Thursday, 9 February 2017

PART 2: SIRADIN SO NA AMINTA DA SOYAYYA



PART 2: SIRADIN SO
NA AMINTA DA SOYAYYA



Na aminta da soyayya
Kaunar ki ce nayo niyya
Ke ce wacce nasa zuciya ta

Kaunarki ta zamto sarkakkiya
Rayuwa ta sa tayo farfadiya
Na rasa inda ni zan tsaya da kaunar ta

Rayuwa tamkar darbejiya
Da daci take tafi madacciya
Ya ki zo kice dani kin aminta

Zo kar kice dani kin kiya
In kinyi haka zan sakaya
Hankali zai gushe kanki masoyiya ta

A kaunar ki ni nake yin zabarbiya
Sauri nake yi bani gajjiya
Saboda son gimbiyar mata

Na aminta da soyayya
Kaunarki ni yau nai niyya
Ya ki yan mata

Na shiga rauni da zuciya
Amma na kasa tirjiya
Kaunarki ce ta sa ni gajjiya zo kice kin aminta

Sahiba ta zo ki bani soyayya
Aminiya ta kan ki bani alkunya
Sarauniya zo kice na aminta

No comments:

Post a Comment