ar So ba ne, sai dai Dabi’ar abota ne yin auren da babu farin ciki a cikisa.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 26

Ka zama mai Rahama ga Mutane: Mai yiyuwa ne kaima ka samu Rahamar Allah.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 27

Ka yi magana mai kyau ga kowa don itama Sadaka ce

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 28

Kayiwa bakinka linzami wata rana sai ya jefaka a rami

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 29

Zina itace mafi munin laifi a cikin al’uma, ka guji aikata ta, don kaucwa mummunan sakamako.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 30

Nagarta itace hali mai kyau, ka zama mai nagarta sai ka rabauta.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 31

Kayi jinkai da wadanda basada, ka tausaya musu, wata rana za kayi galaba…

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 32

Kada kiyayyar da ke tsakaninka da makiya ta hanaka fadar gaskiya akansu. Wannan shi zai kusantar da kai ga jin tsoron Allah.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 33

Yi kokarin zama mutum wanda ya san ya kan iya yin kuskure: kuma idan ya nemi gafara. Ganin kankantar laifi bala’ine mai girma.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 34

Duk wanda ya raina mace to bai san asalinsa ba, wanda ya wutakanta mace, bai godewa Allah ba, don mace ni’imace da Allah ya yi zuwa ga namiji

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 35

Kauna da dadi amma kima ta na idon mai kunya

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 36

Kayi komai cikin so, shi ne matakin cin nasara

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 37

Ni ba wani abu mai muhimmanci bane, ga wannan ni mai tabbaci ne. Ni mutum ne da ba kowa ba kuma ina yin rayuwa ta a matsayin haka. Ina sanar da ku wannan ku sani sunana ba da dadewa ba za a manta dashi, amma ka rayu kana son wani da dukkanin zuciyar ka da rayuwar ka, wannan shine wadataccen abu har kullum.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 38

Sau daya a rayuwa, Na yarda na amince, ka samu wanda ka ke tsammanin zai taimaka maka a rayuwa. Ka sanar da shi wani abu wanda baka taba sanar da wani shi ba a rayuwar ka amma sai ya tarwatsa ya fallasa dukkanin sirrin ka. Sannan kuma ya nemi da ka kara sanar dani wani. Sai na sanar dashi manufar rayuwa, manufar da ba zata taba zama gaskiya ba, manufar da ba zan taba cimma ba, da kuma wadansu abubuwan da banshirya a cikin rayuwa ta ba.  Lokacin da wasu abubuwa masu kyau suka faru, zaka tsaya don sanar da su game da abubuwan, alhali ka sani zasu tarwatsa maka al’amari.  Basu damu da suyi kuka tare da kai ba idan ka shiga tsananin damuwa ba, ko farin ciki lokacin da ka shiga nishadi. Ba zasu taba aikata wannan ba, don sun tsani al’amur ranka, ko suna so ka kasance a kullum a wulakance ba ka da amfani, sannan kuma suce sune zasu doraka a bisa wata hanya mai kyau su nuna maka abubuwan da zasu gina maka rayuwa, su tabbatar maka da kariyar mutuncinka. Ka sani wannan ba zai taba faruwa ba har abada, ko da a cikin wasa. Abin da kawai za ka yi shine shuru da bakinka a duk lokacin da kuke tare dasu.  Sannan ka da ka damu da abin da za su ce ko za su yi tunani game da kai, sabuda suna son ka ne don abin hannunka. Wannan tunanin nawa, mutane su rike shi saboda gudun shiga yanayin rashin sanin makiyi, ku adana a cikin zukatanku, ku dinga tuna wannan har abada. Ku tunatar da ‘ya‘yan ku tun kuna tare, ku fahimtar da su za su girma wata rana. Rayuwarsu za ta yi haske sannan kuma za tayi kyau.  Mayanka/Mahauta tana ganin rayuka a kowace rana, wata rayuwar sai an zu ta ke tafiya, wata kuma za ta zo bata gaba daya. A tsawon lokacin aikin ka, ka kasance mai fara’a a fuskarka. Idan suka zo ba dole ba ne gareka da ka cigaba da tattaunawar da ka ke ba, amma ka nemo yanda za kayi shuru, don ka kawar da tunaninsu. Ka yi tunani fa ba sa ra’ayinka kamin wannan lokacin da ka samu cin gashin kanka. Saboda kasan kana da amfani da wannan mutumin wanda ke da kyakkyawar manufa a gareka. Ka yi tunani wannan mutum ba zai taba amfani ba a duk kan sha’aninka da al’amurranka da ka ke gudanarwa, nemi aboki na gaskiya wanda ka ke da tabbaci tsara ne a rayuwaka, wanda zai zauna har karshe ku na tare. Rayuwa za ta samu cika da bambanci wajen tafiyar ta. Sirrin ka da tsaro don kana da tabbacin suna daya daga cikin rayuwarka.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 39

So shine a kullum mafificiyar kyauta kuma ta kan samu kai tsaye batare da zato ko tsammani ba.

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 40

Zaifi a tsaneka (ki ka) da yanda ka ke.  Da a So ka da yanka ba ka kai ba

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 41

Zaman lafiya kan maida komai mai yiyuwa. So kuma kan mai da komai mai sauki

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 42

Zuciyar da take dauke da soyayya itace mafi amintuwar zuciya

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 43

Duniya na kama da kasuwa lokacin da zaka shiga tabbas lokacin wani zai barta ba dawowa

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 44

Duniya misalin ta misalin dan aike ne da ubangidansa ya aikeshi kuma ya samu wuri ya fake yana jiran dawowarsa daga inda ya aike shi

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 45

Duniya ki dauka ki aje duk yanda mutum ya ke jiji da kai yake wani fadi wallahi wata rana sai anyi bashi kamar yadda akayi babushi kamin shi

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 46

Duniya da rayuwa abokai ne idan ka biyewa rayuwa ita kuma duniya zata biye maka amma kuma ka sani cewa zasu kai ka su baro wata rana

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 47

Duniya kamar misalin bako ne da zai sauka a gidanka komai dadewa wata rana zai bar gidan zuwa gidanshi na ainihi
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 48

Duniya! Abin ayi hattara da ita ce domin idan kayi sakaci wata rana zata saka kuka
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 49

Duniya kamar gona ce duk abin da ka shuka babu makawa shi ne abin girbarka

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 50
Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba tamkar jakine da kaya
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya
MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 51

Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba kamar kasuwanci ne da ba riba a cikinsa

Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 52

Duniya! Wasu na kuka a cikinta wasu ko dariya suke
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 53

Duniya! Yanda aka zo cikinta babu komai tabbas haka ake barinta babu komai
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

MAGANGANUN HIKIMA: SHIRIN SAHIHIYAR RAYUWA

FITA TA 54

Duniya kamar hadarin mushaki ne (hadarin da baya ruwa) ana ganin hadari ya hadu kamar da gaske ruwa za a yi sai kaga ya watse wayam!
Sharahbil Muhammad Sani: www.sahihiyarrayuwa.tk www.facebook.com/sahihiya

8 comments:

  1. Masha Allah jazakallahu khairan zadakallahu ilman wa imanan wa taufiqan

    ReplyDelete
  2. Allah Yasaka da Alkhairi 🙏

    ReplyDelete
  3. Allah yatsare

    ReplyDelete
  4. Masha Allah muna jin dadin hakan Allah kara basira da daukaka

    ReplyDelete
  5. Great and I have a nifty supply: Who Repairs House Siding residential renovation contractors near me

    ReplyDelete