HUBBUL YAKIN cigaba 4
ASIYA SADIQ MACCIDO
(ASIKHAN)
Copyright © Asiya Sadiq September, 2017
Hakkin Mallaka (M) Asiya Sadiq September, 2017
Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State, Nigeria
Tel: 08113777717
Book 1 of Hubbil Yaqeeen Series |
A
haqiqanin gaskiya taji dadin zuwan su matuqa domin tayi fira sosai dasu gaskiya
gwanayene wajen bayar da dariya sai
faman dariya suke sta, kuma sun tattauna abubuwa masu muhimmanci wanda ya shafi
aure, kasha gari da safe sbayan Sulaiman ya wuce office ta shirya tana zaman
jiran habiba isowar habiba yar aiki su Khadija bata wani dade sosai ba tazo
suka wuce sai gidan mai kitso: Habiba tayi Sallama dasu ta wuce tayi sa’a kuwa
bata cimma kowa ba ita kadai ce suka gaisa da inna Kande tsohuwa dattijuwa da
ita mai kirki, zauna yan nan ki jira na dan dama kokon nan kinji ta
shimfida mata tabarma Bilkisu ta zauna
ita kuwa taje tadama koko ta sauke ta zuba a wani bokiti mai murufi ta kai daki
ta ajiye ta fito. Sannu da zuwa fah, ince dai kona tsaidaki ko kiyi haquri fa,
haba inna ba komai ai Bilkisu ta fada tana maid an murmushi. Kujera ta dauko ta
zauna wane iri za’ayi? Kitson ulu nakeso tau sai ki juyo a fara aiko. Kitso
take suna dan fira, basu dade da fara kitso ba sukaji Sallama, wa alaikissalam
ah hajiya Larai sannu da zuwa, wata babbar mace c eta shigo suka gaisa sa juna.
Kai bari kallah kitson nan yayi kyau sosai, murmushi kawai Bilkisu tayi ya
sunan ki sunana Bilkisu, yarinya mai hankali da nutsuwa nan dai aka fara fira
da matar, ita dai sba mai fara’a bace sosai irin mutanen nan ne da basa son
Magana ba ruwanta, ita dai har a ranta Bilkisu ta shiga a zuciyanta. Bayan an
kamala yi ma Bilkisu kitso ta bude Jakarta ta dauko wata leda wanda ta rikowa
mai kitso,sabulai ne na wanka dana wanki ssai man shafi da turare ta ajiwa mai
kitso tayi godiya. Kai! Alhamdulillah nagode sosai buki inna Kande ce da
murnanrta sosai wane layi kike ne domin ban saba ganinki ba. Anan bayan naku
nike gaidan mu yana kallon bayan ginar church dincan mune karshen layin da
karfi. Inna Kande tace gidan gate kalar madara da baki a firgice, ita kuwa
hajiya Larai da take zaune mikewa tayi zumbur da karfi firgice lafiya inna meya
faru kika firgice haka na fadi wani abune ku gayamin a’a ba komai Bik
ai---ai--- inna Kande bata samu dammar iyadda maganarda takeyi ba, ji kawai
Bilkisu tayi an cakume tad a karfi an shaketa, ina dana? Hajiya laraice ta
shaketa take mata wannan tambayar a gigice. Bilkisu ke kokarin kwatar kanta nace
ina dada? Ki fito min da dana abinda taci gaba da fadi kenan da kyar inna kande
ta kwace Bilkisu a hannunta t samu ta riketa shieka Bilkisu yi sauri inji inna
Kande, daukawa tayi ta dauki jakar tat a wuce da karfi said a takai bakin kofar fita tadan juya har
yanzu hargon wa Hajiya Larai keyi tana fisge-fisge ku fitomin da yarona Bilkisu
ki shega nace tsawa inna Kande ta bugamata, ai kuwa da gudu ta fita. Ga baki
daya kan Bilkisu ya kulle tafiya kawai take amma hankalinta baya ga inda take
tafiya. Shin ko dai hajiya Larai mahaukaciya ce? Amma kuma bata da alamun
hauka, ko kuwa irin mahaukatan nan ne da haukar keyi tana taso musu? Can taji
kamar a kunnenta maganar inna Kande “gidan gate kalar madara da baki?” hakika
hajiya Larai ba mahaukaciya ce ba domin inna Kande ma a tsorace ta fadi wannan
maganar, to wane yaronta kuma? Me yasa su suka suka firgita dajin gidan da
take? A dai-dai lokacin da ta’iso kofar gidanta kenan, kicibis tayi da Sulaiman
Bilkisu kin dawo har an gama kitson? Firgigi tayi kamar wadda ta tashi daga
barci kallon shi kawai take batare da tace masa uffan ba lafiya tambaya yana
meya faru Sulaiman ya tambayeta yana mai cike da fargaba hida da tsoron kallon
shi kawai take gaba dayi kamar wata bebiya ta kasa furta kome. Hannunta ya janwo
ya shiga da ita cikin gida bayan ta zauna ya sake tambayar ta Bilkisu lafiya
meke damunki ne bata fasa kallon da take masa baga baki daya ta kasa Magana
kamar wace aka rikewa harshe duk jikinta ya mutu tarasa meya sameta da kyar
taji bakinta ya fadi bacci nakeji tare da wata hamma mai tsayi, to zo muje ki
kwanta girgiza kanta kawai tayi alamar a’a sai kuma ta miqe kafa a nan saman
kujerar da take bisa ta kwanta idanuwanta taji suna budewa suna kullewa sannu a
hankali, nan take bacci ya kamata. Ita ce bata farka ba saida akayi isha’I, a
hanakali ta bude idanuwanta tayi arba da Sulaiman take Bilkisu kin farka? Daga
kai tayi ta bishi dany tace abinci lafiya naga kai bakaci ne murmushi yayi ai
naci nawa wanna naki ne, maida masa tayi da murmushi to ai ni yayimin yawa dariya
yayi nima dai nasan da haka kici kawai wanda zaki koshi harki damu da sauran to
a ina ka siyo shi yayi dadi fat a fada tana dan kallonshi wani restaurant ne ko
dalili sunan shi nan dai tace abinci ta koshi tasha ruwa masu sanyi hankalinta
ya dawo jikinta. Nace ba Bilkisu dazu mun fara Magana sai kikayi bacci meya
faru dake ne dazu? Ince dai lafiya ko? Ai kuwa nan take komai ya dawo mata kamar
yadda ya faru dazu a gidan inna Kande mai kitso a tsorace ta fara bashi labara
kasan meya faru dazu bayan naje wurin kitso har an faramin sai ga wata mata
tazo ----- baran wani almajiri ya katseta almajiri yau a gidnmu Bilkisu ta fada
tana mamaki, a kinga kuwa bamuyi asarar abincin mu ba saiki dauki saura ki zuba
masa ki dawo kici gaba da gayamin abinda ya faru dazu to ta fada tare da daukan
sauran abinci ta nufi almajiri zo ansa da hanzari ya shigo ya gaidata dan
qarami dashi taro kwanon ka a taro kwanon shit a juye masa, nag ode Billy! Da
karfi tadago me kace tasan duk/a fadin duniyarnan ba wanda ke kiranta Billy
idan ba “Man” dinta nada ba kuma yama akayi yasan da sunanta me kace da karfi
ta sake tambayarsa dagowa yayi yace cewa nayi nagode Hajiya ajiyar zuciya tayi
cikin ranta tana mai godewa allah daba yadda taji ya fada ba, a cikin ran nata
ne ta juya zata wuce domin taje ta idarma Sulaiman da labarinda ta fara bashi
mai dauke da al’ajabi da kuma firgici ji kawai taji almajirin yace “ba wani
tsoron da kikaji dazu Billyn da kikaji da farko na fada shi dai na fada tsayawa
cak tayi ta daina tafiya a hankali ta fara juyawa maganarda tayi a rai wadda ko
fatar bakintabatasan anyi baya akayi shi ya jiya Billy fah yace idonta a zare
hankalinta a tashe a firgice ta nunashi da yatsa me kace sake maimautawa. Rike
yake da kofar gate din gidan qafarsa daya ciki daya yana fuskantar ta ya bude
baki yafara Magana “kowane mutum yanada lokacin shina tsoro inayi miki bushara
da yanzu lokacin tsoron ne da firgici da tashin hankali a gareki da kuma
mijinki Sulaiman daga yanzu kwanciyar hankali ta kaurace Mukuhar ----- bata
jira ya I darda maganar da yakeyi bat a fara ja da baya baya ta wurga da
kularda ke hannunta ta runtuma da gudu ya zuwa cikin gida. Da gudu ta fada falo
Sulaiman ya mike ya dai wai Bilkisu meke daminki ne iye? Abinda almajiri ya
fada mata duk ta kwashe fada mishi, tana Magana cikin firgita da ruduwa kuma a
tsaye take bashi labaran ha ta kamala sai dai kuma daya a cikin labarinta ta
boye almajiri ya kiramata wato Billyn da taji almajiri ya kirata dashi,
dalilinta kuwa anan shine tana jin tsoron ta yadda Sulaiman zai kalli al’amarin
ne kallonta yake yi idon sa a zare kai da gani kasan yana cikin tashin hankali,
lokaci daya idanuwanshi suka ciko da kwallah da kyar ya samu ya iya zaunawa
akan kujera, a da-dai lokacin kuwa Bilkisu durkushewa tayi kasa tana tsala uban
kuka, ganin halinda ta shiga yasa Sulaiman ya tuna shifa namijine don haka yayi
yake ya ta yadda ita ya zaunar da ita akan kujera kada ki damu Bilkisu koma me
ne yake shirin faruwa, damu Allah nanan shine gatanmu, bata jira ya idar da
abinda yake fadi bata tari nunfashin sa wallahi bana iya zama anan gidan, ko
kwana daya bana karayi a cikinsa, tun ranar da nazo nake cikin fargaba da
tashin hankali mara misaltuwa, ni bana iya zauna cikinsa ta kawo dai-dai nan ne
ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi don Allah na rokeka ka maidani
gidamu ka kaini garinmu bana son wanna garin duk tausayi ya kama Sulaiman
hakika da gaskiya Bilkisu akwai wani mummunan abu dake biyarsu, tabbas akwai
wani boyayyen al’amari a tattare da gidan nan da suke ciki. Bilkisu ki
saurareni ki natsu da kyau koma menene nayi alkawarin zamu bar gidannan gobe
zanje na nemi transafer dole ne mubar garin nan, yanzu ne taji sauki a ranta
sossai, zo muje mu kwanta in Allah ya yarda komi yazo karshe Bilkisu. Ta shi
tayi ta biyo shi tare sukaje suka kulle kofar gidan sannan suka wuce daki yayi
addu’a akoina ya tofa itama Bilkisu haka suka kulle daki suka kwanta duk da
kasancewar ba wanda bacci ya dauka cikin su. Kamar wadda aka gwanta ta tashi da
sauri ta girgiza Sulaiman tashi-tashi sai dai abinda bata sani ba bacci yakeyi
bad a sauri ya tashi lafiya wani abinne kuma? Menen? Gobe idan zakaje office
neman transfer tare zamuje ko domin bazan iya koda second daya a gidannan ni
kadai ba wallahi. Ajiyar zuciya yayi game da murmushi da yaji akan wannan bin ne
kafin nawuce zanyi waya da abokin aikina Nuhu kinsan yanada ‘yaya mata masu dan
girma kuma kinsan gobe ba skull kinga sai suzo su tayaki zamam har na dawo
kinji to ta fada tare da da’a kai alamun ta gamsu da haka. Kasha gari asuba
daya daya tashi baije masallaci ba domin samin halinda suke ciki, shi dai
gurinshi su bar garinnan lafiya, bayaso wani abu ya cutarda su musamman ma
Bilkisu. A hakikanin gaskiya sanan kanshi ne akwai abinda yake faruwa a
gidannan, shima kanshi ba saudaya ba basau biyu ba yasha jin abubuwa a gidan
sanna kuma yasha garin sai dais u kama yi masa kamar dabo, baifi sati biyi bad
a ya fito daga wanka yazo a dressing mirrow kawai wani kato ya gani a bayanshi
hankali a game da katon shine a gefen fuskarshi tun daga samamn girrshi harya zuwa
kumatunsa wani irin mummunan rauni ne yank ace babba wadda har kama hango
kashin fuskarsa, jinni ne yake zuba kamar fanfo daga mummunan raunin har ya
rife masa gaba ki dayan fuska, da karfi ya juya amma ba’a mamakinsa ba wannan
katon ba dalilinsa suke maida duban sa yayi ya zuwa madubi sai kuma ya sake
ganin wanna katon da karfi ya juya zai fita yabar dakin sai ga Bilkkisu ta
shigo kannewa kawai yayi domin kada ya fada Bilkisu ta firgita kai abubuwa ba
iyaka da suke faruwa dashi a gidannan, lallai akwai boyayyen alamari, a dangane
da gidannan numfashi ya sauke sa;annan ya tayar da Bilkisu domin ta tashi tayi
alwala suyi sallah. Bayan sun idarda sallah ga musu break fast suka ci, ya
tashi taje yayi wanka, Bilkisu bata yarda ba’a bakin bandaki tashi dai abin
dariya ma ya koma yana bashhi, har ma dai lokacin da tace itama sai ya jirata a
bakin bandakin tayi nata wankan domin ita sambata yarda ta fada bandaki ita
kadai ba dolen shi ya zauna yayi gadinta hart a kare wanka yanata faan yimata
dariya, ita kuwa ko a jikinta, ita dai kada yayi nisa da ita. Bayan ya kamala
shiryawa yace mata shifa zaije ya nemo transfer dinda ya gayamata daga nan kuwa
zai wuce gidan wanda ya basu haya domin ya sanarda shi sufa zasu bar masa
gidanshi. Nnfa kawai, wata sabuwa inji iyan caca!! Alan baran taki yarda sam
ita ba ba inda zaije ya barta. Ke tunfa a jiyannan nayiwa Nuhu text akan cewa
ya kawo diyan shi a yau a gidanana suyi mana wuni, kinga shima yayimin reply
kinga danna wayarshi shima ya nuna mata reply din Nuhu ta gani da kanna in
allah ya yarda duk da haka said a kyar sannan ta yarda zata zauna da sharadin
zata zaunaa kofar gate har Nuhu ya kawo yaranshi tukunna kafin nan su dunguma
su koma cikin gida. Ya ya iya haka ya amince ta biyoshi suka fito tare, sunyi
sa’a kuwa domin a bakin kofar gidan su. Ajiyar zuciya su duka sukayi. Sulaiman
ya fara Magana Alhamdulillah baba kazoo akan dai dai lokacinda ake bukatar
zuwanka cikin rashin gamsuwa da abida suka fada ya tambaya a dai-dai lokacinda
ake bukatar zuwana? Me kuke nufi su duka suka fashe da dariya Baba wani tsoro
takeji n tafi na barta ita kadai a cikin gida, tunda yanzu gaka ba sai ka
tayata zamaba. Murmushi yayi mai hadeda ajiyar zuciya eh zan iya tayata zama
daga nan wajen har kaje kadawo daga inda zakaje, ga baki daya suka sake dariya,
ai ko aciki baba zaka iya shiga mu a wurinmu ai kai tamkar dan uwammu ne na
jinni sulaiman ya fada a-dai-dai lokacinda yake shirin tada mashin dinshi, a’a
nikam dana ai lokaci shigowana baiyi ba tukum, idan lokaci shigana cikin
gidanku yayi bama sai kun kirani bada kaina zan shiga. Allah ko Baba Sulaiman
ya fada a dai-dai lokacinda mashin dinshi ya tashi ya bashi amsa kai tsaya to
Allah ya kaimu lokacin ya tuka mashin dinshi yayi gaba murmushi, suka sake su
duka tareeda fadin amen, a nan Bilkisu a zauna suka dan fara hira da juna, Baba
ne ya tambayeta ‘yata me yake baki tsoro cikin gidanku da har kike shakkar zama
a ciki? Sai da ta danyi jim sanna ta iya bude baki ta fara gayamasa abinda ya
dace ya sani bayan takai aya, yayi dogon numfashi daga ganina gujewa bla’I
bashine tsira daga bala’I ba, fuskantar bala’In shine masalaha, irin wayannan
abubuwa suna faruwa daku kuntaba samun dama kuka tambayi kanku shin meye
dalilin faruwar duk wayanan abubuwa? Tabbas akwai dalili, dalili mai girma, da
ganan kuwa har zuwa Birnin sin in kunje ba zaku tserewa faruwarsa ba. Diyata
ina mai baki shawara duk da ba, za ki fuskanci koma meye yanzu gadan abinda zan
iya taimaka miki dashi yasa shannunshi a cikin babbar rigarda ke sanye a
jikinshi take cikin yanayi na rashin gamsuwa kana ta mika hannu ta karba.
Bilkisu koda ni mai cutarwane bazan taba cutar daku ba ki duuki wanna maganin
duk wata hanya da kikasan wurine da ake iya shiga cikin gidanki, ma’ana bakin
kowace kofa harta bandaki ki zuba maganin, yadda kuwa zaki zuba kereriyar kofar
zakibi, kina zuba maganin tun daga farko ta har karshe, karki damu kome
muguntar abu bai isa ya ketare takan layin nan ba, kuma koda kin share maganin,
aikin shi yanan bazai goge ba, abu daya kawai ke ruguza maganin shine idan ruwa
ya zuba a inda aka zuba maganin, ruwa anan ana nufin duk wani abu da bane ina
fatan kin fahinta, daga kai tayi eh Baba na fahinta nagode sosai Allah ya saka
da alkhairi amen, tashi ki shiga cikin gidanki ba abinda zai sameki kinji yanzu
ya zama mini dole na tashi na bar wurinnan ba domin naso ba. Ji tayi matukar
karfafa mata guiwa ta tashi ta shiga cikin gida kai tsaye, da isarta kan kujera
ta zauna kalaman Baban nan suka ringa fadomata a rai kwata tawata ta rasa ta
inda zatasa kalaman nashi, shin gargadinta yakeyi ko kuwa shawara yake bata,
koma meye yau zata saka maganinda ya bata kuma zata ga karshen koma meye kafin
gobe su kaura ya zuwa garinsu, murmushi ta saka wani irin dadi taji ya ratsa
zuciyarta. Aunty taji ankira da karfi, juyowa tayi su Ummi ta gani tana
murmushi har a ranta taji dadin zuwansu, sai a yanzu kuka zo, waya kawo ku
Babamu ko? Ina yake ne. amina ce tace ya wuce shine ko shigowa baiyiba, ku zo
ku zauna, aunty sa mana nicklochen sukayi zamansu, suna masu nishadi, sai
fara’a take yaran akwai su da shiga rai, sai dai abin mamaki zuwansu da salo
Ummi kuwa shiru-shiru ba ruwanta, har iyayen suna fada ko Magana batason yi
idan dai bata zama mata doleba amma a wannan karon itace mai baki karma bakin
nata da salo ya zarce na Amina a wannan karon ita kuwa Amina itace ba ruwanta a
wanna karon.
Zamu cigaba Insha Allahu
Muna godiya
ReplyDelete