Friday, 3 February 2017

SO ZAI SAKANI IN MIKI KOMAI...

SO ZAI SAKANI IN MIKI KOMAI...


Ni na aminta So zai sakani in miki komai
Na zamo gwani na fada kan sonki an kirani Jarmai 

Soyayyah silar rikicewa na rike maikamai
Sunanki ya zamo lakabi gareni na zama na Sadiya an fada maimai

Naga Sauyin al'amarina 
Sai tunani safe da rana 

Duk wanda zaya soki na shaida bai zai kai ya ni ba
 Sunanki ya fimin komai daraja bangano yashi ba 

Wazai tabaki in har gani da rai bai ciyo wuya ba
Sam bani fargaba sanadin So na daura damba

Ban bukatar Amini gyara
A tabaki in saka Sara

Shi so saboda bashida tabbas aka kirashi tsuntsu 
Hanta da Zuci in suka firgice So ne yake tsumasu 

Zanso batun da nayyo miki Soyayya tawa ki gamsu 
So yasa nazama gwarzo 
 Kici nama ni inci kanzo

indai ban ganki ba kunci kan hanani bacci 
ko yanayi na sanyi sai na rika mafeci ....

No comments:

Post a Comment