Na rasa gane dadin zuciya tun lokacin da na ganki
Hakama na rasa gane kaina kanki diyar kirki
A duk lokacin da na kalli idanunki
Nakan kauda idanuwa na daga naki
Wannan wani abin mamaki
Ne a soyayyarki
Kaunarki ta tarwatsa al’amari
Ki taimaka ki saitan lamari
Ina son jin maganarki har abada
Ki yarda ki gina min lamari na na har abada
Mafarkin da nayi akanki
Ya tabbatar mini da haske da mi’imarki
A ciki nayi yaki a akanki
Kuma kin zamto uwa ta daki
Ki sani cewa ni ne sadauki naki
Mai kokarin kare hakki
Gani nazo kula na baki
Zaki ji dadi kula zan baki
Lafiyarki ni zani kare
Sururarki ma har mu kare
Ci da sha gasu a tare
Bani fatar a ce mu ware
Kaunarki kullum sai nasa turare
Ina ta fatar gyaranta kuma na kare
No comments:
Post a Comment