Ku kalli wannan matar da ke bayani akan zaben 2019
LAFAZIN SOYAYYA
The No: 1 Hausa Love Website in the World
Monday, 21 January 2019
Sunday, 20 January 2019
TUNATARWA
Don Girman Allah Karkai Ido Biyu Da Wannan Sakon Baka Tura Zuwa Gababa, Koda Baka Da Lokacin Karan Tawa...
Insha Allahu Wasu Da Yawa Zasu Amfana, Allah Yasa Harda Ku...
Manzon Allah s.a.w Yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAQUMMA"
Wani mutum yazo wajen manzon Allah S.A.W. ya ce: Yah-Manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.
1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane? Sai ya ce "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa."
2. Ina son in zama mafi arziQi a cikin mutane? Sai ya ce "Ka zama mai wadatar zuci."
3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane? Sai ya ce "Ka zama mai amfanarwa."
4. Menene zai kare ni daga wuta?,Sai ya ce "Ka zama mai yawan yin Azumi."
5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane? Sai ya ce "Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka."
6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah? Sai ya ce "Ka yawaita tuna Allah."
7. Ina son imanina ya zama ingantacce? Sai ya ce "Ka gyara halayen ka."
8. Menene yake huce fushin Allah S.W.T.? Sai ya ce "Ba da zakka a boye da kyautata ma 'yan uwa."
9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah? Sai ya ce "Mummunar hali shine rowa"
10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah?,Sai ya ce "Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah."
YA ALLAH Ka sa mu gama daduniya lafiya.
CHIARMAN GWANDU LOCAL GOVT YABA YANSANDA UMARNIN A KAMOMAI NAMAI'KYAU TARE DA TSARE MAI SHI ...
Daga Namaikyau ...
ZUWA GA GWAMNATIN JAHA DA SAURAN WA YAN DA ABIN YA SHAFA .
*SIRRIN ABINDA YA FARU*...
Rigimar Garin Barama dake karkashin karamar hukumar mulki ta Gwandu, Da Chairman din Gwandu Local Govt, Alh Shehu Bagudu Dalijan,
Hakki Na Farko Da Yafara Tauyewa Mutanen garin Barama Shine Lokacin Damina Anyi Iska Kwaninka Rufi Duk Sunkware, Anyi Anbaliyar Ruwa Tsakiya Garin Barama da gidajen Su Duk Suncika Da Ruwa Anyi Kusan Kwana Arba,in Ruwa Basu Janye A Tsakiyar Garin Barama ba,
Gidaje Suka Rurushe Nikaina Mai Wannan Rubutun Nayi Gina Ciki Da Falo Ko Shigarsu Banyi Ba Suka Rushe
Dakunan Da Suka Rushe Sunfi Dari A Lokacin Har Yanzu nan Wasu Basu Sami Daman Gyarawa Ba Saboda Rashin Abin Gyara,
Amma Chairman Baije ba kuma bai aika ba,
Gwamna Ya Turawa Gwandu local Govt Tallafi Akan A rabawa Wa Yan da Wannan Iftila,in nan da na lisafa Ya Shafa Amma Abin Mamaki Ko Magajin Barama Baisan Anyi Ba Ma,ana dai Babu Mutun Ko Daya Daga Cikin Barama Da Ya Samu Wannan Tallafin, Kuma Ina Sane Amma Ban fadawa Duniya ba,
Akazo A Kan Maganar Hanyar Da Tatashi Daga Gwandu Tabi Ta Barama Yawuce Argungu, Mu Mutanen Barama Bamumasan Da An Awon Hanyar ba muntashi Da Safe Kawai Mukaga Awo Yabiyo Ta Garin Barama Amma Sai Wani Kauye Da Ke Kusa Ga remu da Yake Suke da manyan yan Siyasar da akasani Suka Turo Yaran su Cikin Dare Suka Ciccire Itacen Awon Hanyar Suka Mayarda Shi Can Kauyensu, Abin Yazan Rigima Bamu Dauki Mataki ba mukaje Gurin Chairman muka Sanar da shi Halin Da ake ciki Yazo Dakansa yaga yadda Abin Yake Yace Wayan can yan kauyen basuda gaskiya Dan haka aiki nan barama zaayishi Saboda nan Awo Yabi Yayi Mana Rantsuwa Takai 3 Akan Bazaadauke Aikin nan daga Barama ba, Bayan Sati Biyu Zuwa 3 Sai Gashi Yadawo Tare Da Wa yan can yan Siyasar Kauyen Da aka Sani,
Zasu Dauki Motocin Aikin Hanyar Su Mayar da su Wacan Kauyen Batare Da Wani Bayanin Fahimta ba, Mukace Bamu Yarda Ba Abin Yazan Rigima Har Yayi Kirarin Sai Dai Duk Wanda A cikin Barama Yakare Amma Sai Ya Dauki Motocin Ya Mayarda Su Wajen Masu Galihu,
Mu kuma Mukace Sai Dai Yakashe Mu din Kamar Yadda Yayi Ikirarin Amma bazamu Yarda A Dauki Motoci Ba Daga Inda Gwamnati Ta Ajesu A Mayarda su Inda batasan da can ba, Daga Karshe Dai Komawa Yayi Yataho Da Motacin Yan Sanda Sunkai 16 Sukayi Tayi Mana Halbe Halbe Cikin Barama Babu Wanda Ya Kulasu, Saboda Tin Kafin Suzo Nayi Wani Bincike Akan Hanyar Nagano Sukadai ne Ke Haukar su Nacema Mutane Idan Yadawo Daukar Motar Sukyaleshi Kawai Saboda Bashi ne Dankwangilar Hanyar ba kuma ba Dan kwangilar yaturo shi ba Wannan Dalilin ne Ya hana akashe Mutanen Barama Ranar Da Yanzu Munzama Tarihi, Amma Wanna ma ban gayawa Duniya ba,
Yanzu Kuma Yadawo Maganar Dajin Da Ya Tabbatar da dashi Mutanen Barama Suka Dogara Saboda Ya Kwantata Mana Ya Damkawa Hillanin Da Basufi Su 20 Ba Dajin,
Bayan Kuma Duk Inda Yakamata Muje Saboda Ayi Mana Sulhu Tsakanin Mu Da Hillanin Nan Wlhy Munje Amma Anki Azo A Sulhuntamu Muzauna Lafiya Ko Dan Zaben Da Ke Tafe, da kuma magance rigima tsakanin Fulani da manoma.
Mutanen Kauyukkan Da Suka Shafi Argungu Local Govt Da Gwandu local Govt Anyi Meeting Akan Cewa A Raba Hulda Da Hillanin Nan Kar Asaya Garesu Kar A Sayarmasu Kar A Shiga Mota Daya Da su Idan Kuma Sun Mutu Kar Aje Janaiza Bale Gaisuwa,
Jin Wannan Hukunci Yasa Nayi Videon din tare da Hotuna Yada Domin Mahukunta Sushigo Cikin Lamarin Su Sulhuntasu A Zauna Lafiya, domin taimakawa gwamnatin jihar kebbi Wurin kokarin da takeyi Wurin kawo zaman Lahiya a cikin fadin jihar.
Amma Lokacin Da Wa yan da Abin Ya Shafa Sukagani Sukasa Aje Ayi Masu Bincike,
Shikenan Sai Chairman Ya Nuna Baisan Da Wannan ba Sai Ya Bincika Bayan Ya Bincika Yaga Labarin Da Video Sai Yasa Akira Daya Daga Cikin Mutanen garin Barama Ayi Sulhu Bayan Yaje Sai Yasa D p o Na Yansanda Ya kulleshi Yau Kwana 3 Kenan Anyi Ta zuwa Dpo Yaki Bayarda shi Yace Chairman Yace A rike mai shi Sai Ya Nemeshi, Yanzu Kuma Ya ba Dpo Umarnin Ya Kamoni Duk Inda Nake Tinda Ni Na Watsa Labarin Azo Ayi Sulhun Rigimar Da zata Iya Kawo Fadan Kabilanci, Shine Laifina, Yanzu Haka Bayan Wanda Suka Tsare Tin Shekaranjiya Yau Ma Dpo Yakirani Yace min Zasu Rike Magajin garin Barama Har Sai Nakawo Kai na,
Dan Haka Ina Sanarda Duniya Da Yan Uwana Yan Social Media Da Manyan Yan Siyasar mu Idan Kuka Daina Ganin Postin dina To Sunkamani Saboda Su Walakanta ni, ciki da gaskiya wuka bata hadashi,
Yanzu haka wasu cibiyoyin watsa Labarai da yawa sun kira ni kuma na fasa kwai saura D. P. O. Da kuma wanda yasa shi tsare mutane fiye da Kwana 3 Suma su fadawa Duniya nasu dalilin yin amfani da mukamin su na Duniya Domin takurawa talakawa.
By Namaikyau ...
KUNDIN QADDARATA
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
6⃣3⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*MANZAN ALLAH S A W YANA CEWA,KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGIN DABINO NE*
_____________________________________
"Ka yimin afuwa,a yanzu haka tafiya zanyi ta shekara daya,ka barni har na dawo don Allah,na sani cewa ka cika mutum,kuma ka nunan dukkan wata qauna da halacci,amma ina son ka barni har zuwa sanda zan dawo daga wannan tafiyar,wala'alla zuwa sannan zuciyata ta sake sanyaya daga rashin da nayi,ka sani abdur rahman yadda mutuwa ke da ciwo da wuyar barin zuciya,kayi haquri da ni don Allah" ta qarashe maganar muryarta na rawa idanuwanta na tara hawaye,tausayinta ya kamashi,ya sani cewa raba zuciyar sumayya da mukhtar ba qaramin abu bane,a kanshi ta fara sanin so da qauna,a kansa ta fara sabawa da wani namiji baare,ta soma iya magana da d'a namiji,tilas yaci gaba da haquri kafin ya cimma burinsa,zaici gaba da addu'ar samun zabi mafi alkhairi,kafin lokacin dawowarta ya tabbatar shima duk wasu burikansa sun gama cika,ya kammale hankalinsa guri guda,dubanta yayi cikin sigar lallashi
"Na sani cewa shekara daya ba kwana daya bace,amma gurin Allah ba komai bace,Allah ya nuna mana,amma kema sai kinyi yaqi da zuciyarki,sannan kada ki bawa wani dama bayan ni,kinyi alqawari?" Murmushi tayi saboda maganar ta bata dariya,to shi dinma tanqwara zuciyarta take qoqarin yi ina ga ace ta bawa wani dama,ko ya mance zuciyarta ba lafiyayya bace?
"Baka da wannan damuwar" ta fadi tana kada kai,maganar tayi masa dadi sai yayi murmushi ya soma janta da hira,bai tafi ba sai da ya rage mata damuwa sannan sukayi sallama.
A daren kasa bacci tayi baki daya,juyi ta dinga yi daga farkon gado zuwa qarshensa,tunani fal zuciyarta,zuciyarta sam babu dadi,rayuwa kenan,yau zaqi gobe madaci,abinda ya dinga yi mata kai kawo kenan har bacci barawo ya dauketa.
Kwanakinsu a kano sunyi mata dadi qwarai,ana ta gabatar da hawayan sallah irin na al'ada don ma saura suka tarar,garin cike yake da baqi cikin kowanne sassa na duniya masu zuwa kano daga qasashe daban daban,kama daga qasashen turawa har na larabawa don ganin hawan sallahr garin kano,wanda babu irinshi kaf arewa saidai a kwaikwayeshi,ta yadda tabbas kano nan ake morewa bikin sallah ba kamar sauran garuruwa ba da basusan ana yiba ma,tayi hira da mama malam da qannenta iya son ranta,abin dadin uncle farouq ya qara musu kwanakim yace su cikashe kwana goma,randa suka cika sati suka soma zaga 'yan uwa da qawayen anty dije suna musu sallama,kusan ko ina da sumayyan aka je don itama ta yiwa dangi sallama,kwana biyu suka kammala ya rage musu kwana biyu su koma abuja don fara shirin tafiya uk london.
Washegarin ranar da zasu tafim bayan ta gama hada kayanta baki daya ta shirya tsaf ta shirya abdallah,ta riga data yiwa driver magana zata unguwa,gidan yaya yahaa take son zuwa don yi mata sallama,anty dije tace zaya zo ya kaita,qarfe sha biyu na rana ya iso,ta yiwa mama sallama ta dauki abdallah suka tafi.
Daga falo suke amsa sallamar tata,yaya yahanasun ce kawai ta dauki murya,jamila fatima da fiddausi nr zaune duka a falon,gefe kwanon koko ke da kofuna da alama shi suka gama sha,baki daya fiddausin ta fige ta fita kamanninta tayi baqi kamar ba ita ba,yaranta uku a yanzu (banda yaran data haifa wanda sumayya taje sunansa)har yau tana gida babu wani ci gaba,uwar miji tace ba zasu iya ba ta cika haihuwa,danta ba qarfi gareshi ba,sai su fatima da rashin aure kan lokaci yasa suka soma tsotsewa,jamilan ta qwallafa rai kan wanda takeso shi kuma yayarsa ta hana tace auren gida zaiyi,fatima ma kuwa babu maganar kowa,baki dayansu anty dijen ke riqe da su,abun akwai tausayi,mataimakin madogarar dama qwaya daya ne MUKHTAR,a yanzu da babu shi kuwa babu wani mai dubansu,dukkaninsu washe bakin ganinta suke itama tana amsa musu fuska sake har tayi matsugunni kan daya daga cikin kujerun,tuni abdallah yayi wajen yaya yahanasu,ta rungumeshi tana shafa kansa tare da duban fuskarsa,qwalla ta cika mata idanuwanta har ta soma gangarowa,duk sanda taga yaron mukhtar yake tuna mata,kamanninsu daya,tana jin kanta a mai laifi,a wadda tayi silar maida shi maraya,kullum kwanan duniya sai ta yiwa zainab Allah ya isa.
Baki dayansu jikinsu yayi sanyi ganin yadda yayan ke share hawaye,tuni itama sumayya ta fara goge tata qwallar,tsawon mintuna kafin su bawa zukatansu haquri sannan suka shiga gaisawa,baki dayansu kunyar sumayyan sukeji,ga wani girma da suke bata na daban,ranar anan ta wuni,har la'asar,sai ina kasa ina ka ajjiye suke da ita,sai da tayi sallar la'asar sannan tayi sallama da su bayan ta ajjiye ma yaya yahanasun sabulai klien da su maggi cikin leda mai layi layi,sannan ta baiwa fatima da jamila dari biyar biyar,fiddausi dubu daya duk cikin irin kudadenta.
Hakanan ta tsinci kanta bayan fitowarta da yiwa mai a daidaita sahun data tsaida kwatancan gidanta,ma'ana gidan qarshe da suka zauna da mukhtar,wanda tun wajen raba gado ya shigo cikin kasan su,daidai madaidaicin get din gidan ya ajjiyeta,ta sallameshi ta dauki abdallab,jakarta ta laluba cikin sa'a muqullan na ciki ta sanya ta bude fa shiga.
A hankali ta dinga takawa tana duban gidan,duk taku guda na dawo mata ne da duk wata rayuwa tata da ta shude can baya,sannu a hankali zuciya da gangar jikinta suka raunana,ta dinga takawa a sannu har ta kai ainihin falonsu,duk kayanta na jere ma ciki babu abinda ta fitar,saidai gidan yayi qura sosai saboda rashin kasancewar kowa a ciki,shimfide abdallah tayi saman kujera wanda ya soma bacci tun cikin adaidaita,idanuwanta suka wurga zuwa qofar da zata sadaka da bangaren mukhtar,sai ta miqe tana duban qofar harta sada kanta da ainihin dakin gadonshi,babu komai ciki kamar yadda mamallakin gun bai duniya,sai ta gaza riqe hawayenta suka fara sintiri kan kumatunta,gefe guda ta duqe tana bin bango saboda rawar da jikinta keyi ta rushe da kuka mai tsuma rai da zuciya,ta jima tana kokawa sannu a hankali har nauyin dake cikin zuciyarta ya soma raguwa,ta share qwallar tata ba don ta qare ba ta juyo da niyyar miqewa,abdallah ta gani tsaye bayanta yana kallonta
"Wa ya saki kuka ammi?"hannu ta miqa masa alamar ya taho,ya taho din kuwa ya fada jikinta ta rungumeshi tana ci gaba da goge hawaye.
Sai data samu nutsuwa cikin ranta sannan ta qarasa zagaye gudan,duk inda ta taka da abinda zau tuna mata,a haka ta kai har biyar da rabi sannan ta lalubo abdallah dake can wani gu yana wasansa ta sauya masa kaya ta rufe gidan suka fito idanu jajur na kukan da ta sha.
Washegari suka kama hanyar abuja,hankalinta yasi dagawa na barin abdallah da zata sakeyi,bata so yayi maraici irin na mahaifinshi,babu uwa babu uba,saidai ganin yadda sam bai damu ba shi ya kwantar da hankalinta,da fari ya soma maqale maqale amma daga bisani sai ya ware har da shi a masu daga mata hannu,ajiyar zuciya ta saki bayan sun hau hanya sosai ta maida idanuwanta ta rufe,sam bata son komawa abujan nan,tafi qaunar garinta kano,koba komai kowa nata yana can,da zata iya data roqi su anty dijen su barta a can din,saidai yin hakan tamkar butulci ne ga qaunar da anty dijen ke nuna mata fiye da dukkan wata 'ya dage cikin danginsu,duk da 'yan maganganu da ke fara tsowa na hassadar riqon nata da antyn keyi.
Kasancewar basu taso da wuri ba shi yasa basu suka isa gida ba sai takwas na dare,a gajiye kowa yake,saboda haka kowa gun kwanciya ya nema idanuwa cike da bacci,dama tuni sunci abincin darensu kan hanya.
Washe gari da gyaran gidan suka tashi,suka kintsa ko ina,kafin wani lokaci gidan ya dawo hayyacinsa,basuyi dai break da wuri ba saboda aiki.
Zuwa la'asar har abincin dare sun gama,su khalipha na dakinsu suna gayaran kayayyakinsu tare da fara ware wanda zasuyu tafiya da shi,sumayya na zaune falon tana hutawa,hannunta riqe da waya tana neman lambar mama don su gaisa ta kuma ji ya abdallah yake,sallamar amira ita ta katse mata abinda take shirin yi din,ta shigo sanye da yadin sartin baqi sidik wanda aka yiwa doguwar riga,sai dan madaidaicin jan mayafin data yane kanta da shi,cikin fara'a sumayyan ke dubanta har ta qaraso ta samu wajen zama
"Mutanen kano ta dabo,sauka ba sanarwa?"
"Kada ki qorafi,saukar dare ce,har yanzun kuma bamu gama watstsakewa ba,sai dazun muka gama saita gidan"
"Gaskiya kam,ko mu muna nan muna hutu,baqi sun tafi sun barmu da kewa,gidan ba kowa duka ba dadi,kowa ya koma inda ya fito,dadin abun daya nima next week zamu koma school" murmushi kawai tayi,suna hutawa tamkar sunyi hidima da baqin,bayan komai akwai masu aiki dake gudanarwa
"Gaskiya kam ansha baqi,saidai Allah ya bada lada"
"Amin" amira ta fada tana lalubo wata number cikin wayarta qirar iphone 7
"Ki duba dakina can wajen bedside drower akwai black bag ki kawomin gidan umman khalipha" abinda tace kenan cikin salo na bada umarni ta kashe wayar,sumayya ta ajjiye lemo da ruwa gaban amiran tana tambayar maman husna,murmushi tayi tana daukar gorar ruwa
"Husna mutuniyarki,sun koma inda suka fito" idanuwa sumayyan ta dan fiddo
"Suma ba nan suke ba?"
"Eh,mijin anty farida custume ne,basu zama gu daya,yau suna can gobe suna nan,amma lokaci lokaci suna zuwa hutu da kuma lokacin bikin sallah kamar haka" kai ta jinjina
"Allah ya taimaka"
"Amin"hira suke tabawa kadan kadan har ta shigo bakinta dauke da sallama.
Sumayyan ta ganeta tare hadimar amiran ce,tare suke shigowa,isa da qasaitar gidan baabaa prof kusan kowa dame masa aikinshi shi daya,gaida sumayya tayi saidai ta kasa amsawa ta maida mata gaisuwar suka gaida juna,kusan zata dan girme musu saidai ita din yare ce,sannan ta rusuna cikin girmamawa ta miqawa amira jakar mai kyau,amsa tayi sannan tace
"zaki iya tafiya,idan ummee ta tambaya kice ina gidan umman khalipha"
"To madam" ta amsa ta fice,miqawa sumayya jakar tayi tana fadin
"Ga tsarabarki ta saudiyya,babu yawa a karba da haquri" murmishi ta saki tasa hannu ta karba tana godiya tare da fadin
"Mai yawan kenan" tana fidda kayan ciki,turaruka ne designers masu kyau guda uku,agogo cikin dan akwakunsa,sai hijabai saqar qasar oman suma guda uku masu azabar kyau,sun burge sumayya qwarai har sai data fidda murmushi saman lebanta
"Naga kina sonshi ne sosai"
"Naji kuwa dadin kyautarsa fiye da komai cikin kayan nan"
"Ina fata kin yaba"
"Qwarai da gaske" suka sa dariya baki daya,a nan anty dije ta fito,gaisawa sukayi sumayya ta nuna mata kayan ta gani ta tayata godiya.
Wayar amiran ce ta dauki qara,dagawa tayi tana dubawa,idanu ta zaro,a fili ba tare da tasan ta fadi ba
"Na shiga uku ya man yau kuma?" Da hanzari ta daga kiran ta kara kunnenta
"Ok,to yaya" ta fada tana miqewa
"Amiran umman khalipha na wuce,ya man ya aikeni na kaiwa umme waya kada ya qara kira ban je ba,ya kira wayarta taqi shiga haka land line din part dinta"
"Ok,muje na taka miki" sumayya ta fada tana miqewa
"Na gode" ta fada tana murmushi,don haka nan Allah yasa mata qaunar sumayya,burgeta take sosai.
Jerawa sukayi suka fito,suna gab da kaiwa qofa amira tace
"Uhmmm,ko ki tambayi ma mutuminki ko?"
"Ayyah,ya mahmoud,ki gaidashi don Allah nayi laifi kam"
"Um um,ni ba ma shi nake nufi ba,ya mustapha mana" shiru ta danyi gabanta na duka tunda ta ambaci sunam nashi,da ido amiran ke karantarta ganin bata ce komai ba har tana shirin fita ya sanya ta bar zancan ta soko wani
"Yaushe zaki shigo gaida baabaa,yana ta maganan baiga mamanshi ba" dan qaramin murmushi ta saki,sai taji tayi kewar tsohon duk da ba sabawa sukayi ba,amma saidai ko kadan bata sha'awa ko marmarin sake shiga gidan,tun daga randa abun ya faru.
"Ki gaida min baabaa da kyau don Allah,zan shigo idan Allah ya yarda" ta fada da siga biyu don bata da niyyar zuwa din
"Allah yasa da gaske ne,saikin shigo din na gode"
"Nike da godiya,ki gaidamin su ummee ma"
"Zasuji" ta fada tana ficewa tare da jin dadin yadda sumayyan ta nuna kulawa ga ahalinta.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
Tuesday, 15 January 2019
Fwd: TAKING ICT TO THE NEXT LEVEL........
---------- Forwarded message ---------
From: SAHIHIYAR RAYUWA S.R <sahihiyarrayuwa@gmail.com>
Date: Sat, Jan 12, 2019, 3:13 AM
Subject: TAKING ICT TO THE NEXT LEVEL........
To: <lafazinso.love@blogspot.com>
From: SAHIHIYAR RAYUWA S.R <sahihiyarrayuwa@gmail.com>
Date: Sat, Jan 12, 2019, 3:13 AM
Subject: TAKING ICT TO THE NEXT LEVEL........
To: <lafazinso.love@blogspot.com>
TAKING ICT TO THE NEXT LEVEL........
KEBBI STATE MULTIPURPOSE COOPERATIVE BUSINESS UNION TRAINS 200 YOUTHS
Kebbi state Government in collaboration Kebbi Multipurpose Cooperative Society is set to establish four standard ICT training centers and cafes this is in line with the State Empowerment Scheme designed for the women and youths.
The development followed the approval of funds by His Excellency, Governor Atiku Abubakar Bagudu. It is in line with the current administration passion for youths empowerment by equipping them with skills and developmental trainings so as to engage them positively and become financially independent. The participants are to be trained on various ICT skills which includes Computer Appreciation, Software and Web development, Printing amongst others.
Special Assistant on Youth Development, Nafiu Saidu Magini disclosed that the centers are tailored to be self sustaining by providing discounted services such as photocopying, Internet and secretarial services to the general public. He further stated that the centers will be located in all the four emirate councils in the state.
The scheme is one of the continuous efforts and commendable initiatives by office of the wife of the governor, Dr. Zainab Shinkafi-Bagudu to empower women and youths in the state. A total sum of N100,000M was approved by the state house of assembly out of which shops have been opened in 21LGAs and soft loans disbursed to women cooperatives to the tune of N60M. Hon Magini uses the opportunity to appeal to beneficiaries to be conscientious with paying back so that the scheme will continue to revolve.
Kasimu Abdullahi D.
For Hon. S. A Youth Matters
Kebbi State....
KEBBI STATE MULTIPURPOSE COOPERATIVE BUSINESS UNION TRAINS 200 YOUTHS
Kebbi state Government in collaboration Kebbi Multipurpose Cooperative Society is set to establish four standard ICT training centers and cafes this is in line with the State Empowerment Scheme designed for the women and youths.
The development followed the approval of funds by His Excellency, Governor Atiku Abubakar Bagudu. It is in line with the current administration passion for youths empowerment by equipping them with skills and developmental trainings so as to engage them positively and become financially independent. The participants are to be trained on various ICT skills which includes Computer Appreciation, Software and Web development, Printing amongst others.
Special Assistant on Youth Development, Nafiu Saidu Magini disclosed that the centers are tailored to be self sustaining by providing discounted services such as photocopying, Internet and secretarial services to the general public. He further stated that the centers will be located in all the four emirate councils in the state.
The scheme is one of the continuous efforts and commendable initiatives by office of the wife of the governor, Dr. Zainab Shinkafi-Bagudu to empower women and youths in the state. A total sum of N100,000M was approved by the state house of assembly out of which shops have been opened in 21LGAs and soft loans disbursed to women cooperatives to the tune of N60M. Hon Magini uses the opportunity to appeal to beneficiaries to be conscientious with paying back so that the scheme will continue to revolve.
Kasimu Abdullahi D.
For Hon. S. A Youth Matters
Kebbi State....
Monday, 14 January 2019
KOTUN DA'AR MA'AIKATA TA DAGE ZAMANTA AKAN TUHUMAR DA AKEYIWA ALKALIN ALKALAN NIGERIA
KOTUN DA'AR MA'AIKATA TA DAGE ZAMANTA AKAN TUHUMAR DA AKEYIWA ALKALIN ALKALAN NIGERIA
Kotun da'ar ma'aikata ta dage zamanta na sauraron shari'ar da ake wa Alkalin Alkalan Najeriya Mai shari'a Walter Onnoghen, bayan ya ki bayyana a gaban kotun a ranar Litinin.
Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Sai dai babban alkalin ya tura wasu manyan lauyoyi 47 wadanda suka wakilce shi.
Lauyoyin babban alkalin sun ce bai bayyana ba ne saboda ba a mika wa mutumin da suke karewa takardar sammaci a hannunsa ba.
Abin da ya sa kotun dage zamanta har zuwa ranar Talata 22 ga watan Janairun.
Bayan an kwashe lokaci ana gardama tsakanin lauyoyin da ke kare Mista Onnoghen da wadanda ke kara kan ko wajibi sai wanda ake kara ya bayyana a gaban kotun.
Sai Alkalin kotun Danladi Umar, ya ce dole sai ya bayyana a gaban kotun da kansa, kafin a fara sauraron karar.
Ko da yake lauyoyinsa sun ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar. Sun ce ba a bi ka'ida ba wajen gurfanar da shi.
Ana sa ran kotun za ta tube shi daga mukaminsa domin kada ya yi katsalandan ga shari'ar.
✍ MUDASSER SANI BIRNIN KEBBI
Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Sai dai babban alkalin ya tura wasu manyan lauyoyi 47 wadanda suka wakilce shi.
Lauyoyin babban alkalin sun ce bai bayyana ba ne saboda ba a mika wa mutumin da suke karewa takardar sammaci a hannunsa ba.
Abin da ya sa kotun dage zamanta har zuwa ranar Talata 22 ga watan Janairun.
Bayan an kwashe lokaci ana gardama tsakanin lauyoyin da ke kare Mista Onnoghen da wadanda ke kara kan ko wajibi sai wanda ake kara ya bayyana a gaban kotun.
Sai Alkalin kotun Danladi Umar, ya ce dole sai ya bayyana a gaban kotun da kansa, kafin a fara sauraron karar.
Ko da yake lauyoyinsa sun ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar. Sun ce ba a bi ka'ida ba wajen gurfanar da shi.
Ana sa ran kotun za ta tube shi daga mukaminsa domin kada ya yi katsalandan ga shari'ar.
✍ MUDASSER SANI BIRNIN KEBBI
Thursday, 5 April 2018
HUBBUL YAQEEN SERIES 5
HUBBUL YAKIN cigaba
ASIYA SADIQ MACCIDO
(ASIKHAN)
Copyright © Asiya Sadiq September, 2017
Hakkin Mallaka (M) Asiya Sadiq September, 2017
Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State, Nigeria
Tel: 08113777717
Book 1 of Hubbul Yaqeeen Series |
Shi kuwa
Sulaiman tunda ya wuce bai tsaya ko inaba sai a bakin gate din office dinsu,
kaf ya tsaya tsam kamar wanda yaga wani dodo, sani ya manta oganshi yayi
tafiya, ya tafi wajen wani comfrence da za’ayi a sokoto kuma zasuyi kamar kwana
shida zuwa biyar basu dawo ba, to meyasa ma wai bai tuna ba sai a yanzu, wani
tsaki yayi mai hade da takaici, said a yayi kamar minti biyar a bakin gate din
office din nasu sanna ya tada mashin dinshi ya nufi gidan Alhaji day a basu
haya domin ayita takare idan yanada wani gida ya canza musu ko kuwa asan yanda za’ayi
kafin nan da zuwan kwanaki shida da oganshi zai dawo ya nemi transfer ya bar
gari tun a kan layin gidan Alhajin ya fara ganin dandazon mutane ba adadi har
ya iso kofar gidansa, me zai gani ga dukan alamu wani abu akayi ras! Gabansa ya
fadi a wurinda shimfida take ya dire takalma yayi sallama ya mike hannu tabbas
gaisuwar rasuwa ake yayi gaisawa aka ansa masa ya nemi ya gana da babban dansa,
kasan cewar yasan sulaiman domin tare dashi akayi process din gidansu Sulaiman.
Bayan da Sulaiman ya kara yi masa gaisuwa ya tambayeshi yanda haka ta faru, ya
shaida mai matukar rudarwa, a jiya da dare ne yana bacci sai kawai akaga ya
mike tsaye ya sauka daga kan gado, ya farayin da baya-dabaya yana ta ko’ina har
ya fadi kasa, likitoci sun auna sun fada cewa sakamakon ganin wani mummunan tashin
hankali da idon dan adam da kuma kwakwakwar sa basa iya dauka da yayi shiya
hifar masa da wani matsanancin bugun zuciya da har yayi sanadiyar rasa
rayuwarsa a nan take dirshan ya fadi a kasa hawaye suka riqa zuba a idanuwansa,
al’amarinda yayi matukar bawa mutanenda ke wurin mamaki kenan hade da tausayin
musamman babban dan Alhaji, lallashin shi aka dingayi har ya dawo cikin
hankalishi ya daina kukan da yake. Shi kadai yasan abinda yakewa kuka tabbas
shakkah babu akwai wani mummunan abu dake shirin faruwa dasu, gashi sub a yan
gari ba yaya zai yi. Ya zabura ya mike ya sake gaisuwa yayi sallama ya wuce,
dole subar garinan gobe-gobe ba domin sko yanzu lokaci ya kure musu bad a sun
bar garin a yau, kara gudu yayi kamar wanda zai tashi sama domin kar dai wani
abu yazo ya sameta domin kuwa Bilkisu shi c eta fado mishi a rai, kar dai wani
abu yazo ya sameta. Krar shit ta dawo masa da hankalin shi daga tunaninda
yakeyi bai yi ni yar ya dauka ba kuma dai yaji bari ya dauka aljihu ya zara wayar
shi sanan abakinshi Nuhu ya gani da sauri ya dayka ya karakan kunnensa, slamu
alaikum ya fadawa alaikussalam, Sulaiman don Allah kayi hakuri kaga ban samu
dammar kawo su uUmmi ba Wallahi jiya da sakiyar dare mamansu ta kuma da
matsanancin ciwon ciki amai da gudawa tun sa’annan muna asibiti sai yanzu muka
dawo, yanzu dai Alhamdulillahi ta samu sauki sosai, kayi hakuri fatun sannan
ban masan ida wayana yake ba sai yanzu da muka dawo bare na kiraka na gagayama
bazan samu dammar kawo su ummi ba kasan ya yanda al’amuran suke wallahi tun
sannan bansamu nutsuwa ba sai fa yanzu da kaga na kiraka. Rasa ta cewa yayi can
ya lalibo kalamai yace ai badamuwa Nuhu Allah dai ya bata lafiya ya tashi
kafadarta sai munzo dubata nida Uwargidata tau amen, amee, Sulaiman, When sai
kunzo, sai an jima ya katse wayar. Wani matsanancin gudu yakeyi kamar ranshi
zai fiita ya nufaci gidanshi haiqan dearest!dearest! dearest! Yake fadi kamar
wani mahaukaci, da karfi yasha kwanar gidansi, kicibis! Yayi da wani abin ban
mamaki, Bilkisu ya hango tana fama dariya tana bye-bye da hannunta, kyar ya iso
a gabanta, murmushi tayi ta nufaci inda yake sannu da zuwa ga baki daya ta
jagula masa lissafi zauwa ke dawa kike bye-bye haka? Malam mu shiga daga ciki
ai ko, biye kawai yake da ita, suka shiga cikin gida su waye suka zo wurinki ne
haka, ni fah da farko duk kin tsoratani n zata ko ke kadaice a gidan duk
hankalina ya tashi, wani kallo tayi mai alamar ina ma fushi da kai, eh ai dole
kace haka ai, ta wani shagwabe murya sanna tace stunda kasan Nuhu ya kawo su
Ummi! Shine ka tafi abinka ka shallake, to sune nakewa bye-bye da yazo daukan
su, nayi-nayi ya jiraka amma yaki ta, su ummi!! Kuma Nuhun ne yazo daukan su!!
Mikewa yayi inna lillahi wa inna illaihi
raji’un, a firgice itama ta mike hakika sulaiman dinta ba karamar razana yayi
ba to muje na razana a cikin abinda ta fada. Lafiya dearest meya faru meye don
Allah gayamin, Bilkisu tashi ki had kayanki gobe-gobe zamubar garinnan, me ya
faru ka gayamin! Ta daka masa tsawa tana mai zubarda kwallah batareda tasan ma
tayi ba, da kyar ya kwantarda hankalinshi ya zaunarda ita kana ya bayyana mata
duk abinda ya faru tun daga farko har rasuwar Alhaji da rashi lafiyar mata Nuhu
duka ya bayyana mata shiru tayi ta kasa koda motsa dan yatsan ta akan tsananin
firgitarda tayi Bilkisu! Bilkisu! Ga baki daya batajin abinda yake fada, said a
ya wujijigata da karfi sanna ta dawo ayyacinta, Bilkisu karki damu gobe-gobe
zamu bar garinan a’a ba sai na ta fada tana mai fashewa da matsanancin kuka,
a’a Bilkisu ki bari gobe tunda sassafe, a’a ta durkusa kasa ta rike masa
guwayyunsa na rokka don Allah Mubargarin nan a yau din nan, nunfashi ya aje, to
shikenan jeki hado kayanki mu wuce, karki damu sa sauran kayan, idan nazo
karbar transfer letter din azan wuce dasaura, shiga tayi ta tattara kayanta
shima tattara nashi kayan yakeyi, sai a yanzu ta gane lallai wayannan basu
Ummmi bane, bayan da ta zuba maganin sai taga duk sun wani kamar rikice, ta
tuna sanda ta aika amina kitechen ta dauko mata plate sam takasa shiga a
kitchen din, sa yanzu ta fahimci tun lokacinda ta zuba maganin basu sake takawa
daga cikin falon ba. Tsam ta mike tunawa tayi da yanda Ummi ta dauko jug a
cikin feeg wanda ta cika da drinks din kwakwa ta wankada akan kofar fita falon
wanda zata fitar da mutum zuwa ta gane da gangan ta fadi ta zubar da drinks din
don dai kawai su samu su fita. Kamala hada kayan tayi a dai-dai lokacinda shima
y agama kamala nashi muje ko yace ta janyo hijabinta data ajiye kalar kayanda
ta saka tace eh, muje tare suka nufi hanyar fita, tsayawa sulaiman yayi ya
kalli gidan da kyau ya gayda kai ya wuce suka kulle gida sun juya zasu wuce
sukaji an kyalkayale da wata mahaukaciyar dariya, duban juna kawai sukayi ba
tareda sun ce ko kalaba sukaja akwatunansu sai a kan titi suka tsaya, wani mai
a daidaita suka tsayar, garge zaka kaimu, yasa kayansu ya nufaci garge din,
misalign karfe uku da rabi ne narana garin ana tsananin zafi, wurin fifa ya
tsayar day an layin su, jira suke ya dauko musu hannu su wuce, ji tayi kamar
ana girgiza kasa, ruguzum komi na wurin ya fara rusgawa cikin kasa, kuwwa da
hrgowar jama’a kawai kakeji, motuna da baburra sairuguzawa sukeyi kamar an
cilla a dai daita sahu su, sulaiman ya runtuma cikin, caf tasa hannuwanta ta
cafkoshi, wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta shiga kuka take tana
hargowa karka tafi ka barni tana rike da hannunshi sauran jikinshi kuwa yana
lib, hannunshi ya fara subuce mata tana mai tsala uwar kuwa tsundum ya fada
yana kiiran sunanta Bilkisu! Bilkisu! Sulaiman ya ingi zata, caraf ta dawo daga
wanna mummunan mafarki zatace ko tunani, ita dai tasan a zahiri taga wannan abu
ya faru, lafiya me kike tunani haka? Sulaiman ya katseta, waige-waige take da
idanuwata cikin mawuyacin hali, ke meye? Meya faru? Jin ta kama hannuwanshi ta
jinike da nata, a jiyar zuciya yayi, karki damu masoyiyata insha Allahu zamu
isa gida lafiya, gobe irin wannan lokacin kina gaban Umma, ya fada yana
zolayata, duk day a kokarin da tayi wajen gani tayi murmushi ta kishingida
dai-dai wajen ‘yanBauchi aka ajiye su, sune passengers na farko da suka fara
loda a motar, bayan an saka masu kaya a mota, suka shiga ciki mota suka zauna
suna jiran zuwan sauran passengers, zaunawar su keda wuya dum! Sukaji ko ina
yayi rufe da wani matsanancin duhu smai tsananin muryoyi sukaji kala-kala ta yadda
ba zasu iya tantance ko murya mace, namiji? Ko kuwa karamin yaro ba. Gargadinsu
a kayi da murya mai kaushi akan suyi gaggawar fita daga cikin motar na su koma
ya zuwa gidansu da suka baro, muddin kuwa sukace zasuyi taurin kai, kuwa zasu
hadu da matsanancin hadarin motar da zatayi sanadin halkar duk wani passenger
da ke a cikin motar, sanna kuma aka wayanda basuji basu gani ba, domin kuwa
driver matarshi ta haihu kwana biyu yayi saura ayi biki, idan sukayi sanadiyar
mutuwar wazai dauki nauyin iyalishi kuwa wanda yake kan gaba a kusa da driver
dan makarantane shi kadai ne namiji a gidan su, mahaifinsa ya rasu mahaifiyarsa
ke wahala wajen ganin ta biya masa kudin makaranta. Ita kuwa wannan matar
‘yaranta duka biyu marayu ne ‘yan uwan mahaifinsu sun kwace musu dukiyarsu,
wajen ‘yan uwanta zataje neman agaji. A haka akaci gaba da lissafo musu ko wane
passenger da abinda yake kunshe dashi duk domin dai so fita daga cikin motar
bayanta aka gama gargadinsu, wayau! Sukaga ko’ina ya yaye, kuma motar da suke
ciki hart a cika da passengers, kamar yadda aka shaida musu haka kuwa suka
gani, duk wayanda aka lissafa musu a motar su da ne ke ciki. Kallon juna sukayi
ba yareda sun samu dammar furta wata kalam ba, wayar direba ce yita wau kara,
dauka yayi tareda sallama, slamu alaikum lafiya kalau wallahi, a’a
alhamdulillahi mun gode Allah, amen, amen, sosa kunnenshi yayi yana ‘yar
dariya, eh saura kwana biyu ma ayi bikin ai ina Allah ya yarda. Dam gabansu
yafadi suka sake duban juna da karfi, tare suka hada baki dakata!! Duk motar
kowa ya jiyo ya ba, ana saka kayane a but da hanzari suka bade murfin motar
suka fito, mun fasa tafiya Sulaiman yace gaywa condester, don Allah kuyi hakuri
wallahi mun fasa tafiyar me kace malam, kamar ya ya kunfasa lafiya wanna aima
maganar banzace, duka mutanen wurin suka taso wasu na bayadda hakuri wasu na
zugawa, anan dai aka samu wani dattijo mai hankali da sanin ya kamata, yace
tunda ai ga wasu passengers nan ba sai kawai su shiga a madadin wayannan ba, ai
wannan abun bai kai na wani dogon bayani ba, sukayi masa godiya suka nemi a
dai-daita sahu suka sake saka kayansu suka nufi gidansu da suka saka baro, suka
bar mutanen garage din kowa tana mamakin wayannan mutane haka, su kadai suka
san dalilin da yasa suka bar motar, ba kuzari mai adai-daita ya sauke su a
kofar gidansu, said a suka yi kamar minti bakwai a tsaye suna kallonn-kallo
sanna Sulaiman ya bude gida suka dunguma a ciki, ga baki daya duniya tayi masu
zafi komai ya kulle musu, sun ma rasa ta inda zasu fara bamai cewa kowa ko
kala, suka isa bakin kofar falo ya saka key a ciki yana kokarin mirdawa ya bude
kofar falon, kiririn,kirin wayar Sulaiman tayi kara su duka suka zabura da
karfi, hannu yakai aljihu ya ciro wayar, sunan mahaifinshi ya gani ya bayyana a
gaban screen din wayar shi, dauka yayi, yayi kokarin boye duk wata damuwar shi,
da ke tattare dahshi, slamu alaikum Abba ina wuni lafiya kalau, lafiya kalau
take, komai Alhamdulillahi, Na’am Abba na nameye ya tambaya yana mai nuna
mutukar mamakinshi a filli kamar a gaban Abban nasa yake, kallonta yayi da
hanzari eh yayi murmushin yake yace amen, har yanzu kallonta yake yi, to amen
baba ehan, ya katse wayar har yanzu kallonta yakeyi, ga baki daya hankalin shi
a tashe yake itama kallon nashi take yi, meye ta tambaya tana kallonshi wai
Abbane yake tayani murya, wai a dazun nan Ummata ta kira ki a waya, kika gaya
mata mun dawo ne daga Asibiti likita ya tabbatar mana da cewwa kinda juna biyu
na tsawon wata biyu, dirshan ta fadi zaune barkewa tayi da wani matsanancin
kuka, shima, sulaiman zama yayi a dai-dai kusa da ita sai dai wannan karon ba
lallashinta yakeyi ba, hada tagumi yayi ta fada kogon tunani, shi ba abinya
fada ta gida ba, a can hankalin su ya tashi, kuma ma zai iya yuwa idan wani
yace zaizo a kasheshi a kan hanya sunfi minti goma anan zaune, sa’annan
Sulaiman ya mike ya iyadda bude kofar falon su duka suka shiga ciki, jawo
akwati takeyi itama suka nufi daki ji tayi kamar an ja mata kafa jicce ta fadi
kass ram! Yunkurawa tayi ta tashi amma ta kasa, wasu taurarin wahala ta ringa
gani sunayi mata yawo, yarda tashi akwatin yayi ya nufo inda take da gudu,
yanka kokarin tada ta, lumshe idanuwanta ta farayi, tun tana iya budsu har
takai ga duka suka rufe rungumeta yayi ya kwala uwar ihu, da hanzari ya
tallabeta da gudu ya fito baima tsaya ta wani rufe gida ba. Mijin Khadija yayi
kicibis dashi ya dawo, da karfi ya tsayadda mota, Sulaiman da gudu ya shiga,
Asibiti, asibiti! Da isarsu asibiti aka daurata saman keke da gudu aka wuce da
ita emergency, gaf aka rufe kofar emergency aka dakatar dashi daga yunkurin
shiga cikin dakin da yayi, jiginawa yayi a jikin bango emergency zaune yayi a
nan wurin ya fara kuka ne ya ringa lallashi da kyar da sidin goshin daina
hargowarda yake ya zama hawaye kawai ke zuba daga idanunsa, nurse c eta fito da
fara’arta da kafri suka mike su duka sister ya lafiyar jikinta, zan iya shiga
yanzu, don Allah ku bari na shiga nag anta, Sulaiman k eke jero wayannan zancen
duk shankalinshi a tashe relax malam cogratutaltion ma, wani kallo yake mata me
kikace? Cewa nayi congratulation matarka na dauke da JUNA BIYYU na tsawon wata
biyo, kuma zaka iya shiga ka ganta, za ma kaiya tafiya da ita, because she is
out of danger known. Bai jira ta kommala jawabinta ba yaruga da gudu zuwa cikin
inda dearest dinshi take, zaune ya taradda ita tana kallon yan yatsunta tsaye
ya tsaya cak, kamar tasan dashi ta daga kai suka hada ido, ya karaso inda take
ya rungumeta yana zubarda kwalla, Alhamdulillahi kin tsoratani, don sAllah kada
ki sake yimin irin haka. A nan aka sallame su daga asibiti maigidansu Khadija
ya maidasu gida, sukayi masa godiya sun ma rasa zaune kawai sukayi kamar masu
ansar gaisuwa, kiran mariba akayi, suka tashi sukayi alwala, ya jagoranceta
sukayi sallah, mikewa yayi ya fada kichen a dafa mata indomies, a wani bangare
na rayuwarshi harga Allah dadi yakeji mara misaltuwa, matarshi nada ciki, kenan
zai zama baba, zubo indomie yayi a flate ya kawo masu a nan bedroom dinsu
tareda rowan da zasu sha, aka kira isha’I suka mike suka sauke farali, suka
jawo kwanon abinci sukaci sukasha ruwa, ta tashi da dauki kwanuka da ni yar ta
kai kitchen karaf ya amshe, no wannan ba aikin ki bane yanzu, zauna ki huta,
kada ki wahaltamin da baby, duk da irin halin da suke ciki said a tayi yar
dariya, duk kunya ta lullubeta, ya dauki kwanuka yaje ya ajiye ya dawo, suka yi
addu’a suka kwanta. Wayyo!! Wata kara aka buga mai mai matukar firgitarwa
zunbur suka sauka daga kan gaso jan abu sukaji anayi a falo, kasan tys idan ana
jan abu akanshi zai ringa bada wani sauti daban, kuka sukeji anayi matsananci,
a hankali suka tattaka ya zuwa bakin kofar daki yaddazasu iya hango abinda ke
faruwa a falon, da baya sukaja da kafri saka makon ganin wanan tashin hankali
da basu taba gani shi ba, wata mace ce ko ince budurwa wace bata wuce shekara
goma sha takwas zuwa sha tara ba, ake ja, batareda suna ganin mai jan nata bag
a baki daya jikinta jinine faca-faca, kama kuwa kadan ya rage ya rabuda gangar
jikinta, rokonsu take tana kuka don Allah ku taimaka mini, karaja sukeyi da
baya suka rungume juna suka kankame waje daya, wuf tayi ta nufo su da niyar ta
cafke su, kamar an wulla ta ta fada can gefe daya, sake mikewa tayi kanta yana
shillo ta kara nufo su amma kamar a karon farko ma sake wurgata akayi, kuwa
take kala-kala iri-iri tana yunkurin kamasu amma ta kasa, su kuwa suka buga
suka kara ja da baya suncakankame juna, duk wani yunkuri, na shiga cikin dakin
tayi amma ta kasa Sulaiman ne yayi karfin hali ya ja kofar daki ya rufa da
karfi ya dawo daga baya. Duk hargowarda takeyi a kunnuwansu yake, addu’a suka
yi suka tottafa ko’ina suka haye kan gado ko runtsawa ba wanda yayi-sai yanzu
Bilkisu ta gano dalilin da yasa ta kasa shigawa acikin dakin, maganinda baban
nan ya btane, haka suka zauna ba wanda ya koda runtsa idanuwashi, sai a
shiyoyin asuba su duka bacci ya sace sub a tareda sun sani ba Sulaiman ya fara
falkawa, kasa rufe bakinsa yayi sakamakon kashin ganin matarshi da yayi akan
gado, kofa ya gani bude, a hankali ya tashi ya fara tafiya yana duba kofar, can
ya hango Bilkisushi a falo zauna murmushi, zo dearet, zo mu karanta Qur’ani
kama meye yayi kadan ya cuta mana, shi nake karantawa kazoo mu sauke Qur’ani a
yau dinna, ajiyar zuciya yayi ya sauke nunfashi da karfi okay bari na dauko
nawa Qur’anin, a’a ai gashi na dauko duka zo kawai mu karanta, fitowa yayi ya
nufa ci falon ya tsallaka ya fada cikin falon, sai dai kuwa abinda bai saniba
Bilkisunshi tana kwance sa bias gado tana sharer bacci abinta. Sai da gari ya
fara wayewa sannan ta farka itama kamar yadda Sulaiman yayi haka itama ta fara
duban mijinta har a toilet ta dubashi bata ganshi ba cak ta tsaya da taga kofa
a bude, a hankali ta fara tafiya ta nufaci kofar da zata kaita falo wani
faduwar gaba taji da bugun zuciya tsallako kofar tayi ta nufo mijina kam ta
kame tsaye akan matsanancin tashin hankalin da taji, mijinta dearest dinta ta
gani a zaune da wasu kananan kayan da hula da wasu rufaffun takalma kai! Sak
shigar USMAN! Yadda yake zama, yadda yake kada kafa daya juye hularda yake yi
kai! Kome sak na MAN! Daga kai yayi ya fara dubanta tun daga sama har kasa,
itama suban nashi takeyi, nikewa yayi kau!! Ya wanka mata wani hatsa bibin mari
said a ta fadi ta fasa bakin ta, kamar wanda ya dawo daga hayyacinsa y ace
cikin wata murya wadda ko ba’a gaya maka ba kasan mace c eke wannan murya,
yanzu idan Usman yaji yanda nayi miki fa ya fara dube-dube kamar wanda yaga
usman din a falon, da karfi kuma ya juyo ya kalleta kallo irin na mugunta da
tsananin kiyayya yaci gaba da Magana wannan dai ta mata, idan na kasha ki ai
bai zai taba sani ba yana fadi yana cize hakoranshi, ya nufaci inda take ya sa
hannun ya cafko wuyanta ya dagata dashi sama har ya cirata har karfi aka banko
kofar shigowa falon! Tsohon nan ne da suka saba dashi, da karfi ya wankada
mashin wasu ruwa da suke rike da hannunshi, wai gowa Sulaiman din yayi da karfi
suka hada ido da tsohon, wurgarda Bilkisu yayi da karfi ya sheka ya nufi bangon
falo tuma yayi ya tsunduma cikin bandon baya bace. Baban yaje ya tayadda ita
kuka takeyi kamar ranta zai fita, ba dai Usman ne keyin duk wannan abinda ke
faruwa ba, take fadi tana kuka mai tsanani. Ba Usman bane ke muku wanna abun
amma sanadiyar sa ne duk wannan abun ke faruwa, how? Tayaya? Ina mijina kuma
wane sanadine na Usman aka da yake faruwa dan haka ta fada tareda zubewa a kasa
tana kuka. Gyara zama yayi ya fara fadi mata kamar haka --------
Ku biyoni a littafi na biyu dan jin
cigaban kayatacce labari.
Taku mai debe muku kewa Asiya Sadiq Maccido
(Asikhan)
Subscribe to:
Posts (Atom)